← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 164

Sashe 148

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

sukayi hadda ita kanta uwar gayyar KYAUTAR ALLAH. "A gidan ubanka cikin ya zama naka!! Dan kutmar ubanka!inka kara magana a dakinnan sena ci maka mutumci!" Annah ta fada cikin bacin rai da kunar zucia, taci gaba da magana tana kai dubanta ga Alhaji umar. "Ka gani ko umaruru! Yarinyarnan ta tonamin asiri a garin katsina ta tozartani! Taci amanata! Duk son da nake mata amma sakayyar daza tayimin kenan! Wallahi kin cuceni KYAUTAR Allah!!" Annah Ta karashe maganar tana fashewa da matsanancin kuka idonta na kan KYAUTAR ALLAH, itama tini kwalla suka fara fita daga kwayar idonta... Ganin kwallah a kan fuskarta ba karamin tayarma da RASLAN hankali yayiba, duk ya daburce ya gigice ya fice a hayyacinsa, ya karaso ya tsugunna a bakin gadon ya kamo hannunta ya shiga bata hakuri. "Kukannme kikeyi jewel? Kiyi hakuri knji jewel dina! Banason ganin hawayenki! Hawayenki na tayarmin da hankali! Hawayenki barazana ce ga rayuwata." Ya shiga jero magana kamar zautacce. Duk suka bishi da ido,...Annah ma binshi tayi da ido tana kallon ikon ALLAH.. Alhaji umar ya karaso ya zauna kan kujerar dake kusa da bed din, Ya kai dubanshi kan RASLAN shima juyowa yayi ya fuskanceshi. "Cikinane Wallahi daddy! Ni nayi mata ciki! Dan Allah ka gayawa Annah ciki nane ! Ni da kaina na mata cikinnan ba wani ba! Ina son matata daddy! Inason cikin dake jikinta! " yayi mgnr kamar ze fashe da kuka. Alhaji umar ya zuba masa ido kai daganin yadda yake magana kasan yanason KYAUTAR ALLAH ko ba a fadaba. "Ta yaya ya zama cikin ka bayan kun rabu?" Alhaji umar ya jefo masa tambayar shima cike da rudani a zuciyarsa se addu'arh yakeyi Allah yasa bata hanyar zina aka samu cikinnanba danyasan halin danshi sarai ze iya abindama yafi haka, saboda yanada rawar kai. "Wallahi ciki nane daddy! A bincika a gani ciki nane!" Cewar RASLAN dayake a gigice tsoron ALLAH tsoronshi kada Annah tace ya saki KYAUTAR ALLAH dan yasan zata aikata abinda yafi hakan, da besan inda zesa kanshi ba a wannan karon. "Karya kakeyi dan ubanka! Kana juya, a gidan ubanwa zaka samu kwayar haihuwar daza kayi mata ciki!" Annah ta dakawa RASLAN tsawa. Kowa na dakin bin Annah yy da kallo, dr zilai abunma daure mata kai yayi tace "hajiya dakin bari yayi bayani tinda yace cikin shine aita kwana gidan sauki,..." Annah ta dakawa dr zilai tsawa. "Ubanwa ya sako bakinki a nan sarah! Uwar shishigi mage me kwanciyar daukar rai! " dr zilai taja bakinta tayi shiru tana kallon ikon ALLAH. "Kaima inka kara magana a dakinnan sena kwashi k'ashin bura ubaka!" Annah tayi mgnr idonta na kan RASLAN,shima kyar ya tsayar da kwayar idonsa a kanta. "Dan bura ubaki ki bude baki kiyi magana cikin dake jikinki na uban waye?" Ta juya akalar maganarta ga KYAUTAR ALLAH wadda keta kuka har zuwa lokacin...kasa tayi da kanta still tana kuka kmr ranta ze fita. "Wallahi cikinane, gatanan ku tambayeta cikinane,..." Cewar RASLAN. Annah tayi jim tana hango kamshin gaskia a maganarshi "ta yaya ciki ya zama naka kana juya... Wai banace karka kara maga a dakinnanba!!" Ta karashe maganar tana daka masa tsawa. RASLAN ya dafa kafafuwan alhaji umar wanda ya zuba masa ido yama rasa ta ina ze bullowa al'amarin. "Daddy ma gaya maka cikinane, na riga dana maida matata tin tini c ikin dake jikinta ni nayi matashi, ta fada muku da bakinta gatanan, tsakaninki da ALLAH cikin dake jikinki ba nawa bane?" Ya karashe mgnr idonshi na kn KYAUTAR ALLAH kasa ta karayi da kanta still kwalla na zirya a kan fuskarta. "Gaskia koni shaidace cikinnan na Alhaji karamine, Annah aide kinsan tarbiyar da Kikayima KYAUTAR ALLAH inba tsautsayiba bazata iya bawa wani d'ana miji jikintaba inba shi Alhaji karamiba dayake matsayin mijinta....dan ALLAH Annah kiyi hakuri ki barshi da matarshi tinda yace ya maidata sannan Allah yasa da rabo, kinga ko wannan ma isharace ALLAH ya nuna a nan, tinda kinsa ya saketa kuma ya maidata ga rabo ya samu dukda karancin shekarunta,..." Annah tayi shiru tana sauraren kalaman dake fitowa daga bakin Jummai, taso dakatar da ita ta zabga,mata rashin mutumci Amma batayi hakanba Haka kawai taji jikinta yayi sanyi. Ganin hakan yasa RASLAN fara magana cikin sanyin muryar "Allah ma shaidata ne, na maida iyalina, seda ta zama halak dina kana na fara kusantarta , cikin jikinta nawa ne halak malak, dan Allah Annah kiyi haquri karkice zaki rabamu.." Ya karashe maganar kmr me shirin fashewa da kuka, Annah ta zuba masa idanuwanta dake cikin glass bata taba ganin jikinsa yayi sanyiba irin na yau. Haka kawai taji ta amince jikinta yayi sanyi xuciyarta ta cika da farin ciki ta sauke ajiyar zucia. "To shikenan, Allah ya rabata da cikin jikin nata lafia..." Sosai kowa yaji dadin kalaman Annah cikin sanyin murya, babu wanda beyi mamakin sanyin datayiba a wannan karon. "Amma de RASLAN kai macucine, kema KYAUTAR ALLAH macuciyace ashe muna gida daya, yana zagayewa yana miki abubuwa, Amma dan munafunci baku taba gayaminba, munafuka kawai, ashe haka kike bansaniba! To gashi ynzu ALLAH ya toni asirinku..." Annah ta fada cikin tsiwa, kowa ya zubo mata ido zucia fal wani mamaki yanzufa ta gama mgnr arziki kuma ta dawo ta tsiya, "me hali baya barin halinsa!" RASLAN ya fada a ranshi . "Shikenande tinda me faruwa ya riga ya faru A kawo fatiha kafa dari da hamsin ALLAH ya raba jikata da cikinnan lafia..." Kowa dake dakin seda daria taso subuce masa wai fatiha kafa dari da hamsin, Amma duk suka hadiye dariyarsu, gudun kada su jawa knsu zagi. "Tsufa labari" alhaji umar ya fada a ranshi,ada ko an gaya mishi mahaifiyarsu zata zama hakan baze taba yaddaba, sude duk yadda zata zama suna sonta a matsayinta na mahaifiyarsu, uwa uwace koda ace tana yawo a kan bola ne. Addu'ah suka shiga jerowa Ammafa ba fatiha dari da hamsin ba. Kowa dake dakin seda ya tsinci kansa a farin ciki hadda Dan liti daya tsinci wasu abubuwan dasuke cewa. Aka shafa addu'arh da fatan ALLAH ya sauki KYAUTAR ALLAH lafia. Annah ta nisa kana ta kai dubanta kan raslan tace "mashahurin maci amana, data haihu zaka saketa dan kutmar ubanka, tinda ba kanwar babarka bace..." RASLAN ya yatsina fuska yace "meze hana kice insha maganin kwari in kashe kaina kawai kowa ya huta..." Annah ta gallara masa harara tace "Nan kafi auki gun rashin kunya, rasa kunya beran tanka!, dan k'ashi da tsoka kawai... Kayima danka katangar dalma da gidana, harse KYAUTAR ta haihu se yazo ya ga yarsa ya hado da takaddar saki kuma.." RASLAN da baki ya bude yace "Wasa kenan..." Annah tace "kanwar uwarka tsohuwar karuwar nan itace take wasan!" RASLAN yayi murmushi halin Annah se hakuri. "Wait! Hajiya Annah wai naji da kika shigo kina mgnr nace zan kasheki ne! Sharrin da kika kullamin kenan?" Cewar RASLAN da mgnr ta fado masa rai yanzu. Annah tace "Ai zaka aikatane shiyasa nayi gaggawar tarar abun, saboda kai dinnan babu abinda bazaka aikataba, tinda ka lallaba ka narkawa jikata narkeken ciki, ina gidan, kai nimade se a hnkli!... " duk yan dakin Seda suka kwashe da daria inka cire umar da KYAUTAR, wadda kanta ke kasa, se dan liti da besan komiba ... Annah ta mulmulo wani zagi dukta mulmula musu, tini sukaja bakinsu sukayi shiru... Tasowa Annah tayi daga kasan tiles din datake zaune zaman dirshen, ta dauko sandarta ta dogara ta karasa bakin bed din da KYAUTAR ALLAH ke kwance ta hau jero mata sannu tana nadamar dukan data mata jiya. "Sannu kyautar, An munafunceni, anci dadih gashi yanzu ana gurzar wahala to ALLAH ya raba lafia...." KYAUTAR ALLAH tayi kasa da kanta cikin kunya... "Zuwa anjima za ayi miki scanning..." Cewar dr zilai Annah tace "tou tou shikenan likita, to shi cikin na jikinta watanshi nawa?" Ta karashe maganar tana murmushin farin ciki. Dr zilai tace "Wata biyu ne hajiya..." "To Alhandulillahi..ashe zanga jinin jikarnan tawa, Kai ALLAH na gode maka..." Ta karashe mgnr tana daga hannayenta sama cike da godiyar ubangiji. Kowa na dakin seda farin ciki ya rufesa, musammanma RASLAN. Da yammaci akayi mata scanning din kmr yadda dr zilai tace,,, dr zilai ta jawo RASLAN office dinsa ta masa gargadi kan bnda sex saboda in aka cika matsa mata cikin ze iya zubewa. Jim RASLAN yayi zucia babu Dadih Amma dole yayi hakuri. "Dr dan ALLAH ko kadan kadan bazan iya yiba..." Yayi mgnr hadi da marairaicewa. Dr zilai ta zuba masa ido kana tace "Ai daka cika matsawa cikinka ze zube, kuma kaga yarinyarnan tayi karama da daukar ciki, kaga ai abar a tausaya ce....plx kada ayi making love da ita se in cikin yayi kwari dan ALLAH, sannan banda aikin wahala..."_ RASLAN yace "To dr kamar yaushe ne cikin zeyi kwari?" Dr zilai tace "Kamar nan da 2 month to 3 month haka..." RASLAN ya zaro duk idanuwansa waje yace "What! Habade!" Dr zilai ta daga masa kai alamar tabbatrwa. "Yayi yawa mana dr, Dan Allah babu wani abu daza a dan iyayi..." Yayi mgnr hadi da marairaicewa. Dr zilai ta zuba masa ido tana karantarshi ko be fadiba ta gano shi mayen sex ne. " kuskure kadan inyasa ka shiga yarinyarnan zaka fito da cikinka waje..." Jim RASLAN yayi kwayar idonsa na yawo a kan dr zilai, tabbas yanason cikinnan na jikin jewel dinsa fiye da yadda yakeson rayuwarsa, a halin yanzu komi nasa ya tattara ya daurawa cikinnan na jikin KYAUTAR ALLAH, du burin duniya inyazo ranshi to a kan cikin nan ne na jikinta. "To zan kiyaye..." Ya fada jiki a sanyaye. Accout din dr din ya amsa nan take ya tura mata makudan kudi, tukuicin fadar kyautar Allah nada ciki, sosai dr zilai taji Dadih saboda kudaden sun so gigita mata lissafi, nan ta shiga jero masa godia, Yace mata ba komi ta cancanci mafiyin hakan, daga haka ya tashi yabar dakin. Washe garin ranar Alhaji umar ya koma garin abuja, shima bayan ya cika dr zilai da goron albishi. koda ya isa abuja be sabar da ummih komiba. Nan Annah da Jummai ke kwana dashi kanshi gogan, ko Annah ta korehi be tafiya, kullum cikin siye siye yake siya wancan siya wannan, duk KYAUTAR ALLAH
Chapter 148 · 0% Book details