← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 164

Sashe 121

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiga mota suka koma zuwa asibitin. Har zuwa lokacin ba asamu RASLAN ya farkaba likitoci nata iyakacin bakin kokarinsu. Alhaji harun da alhaji musa suka tari dan uwansa da tambayar meyasa Annah suka nufa garin katsina yau ba taredamu sun saniba.." Alhaji umar yace "Saboda ita ta bukaci hakan naso sanar daku Amma duk tabi ta uzra.." Suka gamsu da mgnrsa, tareda mata fatan sauka lafia, time to time sunata kiran Annah a waya. Tana fita daga asibitin, ta tari me adai-daita sahu, ta hau kawai ba tare datamasan inda zatajeba, se hawaye wani na bin wani a kuncinta, bude bag dinta tayi ta dauko tissue ta hau goge hawayen dake zirya kan kuncinta, ji takeyi kamar zuciyarta zata buga saboda tashin hankali da damuwa, gaf hankalinta yanaga danta data baro yashe a kasan tiles din dakin, bazata jure ganinsa bane shiyasa ta fice daga asibitib. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Shine abinda taketa maimaitawa a zuciyarta ko zata samu sassaucin radadi da azabtuwar da zuciyarta take ciki, bata taba nadamar Auren Alhaji umar ba se yau, haka kawai taji tanajin haushin kanta ba tare datasan dalilin hknba, tadesan silar tsanar Auren daddyn Raslan saboda Annah ne. "Hajiya ina zan kaiki! Hajiya ina zan kaiki! Hajiya ina zan kaiki!!" Shine abinda me napep din keta fada Da dan daga sauti Amma sam bata jiba, ta riga da tayi zurfi a tunani,. Ta mirrow ya kalleta yaga se sharar kwalla takeyi da tissue haka kawai yaji tausanta ga zuciyarsa dan yasan ba karamin Abu bane yasata kuka saboda bega alamar wahala a tattareda itaba naira iya naira ta zauna ko daga fatar jikinta zuwa kayan dake jikinta ya isa ya yasashi gane hakan. Packing yayi a gefen hanya, ya juyo ya kalleta. "Hajiya nace ina zamuje!!!" Ya fada da karfi sosai. Firgigit ummih tayi ta dawo da dubanta garesa hadi da saurin share kwallarta tana kakalo murmushi dayafi kuka ciwo, ba tare datayi maganaba kawai ta kauda face dinta gefen titi... "Hajiya kin hau kuma baki gaya inda za a kaikiba, tin dazu se tafiya kawai mukeyi a kan titi...kuma inata magana baki jiniba..." Me napep din ya fadi hkn yana kallonta cikeda tausayawa. Ummih tace "Ayyah yi hkri banjika bane,....ina zuwa..." Ta fada hadi da zipping zip din bag dinta, ta ciro wayarta kawai ta tsinci kanta da dealing number din wata kawarta ko ince class mate dinta ada, wadda suka dade basu haduba tare sukayi karatu da ita rabonta da ita tin rabuwar karatunsu da a abuja take aure, mijinta police ne shine aka masa trnsper zuwa garin kaduna, a garin abuja nan sukayi krtun tare. Direct ta fada contacts dinta tashiga searching number din hajiya SAUDE nan da nan number ta fado ta danna dealing bugu daya ta daga. Daga bangaren SAUDE ta saki fara'a tana fadin "wai-wai lalle yau ranar fara take sol gareni, mrs U-safana kece kuwa ko kafarki nakeyi?" Cikin dakiya ummih tace "Ni ce , hajiya SAUDE har yanzu kuna kd ne?" Hajiya saude tace "eh muna kd Hajiya zainab..." Ummih tayi jim hadi da sauke Ajiyar zuciya kana tace " ina kd ganima a hanyar zuwa gidanki, wani anguwa kike?" Farin ciki ya lullube zuciyar SAUDE, amma tin a farkon, mgnr Ummih ta gane tana cikin damuwa, tace "Kai Amma Alhamdulillahi, kina ta dai-dai ina ne yanzu?" Ummih tace "Ina napep ne Ai banmasan a ina nakeba..." Nan SAUDE ta kara tabbatrda cewa Ummih na cikin damuwa, tinda tace mata tana napep, saboda tasan waye mijinta a Nigeria adduarh tashigayi a zuciyarta Allah de yasa ba rabuwa sukayi da mijintaba. Amma a fili tace bama me napep din wayar....ummih ta miqawa me napep din wayar ya miqo hannu ya amsa Hajiya saude ta masa kwatancen gidanta tsaf ya gane, ya miqawa ummih wayar ya juya kn napep din zuwa kawo new barrack. Suna isa bakin kofar gidan ummih ta kira saude ko dagawa tabayiba kawai ta ziro hijjabinta ta fito kofar gidan itama babbar macece kamar Ummih, sede ta dan girmema Ummih da kadan hajiya SAUDE nada yara uku duk basa kasar suna Germany karatu. . Fitowa ummih tayi daga napep din ta ciro kudi yan dubu dubu guda goma ta miqawa me napep din ya amsa hadi da zabgo mata godiya har suka shige cikin gidan ita da hajiya saude, kana ya tayarda napep dinsa ya fice a anguwar se adduarh yaketa jerowa ummih iri iri. A bedroom din haji saude suka yada zango suka zazzauna a bakin bed hajia saude ta cika mata gabanta da kayan maqulashe da tande tande ummih ta gaza ko shan ruwa. Hajiya saude ta fahimci hakan zaunawa tayi gefen gadon cikin damuwa ta zubawa ummih ido tace "Mrs U-safana meke damunku....please kada kice bakomi dannariga dana hango damuwa a kwance a kan fuskarki, kinga babu damar kiqi gayamin kiyi zurfin ciki dannasanki da zurfin ciki hajiya bamejin damuwarki inba aminiyarki hajiya hadiza ba,...dan Allah ki gayamin, ko ba komi zan baki shawara me kyau zainab ko in tayaji addu'arh, zainab ina jinki kamar yar uwata ta jini, dukda haduwarmu dake a school ne ko ba komi ai anyi zaman mutumci a school kuma anyi zumunci kecede baki dauki zumuncinmu da girmaba hajiya saboda Qawarki hajiya hadiza da batason kowa ya rabeki, amma ni harga Allah inasonki zainab dan Allah ki gayamin damuwarki...domin kowa ya ganki yasan kina cikin damuwa.." Hawayen da ummih taketa boyewa kawai suka ballo suka shiga zarya a kan kuncinta, kmr ranta ze fita haka takeji a kasan zuciyarta.... Hnklin hajiya saude ya kara tashi nan da nan damuwar dake ranta ta karu. Tahau rarrashin ummih hadi da ban baki, da kyar ummih ta sassauta da kukanta kawai ta tsinci knta dason ta sanar da hajiya saude damuwarta ko zata samu sassaucin zuciyarta. Ta kwashi komi ta gaya mata na kyautar Allah da Raslan kama daga kan haihuwar kyautar Allah har zuwa Aurensu da Raslan harma zuwa yanzu komi sedata gaya mata da matsalar Hajiya Annah. Hajiya saude ta sauke ajiyar zuciya tana nazarin Abubuwan da ummih ta gaya mata a zuciyarta, abinka da madu ilmin addini dana boko. Sauke ajiyar zuciya tayi ta rafka uban tagumi hannu biyu biyu, yayinda ummih ke jingine da bayan fuskar bed din har lokacin hawaye basubar bin kuncintaba, sede sun ragu ba kamar d'aba, tanaso ta tsayar da hawayen nata amma ta gagara hakan. "Wato hajiya zainab na fahimci wani abu a bayanan nan naki, inada tabbacin ku kanku baku san da hakanba, idan har lissafina da fahimtata sunkai inda ya dace, na fahimci cewa danki tin ranar daya daura idanuwansa a kan yarinyarnan ALLAH yasa masa sonta da kaunarta ga zuciyarsa, bazan taba mantawaba wani lokaci kin taba gayamin cewar danki ya bar cigaba da karatunsa saboda ita wannan yarinyar, sannan a knta ya hakura da kasuwancinsa ya dukufa gun kulawa da ita harta girma so kinga a nan ita kanta yarinyar da sonsa ta girma, sannan shine ya koyarda ita son nasa saboda yana sonta fiyeda yadda ku kuke tsammani, itama tana sonsa, dukkaninsu babu wanda ze iya rayuwa babu dayansa inhar dayan nasa na doron duniya, so a nan ina ganin dake ki so da ita kakar tasu ta so inda rabu dole zasu koma da Aurensu, in uban gijinmu yaso hakan...sannan yadda shi danki ya dandana yarinyarnan a yadda kika bani lbrin komi nasan baze taba kyaletaba, kuyima kanku kiyamun laini ku barsa da Auren matarsa tin be haifar muku da d'a mara idoba...a banza kina neman halaka danki na cikinki, haba zainab! Idan rai ya baci hankali shike tafiya yawon nemoshi.." Ummih tayi jim tana sauraron klmn Hajiya saude sannan tana tacesu a kwakwalwarta. "Hajiya saude a nan meye lefina?" Hajiya saude tace "ni bance naga lefinki A kan wannan mgnrba, saboda Ai nasan zuciya batada kashi, ko nice a matsayinki abinda zan Aikata kenan,Amma ko ba yauba karki kuskura ki rinka saurin cewa zan tsine maka, Wannan sam be kamataba ga uwa ta gari! , saurin cewa zan tsine maka be daceba sam-sam, hajiya karki biyewa wata taja ki tsinewa danki a bnza ta barki da asara.." Ummih tace "hkne Hajiya nima bacin Raine...ni yanzu hajia duk ba damuwataba , damuwata d'ana, dana baro a can yashe inason sanin ya yake Hajiya zuciyata da rauni, in yaronnan ya mutu bnsan ina zansa kainaba....." Hajiya SAUDE tayi jim kana tace "Ki sa wani Abu a cikinki se insan yadda zamuyi, kada ki damu ke uwace kiyita tsananta adduarhki a garesa, Allah ya bashi lafia..." Ummih ta rausayar da kai tace "Ameen hajiya SAUDE, ngde ....amma bna tunanin zan iya sawa cikina wani Abu harse naga yaronnan a wani hali yake ciki,..." Hajiya saude ta dafata cikin kwantar da hankali tace "ki kwantarda hankalinki yana cikin Aminci..dan Allah kisawa cikinki wani Abun inada tabbacin yau da wuyama in kinyi breakfast..." Ummih tace "wlhy banyiba hajiya, ni tin jiya da naji mgnr zuwanmu kd, hankalina yaki kwanciya..." Hajiya SAUDE tace "To kngani dan Allah sanyawa cikinki wani abun...." Hollandia yogurt kawai ummih ta iya yima kurba biyu ta ajiye hajiya saude ta tashi ta shirya ta sanarda me Aikinta in zata fita, damaan mijinta baya nan yaje wani aiku ogun state. Motar hajiya saude suka shiga, hajiya saudan ke driving suka fice daga gidan, zuwa giwa hospital. Suna isa garin katsina already daman umar ya sanar da dreva zuwansu dan haka nan suka samesa, da temakon wata ma'aikaciyar gun da jummai akasa kyautar Allah a motar wadda hawaye be bar zirya a kuncintaba haf lokacin. Direct asibitin da aka musu Transfer aka nufa dasu, suna zuwa aka basu daki aka kara duddubawata suka sa mata drive. kwance take knta na kallon sama yayinda zuciyarta ke garesa, kawai taji hawaye na bin kuncinta zuciyarta se tiriri kawai yake tasowa, "daddyna!" Ta fada a bayyabe still tana kwallah Annah dake zaune gefen bed din ta tabe baki zuciya fal takaicinta. "Ci gaba da kuka ki kashe kanki kinji, tinda de bakisan inda ke miki ciwoba, bakisan cewa duk fadannan da nakeyi a kanki bane kyautar banason ki shiga damuwa da matsala ko bayan bana raye, ki duba ki gani zainab bata kaunarki Haka kishiyarki wannan karuwar, bazaki iya kishi da itaba sam-sam, shiyasa na matsa kan ya
Chapter 121 · 0% Book details