← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 164

Sashe 144

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

a guje, idanuwansu suka sauka a kan kyautar Allah Dake tsugunne se duka Kawai Annah ke kai mata da sandar karfen dake hannunta, sosai sukayi mamakin ganin Annah na dukan KYAUTAR ALLAH yau da kansu abinda basu taba ganiba tsawon zamansu a gidan se yau.... Jiki na rawa jummai ta karaso tana Bawa Annah hkri, Amma ina idanuwanta duksun rufe se kwala mata karfen takeyi, tini wasu sassa na jikinta suka fara fitar da jiki saboda azaba tanaso ta tashi ta gudu Amma ina ta gaza tashi ta gudun saboda kafafuwanta dasuka mata mugun nauyi. "Annah ki bari karki kasheta!!" Jummai ta fada kmr zata fashe da kukan tausayin KYAUTAR ALLAH, Annah na haki tana fadin "Ki barni in kasheta!!" Ta daga sandar da karfi ta rada mata a dai-dai saitin goshinta ai ba wani bata lokaci jini ya balle ya fara zuba saboda wawakeken ciwon dataji mata a goshinta ya shahara ... Azabar ciwon data ji mata a goshin ya gigitata, abinka da jikin yan hutu ba asaba da wahala ba, nan da nan ta gigice ta fice a hayyacinta, ta fashe da matsanancin kuka , bata masan sanda ta miqe ta a haukaceba ta dafe knta inda ke zubar da jinin ta ruga da gudu kmr mahaukaciya zata fice a falon, dai-dai ya sako kai sukaci karo da juna, ta juya zata fadi ya tarota da hannunsa na dama, ya zuba mata dara daran idanuwansa, meze gani! Jini yaga yana ambaliya a goshinta babu kakkautawa,,se fisge fisge takeyi sam bata hayyacinsa batamasan a hannunsa takeba, fadi takeyi. "dan ALLAH Annah karki kasheni! Ba lefina bane!! Wallahi bansan ina da cikiba!!" Kalaman dake fita daga bakinta kenan cikin fitar hayyaci. Sam be fahimci kan maganganun nataba yaji tausanta ya rufesa, again zuciarsa ta cika da mamakin wai yau Annah ce ke dukan KYAUTAR ALLAH da hannunta, daba dan yaxo yaganinma idanuwansaba da ko gaya masa akayi baze taba yadda ba . "meya samu goshinki plx?" A matukar razane ya tambayeta, idanuwansa duk a waje kmr zasu fito fili saboda tsabar tashin hankalin ganin jini na kwarara babu kakkautawa daga goshinta.. Dai-dai Annah ta karaso ta fisgota a hannunsa tana jijjigata tana fadin "zaki gayamin gidan ubanwa kika samu ciki ko senayi ajalinki yanzunnan...baza ki jawomin abin kunyaba da raina d lafia taba....kwara in kasheki in huta...!" Kalma daya ya iya riqewa a cikin kansa nan da nan ya shiga juya kalmar a cikin duniyar kwakwalwarsa, " ciki! Ciki! Ciki! Ciki kuma?" Ya jefawa kansa tambayar da bemasan meye amsar taba. Kara fashewa da kuka KYAUTAR ALLAH tayi hadda shasheqa kmr numfashinta ze dauke still ga jini nata kwarara ta goshinta, hatta fara ganin jiri,,, "dan ubanki baza ki gayamin wa yayi miki ciki ba!" Annah ta fadi da karfi, bata san sadda ta kufce a hannu taba tana saboda matsifa tana kokarin faduwa ta bugu da hannun kujera RASLAN dake tsaye ya karasa ya tallabota cikin dimauta hadi da tashin hankali,ya juyo da ita, yaga idanuwanta harasun fara kakkafewa saboda jinin daya zuba daga goshinta a kalla ze kai rabin leda. "KYAUTAR! KYAUTAR!!" Ya shiga kwalo mata Kira a razane amma ina tini ta sume , jiyowa yy da dubansa kan Annah, cikin kunar,rai hadi da gigita duk ya fice a hayyacinsa, ya fara magaba "Wallahi matata ta rasa ranta a kanki se kinci gidan yari!!" Be jira wata wataba ya ciccibeta suka fice a falon direct notar dasukazo dashi ya shiga, daman yusuf na ganinsa da ita a hannunsa ayi saurin karasowa yayima motar key suka fice a gidan,... Raslan na zaune a mazaunin baya yana rungume da ita a jikinsa se kiran sunanta yakeyi kamar wani zararre, ... Hkn ya bawa yusuf tabbacin asibiti zasuje, direct asibitin dasuke zuwa suka nufa daman shine asibiti mafi kusanci dasu suna isa ba wani bata lokaci aka nufa emergency da ita a kan gadon daukar mara lafia, wata nurse ke turo gadon, RASLAN na biye dasu , suna shiga emergency room din aka daketa aka daurata a kan gadon dake dakin, Har lokacin jini se kwarara yakeyi a goshinta, duk tabi ta batashi kaca kaca da jinin daya daukota kai kace dambe sukayi da jinin rago. Doctor zilai tayi tayi ya fita waje ya jirasu amma fir yaki fita... Dole a gabanshi sukayi mata treatment din dazasu mata, a farko de suka fara mata allurar da jinin nan ze tsaya, kana suka shiga mata gwaje gwaje, saboda dr zilai taga wasu alomomi dasuka bata mamaki gami da yarinyar, dan haka ta duba jininta ta nufa lab dashi bayan sun samu ta dawo dai-dai anyi mata dressing din wawukeken ciwon da annah taji mata a goshinta,da wadanda ke jikinta...canza musu daki akayi, hadi da maqala mata drib, se sauke ajiyar zuciya takeyi a wahalce dukda sanyin a.c dake dakin Amma zufa takeyi RASLAN ya zauna gefen bed din kamar zautacce ya zuba mata ido yayinda hannunta da beda Drib yake cikin hannunsa, se kissima irin bura ubar dazewa Annah in wani abu ya samar masa me dadinsa, Gabaki daya a bukace yazo yau burarsa na a miqe kmr sanda jiyama a hannunsa ta kwana se rarrashinta yakeyi, Amma fir taki hakura ta tubure kan dole se tashiga gindinta, dole ya nufo garin yau... Gashi ynzu an jaza masa jarfa, an maida hannun agogonsa baya! shi ynzu babban burinsama yaga ALLAH ya tashi kafadunta,kafin yaci gaba da gasa mata durinta da burarsa. kalamansa sun firgita Annah, komawa tayi ta zauna kan kujera zucia babu dadih se ynzu taji ta fara nadamar abinda ta aikatawa KYAUTAR ALLAH, Amma tasan ko wacce mariqiya ta kwarai dole ta shiga dimauta inhar taga wadda take riqo da cikin shege. Fashewa da matsanancin kuka Annah tayi.. Jummai da laraba suka zubo mata ido. "Ni yaronnanan yace ze kashe!"ta fada tana fyatar majina. Jummai da laraba duk suka bude bakj jin har Annah ta fassara kalaman RASLAN zuwa kalma me mugun riski da hatsari. "Annah shifa ba cewa yayi ze kasheki ba!!" Cewar Jummai. Annah ta zaburo mata tace "To durun uwarki yace! An gaya miki ni kurma ce muna fuka kawai! Maza jeki dauko min wayata ki kirawomin umaruru yazo yau dinnan, ga dansa nan yace ze kasheni, maza ki dauko waya ki kirawominshi tin kafin ya dawo gidannan ya kasheni kamar yadda yace!" Ta karashe maganr tana kurma uban ihu se maimaitawa takeyi wai RASLAN yace ze kasheta... Girgiza kai jummai tashigayi tana mamakin mummunar sharri irin na Annah, ta nufa bedroom dinta, ba jimawa ta dawo hannunta riqe da wayar Annah, ta mika mata, kin amsa tayi ta watsa mata mugun kallo kana ta daka mata tsawa "dan bura ubaki ba cewa nayi ki kirawomin umaruruba! .." Jiki na rawa Jummai ta nemo lambar alhaji umar tayi Dealing bugu daya biyu ya dauka, Annah najin ya dauka ta fisge wayar a hannun jummai ta kara a kunne, hadi da fashewa da kuka kmr wadda aka aikowa da mala'ikan azabah.... Hankalin alhaji umar in yafi dubu seda ya tashi, tana fara kukan ya fahimci koma meye RASLAN ne ya kara debo masa wata tsiyar. "Me kuma ya debo min?" Ya fada a ransa,,Amma a fili ya shiga bawa Annah hakuri. Cikin kuka Annah tace "Riqe hak'urinka banaso! Ka haifarmin matsifa da bala'i a matsayin jika, gashi ynzu wai har danka ke ikirarin ze kasheni da wuqa! Ka hanzarta zuwa tin be kaiga kashe ninba kamar yadda yayi ikirari!" ta karashe mgnr tana fashewa da wani mahaukacin kuka. "Kisa kuma!" Alhaji umar ya maimaita cike da mamakin hadi da rashin fahimta. "Annah wai wanni dan kike nufi?" Ya jefo mata tambaya cikin rashin fahimtah nan da nan duk ya daburce yadesan in RASLAN ne baze taba cewa ze kashe Annah ba, inbade giya yasha trela goma ba to shine ze yadda yace hakan. "Wanni d'a gareka a duniyar nan? Naga de ai d'a daya ka haifa gashinan kuma yana yawo a doron duniya! To shi yace ze kasheni har lahira! Ko kana nufin karya nakeyi....wayyyihuh ALLAH nah!" Ta fashe da mahaukacin kuka hadda daura hannu daya a kai tana fadin "Shikenan kar kazo ka bari seya kasheni inyaso se kuzo ku dauki gawa tarh!!" Ta kara kurma ihu tana haniniya kamar tsohuwar mota se jijjiga kawai takeyi tana kurma ihu kai kace kashe tanma akayi gabaki daya. Alhaji umar dukya gigice yama rasa mezece zuciyarsa ta mamaye da tunanin to me Annah tama RASLAN da har yake ikirarin ze kasheta. "Dan ALLAH kuyi hakuri Annah, insha Allahu zanzo gobe zanci masa mutumci zanji dalilin dayasa yace ze kashemin ke! Kwara tin kafin ya kasheki ni in kasheki!" Annah ta tsagaita da kukanta cikin jin dadih tace "to shikenan! Na hakura! Amma de inkazo karka kasheshi kadeyi masa katangar karfe da gidana, inba haka ni ze kashe wata rana!" Alhaji umar yace "to shikenan yadda kikace haka za ayi...insha ALLAH gobe da safe zanzo.." Annah tace "yauwa kazo din, komi kakeyi ka barshi kazo, nida nasoma kazo yau ne ai..." Alhaji umar ya duba time yaga 6:2pm kwantar da murya yayi yace "Annah time ya tafi, dan ALLAH kuyi hakuri zuwa goben se inzo da safe...." Annah tayi jim kana tace "To shikenan,kazo de da asubahi, saboda yanzu basa gidan suna asibiti shida yar bura ubar yarinyarnan..." Jim Alhaji umar yayi yana nazarin mgnrta ta karshe yace "asibiti kuma? Waye ba lafia..." Annah ta matso wasu kwalla masu zafi tace "H mmm bari, maganar babbace, sekazo gobe zakaji koma meye!" Alhaji umar yace "okay..." Zucia fal zullumi da tunani tunani, daga haka sukayi sallahmah ta miqawa jummai dake tsaye wayar. "Amshi muna fuka, kin bi kin zubomin idonki masu kama dana mayu, anya baku hada iri da mayuba ko kuma masu kambun baka.." Jummai ta amshi wayar hadi da tabe baki ta juya ta nufa bedroom dim Annah da wayar, "uwarki tanih tsohuwar barauniyar nan ita kika tabewa shegen bakin nan naki me kama da durin sah,..shegiya mara fasalih, a haka wani namiji zaki samu ya aureki...sede in makaho kou?" Jummai na jinta amma tayi kmr bata jiba, dan ita Annah ma tsoro take bata a halin yanzu, kadama tayi magana ta juyar da maganar zuwa tace zata kasheta tashiga uku ta lalace, kadan kenan daga aikin Annah.
Chapter 144 · 0% Book details