← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 164

Sashe 117

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya turo musu da lambar dakin, dan haka direct suka shiga cikin Asibitin. Alhaji umar da Abdullahi sune a gaba. Se ummih da ihsan da sadia suna biye dasu a baya. "Dan Allah ihsan ki sasssuta dacin ciwngom dinnan please.." Ummih ta juyo tayi mgnr ga Ihsan dai-dai sun shigo cikin Asibitin. Ba tareda ihsan tayi mgnaba ta dan sassauta da cin ciwngom din, ammafa batabar cin ciwngom dinba.Anty sadia dake jinsu ta taba baki kawai ba tareda tace komiba, saboda yanzu datayi mgna ummih zata hayayyaqo mata, daman tin a jirgi suketa harare harare itada ihsan din kmr wasu kishiyoyi, gabaki daya sun tsani juna, musammanma Anty Sadia ta tsani ihsan fiyeda tunanin duk wani me hankali. Ummih kam a kan ihsan sunma dena jituwa itada Anty sadiar, saboda sadiade bata gani tayi shiru, ita kuma ummih inde a kan ihsan ne bataqi ta bata da kowaba. shiyasa ita kuma ihsan take tsula tsiyarta son Ranta, dawowar gidan ta amshi kudi a hannun ummih fiyeda tunanin me tunani, kudinma data Amsa sunyi yawa, kawai sede tayita barnarta da kudi ta kaiwa uwarta rabi suyita bushasha daman hajiya hadiza ido a nera ai babu dama, seta kara gwangilar bleaching, dabin manya manyan bokaye. Tin kafin su iso bakin kofar dakin idon ummih ya sauka a kan Raslan, kallo daya ta masa ta gane a hargitse yake, dukse yayi mata wani iri, gashi ya rafka uban tagumi, ga bandeji ga kansa, haka kawai ta tsinci gabanta da faduwa Ras! Ras!. A hnkli ya dago idanuwansa, jin kamshin perfume irin na ummihnsa, dago kansa dazeyi ya sauke kwayar idaniyarsa a kansu. Miqewa tsaye yayi, yana qoqarin qarasowa inda suke, dukse suka bishi da ido, musamman ihsan da ummih. "Sannunku da zuwa harkun iso.." Ya fada yana shafar cikinsa da babu komi, harma ya fara masa ciwo ciwo ga bakinsa ya masa nauyi saboda rashin brush, jikinsa kuwa se amsa kuwwar ciwo ciwo yake masa, saboda rashin wanka, ya riga yasaba tin Asubah yake wanka kafin yaje masallaci, yau dabeyiba dukse yaji beji dadihba, yana jinsa a rabin mutumne. ga damuwar kyautar Allah mamaye kaf-kaf da zuciyarsa. Alhaji Abdullahi da Alhaji umar ne suka amsa fuska sake, tareda tambayarsa yame jiki, ya amsa da da sauki,. "Son how farh..." Cewar Anty sadia data qaraso inda yake ta daura guiwar hannunta a kafadarsa , suka kalli juna ya sakar mata murmushi itama ta sakar masa murmushin, a haka suka gaisa, ya gaida ummih ta amsa , babu yabo babu fallasa,se binsa takeyi da kallo kawai. Ihsan kam se wani hararsa takeyi, zuciya fal bakin cikinsa, daman tanada haushinsa na zuwa da yayi ya tare a Kaduna, Ko kiranta bayayi, ya mayarda ita banzar bazara ita kumafa tanason mijinta, kullum seta kalli hotonsama take iya rintsawa musammanma a yan kwanakin nan. Raslan de satar kallonta kawai yayi ya dan lashe lips dinsa, ga kaya nan yana gani acan-acan... A tare suka karasa cikin dakin. "Son kayi fresh abunka, jininka yayi acan-acan dashi, Anya ba kyautar Allah bace ta mayar maka da naka jinin sabo, kamar yadda nata yake sabo kar..." anty sadia ta fada, dai-dai suna shigowa dakin seda ta bari Ihsan na daf dasu ta yadda zata iya jiyo komi, kana tayi mgnr hatta ummih tajiyo mi tace, Amma tayi kmr batajiba, ihsan kam rantane yayi wani irin jahilin baci, taji kamar ta hadiye zuciya ta mutu, dajin abinda Anty sadia ta fada kwara ta mutu a cewarta. Raslan kam murmushi kawai yayima Anty Sadia idonsa na kan ihsan Se tafiya takeyi tana jijjigar jiki, shi kuma uban yan kwad'ayi har yaji kwad'ayinsa ya tashi, Amma ya shanye danyasan ba samu zeyiba, sede kwad'ayin ya kasheshi.musammanma yadda take ciki dashi dinnan, yasan inya kuskura ya kusancetama zesha magana, dukda durin bb dadih, daza a bashi zeci yayi manage wai ance a rashin uwa ake uwar daki. Tin shigowarsu dakin idon ihsan ya sauka kan KYAUTAR ALLAH hk kawai taji gabanta yayi mummunan faduwa, .... Duk karasawa sukayi suka tsugunna suka gaida Annah tareda tambayarta yame jikin. dukkaninsu ta bisu da kallo ta tabe baki kana tace "Lafia lau abdullahi,lafia lau umar...lafia lau sadia danba halinkiba..ku sauran ku riqe gaiguwarku bana bukatar, ko ince baku isa in amsa gaisuwar takuba tsofaffin karuwai, waiku inaso in tambayeku, ba ayi muku tarbiyar sa hijjabi bane...duba kuga waccen wadda ta gama bada gindinta ma mazan duniyama tasa hijjabi a mutumce wanima ya ganta a haka bazece ta ajiye yar shegeba da ba asan ubantaba, to ta yayama za asani tinda mazan dasuka cita sunfi dubu dari da saba'in... kede zainabubu, jininki beda kyau Wa billahillazi! Allah yafi Annabi sani banji dadin zuwanki zuri'arh taba! Gashi kin haifo mana gawurtaccen dan iska mara ta ido..." Annah kawai ta fashe da kuka tana sharar kwallar da babu se kwakulota takeyi kawai. Nan umar ya hau rarrashinta " dallah rufemin baki, duk wayaja mana matsifar inba kaiba...bakasan Asalin anguluba Amma kawai daga ganin sarkin fawa se miya tayi zak'i, uhm ka auro mutsifa ta haifar mana Annobar...to Wallahi yau seya sakarmin jikatarh dan uwar uwar uban ubansa..." Raslan dake tsaye tin shigowarsa ya tabe baki, ko a jikinsa. "Ayi hkri dan Allah hajiya Annah, bawon Allahn nan yanason yarinyar nan, itama tana sonsa, dan ALLAH a barsu tare,mutuwar Aure bata da dadih ko ga uban gijinmu..." Cewar Alhaji Abdullahi dayasha nad'in buzaye. Annah ta table baki ta yamutsa hanci, ta Waskace baki gefe daya, tace "A gidan kakan waye akace mata tana sonsa, kai inma tana sonsa yau sede ta mutu dan bura ubata seya saketa, kajini da kyau kou!" Ta karashe mgnr tana kamo kunnenta daya ta riqe Alhaji Abdullahi yaja bakinsa yayi shiru saboda Abun yafi karfinsa. "Ku zazzauna, ai yau bura ubace kuma za ayita ta kare,....kirawomin wnnan dan muji ya iso, danse kowa ya iso zan jaku daya bayan daya in nuna muku Aika Aikan da shegen nan yayiwa yarinyarcan, shege jinin marasa imani..." Cewar Annah, data krshe mgnr da idonta tar a kn musa. Dealing number din harun yayi yace tambayesa sun iso yace sun iso sunama gab da shigowa cikin Asibitin, yace to kna ya katse wayar. Annah taci gaba da sirfafowa ummih zagi, wadda zufa keta keto mata tinkanma taji me dan nata ya aikata, sam zuciyarta bata kaiga ze ci yarinyarba, Ammade tasan lefin daya Aikatan babbane tinda harya dawo da Annah daga Kasa me tsarki. ihsan kam se rarraba ido takeyi tana hango KYAUTAR ALLAH dake a kwance a kan gadon itama idonta na knsu, musammanma ihsan din datake karajin tsanarta fiyeda ada. Ihsan na karewa KYAUTAR ALLAH kallone danta hango abinda Annah tace zata nuna musu, bata hango komiba se bandeji dake kafarta, se riga kuma da bata dashi ita ga zatonta ko zafine yasa ta cire rigar hkma Ummih tayi tunani tin shigowarta dakin data ganta babu rigar. Anty Sadia de batayi tunanin komiba ta bari Annah ta fallasa musu komi, Amma itade jikinta na bata Raslan yayi Aika Aika ne dan tasan halin son dinta. Ummih kam gabanta se tsananta bugu yakeyi, hakan take ga bangaren Ihsan, se zazzare ido takeyi.. Alhaji harun da matarsa, se dansa Na'im, da Raslan again wanda Aka gama kora yanzunnan, Amma dayagansu shine ya biyosu, dan kulafushin yazo yaga KYAUTAR ALLAH ko ze samu sassauci a ransa. Karasawa Harun yayi da iyalin tasa suka tsugunna suka gaida Annah, hadi da tambayarta yame jikin, amsawa tayi babu yabo babu fallasa, kallo daya zaka mata ka gane ranta a bace yake, idanuwanta sunyi luhu luhu, saboda daren jiya sam bata rintsaba. " dan bura ubaka kai baka iya gaisuwa bane, shege kasha matsatstsun kaya kamar yayan turawa,..." Ta fadi hakan tana kallon na'im wanda ke tsaye yasha kana nan kaya wadanda suka Amsheshi sosai. Murmushi yayi na han dakiqu kana kuma ya hade rai kmr bashi yayi murnushinba yace. "Ina wuni..." Annah ta saki baki, cikeda haushi tace "A gidan uwarka aka wuni yanzu, dan bura uba kai da shegen katon kai kamar yayan aljanu," Na'im da yana sane yace mata inawunin kawai seya fashe da dariyar shaqiyanci, kana yace "zaki fara zage zagen naki kou....shiyasa nace bazanzoba amma DaddyH ya matsamin, nariga da nasan ba wani Abu bane yasa kikeson taramu, kawai so kikeyi ki tasamu kiyita zagi, kina kwashe mana Albarka, haka kawai..." Annah ta zaburo daman a wuya take tace "An zaga dan kwal uba ka, shege dan durun uwa kai! Damanfa kai na jima da sanin halinka, bakada tarbiya kwata-kwata an girmane ba asan an girmaba, ni gabaki dayanku banmasan wadanne irin jikoki baneku, sam babu me kunya a cikinku, duk yan iska ne ku, yan bura uba..." Na'im yace "Godiya muke, hajiya Annah Da girmar kujerarki, na baki sarautar zagi a garin katsinawa...." Nan ta kara mulmulo wani zagin ta mulmula masa, me mugun zafi sam ma baze faduba a bakina. Na'im ya kame baki, saboda jin girman zagin, yace "Ah'ah a huce haka hajiya Annah, Ki huta kakus, A tsirace, kiyi shekaru irin na ginin kasa...." Yadda yayi mgnr seda ya bawa kowa dariya ammafa ciki ciki suka dara, Raslan dake gefensa a bayyane yayi dariyarsa, ya harde da jikin bango, danyace a wannan karon ko an koreshi Wallahi baze fitaba, sede Annah tayita tsine tsinenta ta gaji ta bari. ""Inka kara magana se naci durun uwarka! Wlhy zan barka da tabo! Kamar yadda nabar Wannan mara kunyar da tabo..." Ta krshe mgnr taba nuna raslan. Ummih tabi Raslan din da ido waylto Annah ce taso illata mata d'anda, taboma a tsakiyar kai. Ba kramin zafin hkn Ummih taji ga rantaba Amma dole tayi hkri. Na'im naso yace wani Abu Amma yy shiru gudun kada shima a illatasa irin na raslan dan yasan kadan daga aikin Annah kenan. "Yauwah!" Annah tace hadi da miqewa da kyar ta dauko sandarta ta dogara, ta duba UMMIH galalah, kana ta bude, hanci hadi da baki tace "taso kiga abinda dan iskan danki, ya Aikata, ma yar afiruwar jikatar, ..." Ba musu UMMIH ta miqe tabi Annah zuwa bakin bed din. Annah ta fara nuna ma Ummih kafar kyautar Allah, ba taredatace komiba, kana ta nuna mata nonuwan kyautar Allah harya zuwa wuyanta, duk ba tare datace komiba, Rintse ido KYAUTAR ALLAH tayi
Chapter 117 · 0% Book details