← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 164

Sashe 120

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

a kan fuskar Raslan. Ba tare data Ankareba itama hawayen suka hau auna gudu daga kwayar idonta zuwa gefe da gefen idanuwan nata. "Ko zaka mutu seka saketa!" Annah ta fada cikin dakiya dukda taji tausansa Amma san batajin zata hakura da mgnr ya saketan, dan sam KYAUTAR ALLAH bazata iya da raslan ba, sam Annah Batayi tsammanin Raslan ze iya kusantar kyautar Allah ba seda ya Aikata taga zahiri, shiyasa takeso tasashi ya saketa saboda bataso a kuma abinda ya Aikata tanada tabbacin aka kuma sede a dauki gawar KYAUTAR ALLAH, to tabbas aka dauki gawar KYAUTAR ALLAH zeyi dai-dai da rasa ran Annah ne, duk duniya babu wanda Annah takeso sama da kyautar Allah, dan hk duk wanda ze cutar da KYAUTAR ALLAH dai-dai yake daya cutar da ita, har kwarama a cutar da ita, zata iya yafewa, Amma sam bata yafiya ga wanda ya cutar mata da KYAUTAR ALLAH, shiyasa bazata taba yafewa Raslan Abibda ya aikatawa KYAUTAR ALLAH. "Dan iska kawai!" Ta fada a hasale. "Kisa danki ya sakarmin jika inhar kinsan darajar uwarda ta haifoki, inde kin cika ke yar halak ce kisa danki ya sakarmin jika inde har ke ba yar titi bace...." Annah ta dawo kan ummih rai a zafafe take mgna. Mgnr tayima UMMIH zafi nan da nan ranta ya harzuqa zuciya bata da kashi kawai idonta ya rufe. Ta karasa ta cacumo Raslan ta hau sharara masa mari duka tako ta ina tana fadin "Ka saketa dan ubanka! Na gaji da mgnr da kake jawomin ka saketa nace ! Ka saketa dan bura uba kawai! dan kuka Mejawomin zagi dani da iyayena, saketa ko in tsine maka albarka! " kwata kwata idon UMMIH ya rufe se duka take kai masa tako ta ina Raslan dako gezau beyiba dukda dukan da ummih ke kai masa tin can karfin , Amma ko kadan bejin zafin dukan, pain din na kasan zuciyarsa. Zafin kalmar datace ya saketa kota tsine masa tafiye masa komi zafi a zuciyarsa. "Kiyi hkri ummih bazan saketaba!" Ya fada yayinda jini ke fita ta hancinsa, babu kakkautawa, saboda naushin da ummih takai masa ga hanci ya haifar masa da fitar jinin, abinka da jikin hutu. Ran ummih ne ya kara zafafa jin yace baze saketaba ta kara kai masa naushi a hanci saboda idonta ya rufe sam bata gani. Annah ta tsaya tana kallon ikon Allah,. Gaf ilahirin me ran dake dakin zuboma ummih ido sukayi wadda keta dukan Raslan kai dagani Kasan bata hayyacinta, ranta ya riga ya baci. Kowa nason dakatar da ita Amma yana tsoro. "Ki kasheshi! Kije gidan yari!" Annah ta fada cikin bacin rai, kai dajin yadda tayi maganar kasan ranta a bace yake da dukan da ummih keta yima jikan nata. Sam UMMIH batamajin me take cewa se duka kawai take kaima Raslan tincan karfinta, cikin fitar hayyaci da bacin rai daman tanada zafinsa. KYAUTAR ALLAH dakejin kmr ita ake duka duk hankalinta ya tashi, shi ake duka amma zafin ga jikinta take jinsa. Kawai seta fasheda wani irin mahaukacin kukan da batamasan sanda ta fashe dashiba tincan karfinta. "Dan Allah ummih kada ki kasheshi...Please! Wayyoo!! daddy narh!!! " ta fada cikin sarkewar murya irin na me kuka. Dukse kallo ya dawo gareta, ihsan kan ji takeyi kmr ta tashi taje ta shaqeta ta kasheta kowa ya huta, wani irin bnzan kallo ta gallarama KYAUTAR ALLAH, ita kam batamasan tanayiba. Raslan se yaji sanyi ga zuciyarsa ko yanzu ummih ta kasheshi zeyi mutuwar farin ciki, sannan ze mace da fara"arh a tattare dashi. "Ina sonki Rukayyah!" Ya fadi da karfi ta yadda kowa dake dakin seda yaji,.... Ran ummih ya kara baci a matukar harzuke ta kara daukesa da wani wawan mari, tana fadin "Ka saketa inba hkba wallahi tsinuwata ta tabbatr a gareka!'' Ta kara fada a zafafe. Anty rukayya taga zafin da Ummih ta dauka yayi yawa, fushin uwa ba karamin Abu bane ga dan cikinta, darajar uwa ta wuce misali. kawai ta taso ta krso inda suke, ta tsugunna saitin Raslan tace "Raslan Saketa please sbda umarnin Ummihnka please...." Raslan ya dago red eyes dinsa ya kalli Anty Rukayya ya girgiza kai zuciyarsa na wani mummunan harbawa. "Anty inna saketa mutuwa zanyi!" Ummih ta amshe cikin kunar rai "ko zaka mutu ka saketa dan ubanka! In baka saketaba na tsine maka har Abadan...." A matukar razane ya dago ya Kalli Ummih, yaga da gaske take sam babu alamar wasa a tare da ita. Maida dubansa yayi ga KYAUTAR ALLAH, wadda keta kuka har zuwa lokacin kawai ya maida knsa kasa had'i da fashewa da wani mahaukacin kuka kamar zararre. Cikin kuka ya fara magana, "Ummih zan saketa saboda bin umarninki, Amma badan inasoba, Wallahi inasonta itace Natsuwata, itace kwanciyar hankalina, na tabbatr inna saketa na rasa natsuwata har Abadan....." Ya yakara fashewa da kuka kamar ransa ze fita. Sosai kukan ke taba zuciyar ummih Amma ta danne saboda tafiso ya saketan kowa ya huta. Ita knta ta rasama Mike mata dadih a duniya. Kawai Anty Rukayya ta fashe da kuka, saboda tausayi, duk wata halitta dake dakin seda suka tausaya masa Amma banda ihsan wadda zuciyarta ke cike da dumbin farin ciki. Annah kanta jikinta yayi sanyi, ta tsaya tayi shiru. Yaci gaba da mgna hadi da kara rushewa da wani mahaukacin kuka, har numfashinsa na neman kwace masa. "Na....sa....ke.....ta......." Yana gama fadar hakan ya zube kasa hadi da jawo numfashi da Mugun karfi, tin daga haka numfashinsa be kara harbawaba. *MANAGE NAYI BUSY WALLAHI BIKI MUKEYI.....* KYAUTAR ALLAH... *PAID BOOK...500 ONLY...08136349646* *YA ARRAHAMANIRRAHIM* "Wayyo Allahnah nashiga uku! Na bani! Wayyo daddy kar ka mutu ka barni! Dan Allah ka tashi daddyna!!" Shine Abinda ke fita daga bakin KYAUTAR ALLAH wadda duk tabi ta dimauce ta fita hayyacinta, saboda ganin daddynta a kasa warwas kamar gawa, ba karamin dimautar da ita yayiba nan da nan ta nemi yawo a bakinta ta rasa, ta hau kuka tana ihu . Yunkurin miqewa tsaye tashigayi dan tasamu ta karaso garesa, shap tama manta da ciwon dake kafarta, saboda ta shiga gigita iya gigita.... Jummaice ta taso a guje ganin tana neman tashi da ciwo a kafarta kowa be Ankaraba saboda hankalinsu ya koma kan RASLAN....da sauri jummai ta karaso ta riqeta tana fadin ki natsufa da ciwo a jikinki."ki barni inje gun daddy na please!" Shine abinda ya kara fitowa daga bakinta ba tare data masan waye me dannetanba, but idanuwanta duksun rufe. "Yau kika kashemin jika Wallahi kema nice ajalinki zainabu! In bn zama ajalinkiba kice ni ba cikakkiyar yar katsinawa bace!!" Shine abinda ke fita daga bakin Annah rai a bace har tana buga kirji idonta na kan ummih wadda ke tsaye zuciya na tafarfasa, idonta na kan danta dake sume jin hawaye na neman kubucewa daga idanuwanta, kawai ta suri bag dinta dake kasa ta fice daga dakin hawaye na bin Kuncinta na tausan danta tilo daya duk duniya, takaicin kanta ne ya rufeta. farin cikin, dake cike da zuciyar Ihsan baya misaltuwa ji takeyi kamar Anyi mata KYAUTAR Aljannar. Seta fashe da kukan munafurci hadda shasheqa, ganin mijinta a sume. Alhaji Abdullahi da na'im ne suka cincibesa suka fice dashi daga dakin, Anty rukayya and anty sadia maman na'im, DaddyU daddyH daddyM duk suka mara musu baya, kowannensu zuciya babu dadih. Na'im da Alhaji Abdullahi, su suke riqe da Raslan din, direct emergency room suka nufa dashi nan da nan likitoci suka dukufa a Kansa ganin baya numfashi. Nan wajen emergency din duk suka tsaitsaya kowannensu yanata adduarh Allah ya tashi kafadun RASLAN din. Nan dakin suka bar Annah da jummai da KYAUTAR ALLAH, wadda har lokacin se kuka takeyi jummai na danneta tana yunkurin miqewa...Annahh se tsinewa Ummih takeyi. A karshede tace baza ayi kisan kai tana nanba, haka kawai yan sanda suzo su kamata, ta dauki mayafinta ta fice daga dakin tana fitowa ta hango umar da hanzari ya karaso inda take, "Annah ina zaku? Ko kunada bukatar wani abune?" Haka kawai se Annah taji kunya ta rufeta na yadda umar be nuna komiba dukda itace silar komi daya samu dan nasa. Nan ta gaya masa so takeyi subar garin zuwa katsina yanzunnan,.. Umar yace su bari zuwa KYAUTAR ALLAH ta samu sauki mana, Annah ta daka tsalle tace Aah ai yau mutuwace kawai in tayi ze hanata zuwa garin katsina. Umar yace tou, ta koma ciki bari yaje ya samu doctor tace tou hadi da juyawa ta koma dakin, shi kuma ya nufa office din dr hannatu a bakin kofa sukaci karo tana sauri zata nufa emergency inda RASLAN yake kawai sukayi kicibus. Nan ya sanarda ita bukatar Annah dr tace bazeyuba inhar a mota zasu isa garin katsinar, umar yace ah'ah jirgi zasu hau.. Dr hannatu tace to bamuwa.amma ba hk tasoba, taso ace taci gaba da bawa KYAUTAR ALLAH kulawa har tasamu sauki. Komawa office tayi ta rubuta trnsper zuwa wani asibiti babba dake garin katsinar wanda takeda connecting dasu ta tura musu sauran byanan ta system. Ta bawa umar takaddar tareda ita dashi da wata nurse wadda ke daukeda wani basket suka nufo dakin, harma Annah da jummai sun gama shirya KYAUTAR ALLAH cikin doguwar riga an yane mata knta da dankwalin rigar, har lokacin se kuka takeyi, tana kiran sunan daddynta Annah batabi ta kantaba. Wasu allurori dr tayi kata kana ta bata wssu magun guna tasha da kyar tanayi tana kuka. Alhaji umar ya dauketa cir yasata a black car din dasukazo a ciki, se kuka takeyi Annah ta daka mata tsawa dole ta natsu... Annah da jummai suka shiga gidan baya Umar ya shiga front seat dreva yashiga yaja sukabar asibitin suka hau titi motar securities na biye dasu a baya. KYAUTAR ALLAH dake kan jikin Annah da jummai se hawaye takeyi me zafi harga ALLAH tanaso taga daddynta. Tin kafin su karasa airport din Alhaji umar yasaya muku ticket din zuwa katsinar Abinka da kudi sam babu bata lokaci suna isowa kawai suka shiga jirgin. da dabara Alhaji umar ya zaunar KYAUTAR ALLAH a kan seat din jirgin da kyar ta iya zaman amma taji sassaucin jikinta sosai. Alhaji umar yayima Annah Asauka lafia, ta amsa da Ameen, sukayi sallahmade, cikin ladabi. Yana gani har jirginsu ya tashi kana ya
Chapter 120 · 0% Book details