Sashe 109
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 4 min read
marairaice maka uwa basu da uwa da uba..." Ta fada a ranta. A fili tace "Ba dole in hakuraba kakah, Ai abu inya riga ya afku se Hakurin dole, se kuma a kiyaye gaba, Allah ya kiyaye gaban..." Yayi saurin Amsawa da " Ameen, ai insha Allahuma bazan karaba, kadan kadan kawai zanyi tayi, insha Allahu,..." Anty Rukayya tayi tagumi da hannu daya , ta zuba masa ido, wato har ynzude bb mgnr baze karaba, sede yace zeyi kadan-kadan. "Wannan kadan-kadan din da kake cewa Amma inta kara girma kake nufi ko?" Anty Rukayya ta jefo masa tambayar. Ya kwalalo ido hadi da marairaicewa " haba mommyR, nifa na miki alqawarin bazan kara irin hkba Wallahi, kadan kadan dinde, koba hkba?" anty Rukayya tace "toh'' kawai. Mikewa yayi da niyar barin dakin ya nufa gidan. Wayar anty Rukayya tahau ruri, tsayawa yy cak. Cikin hanzari Anty Rukayya ta dago wayar dake kan jikinta, taga number din daddyne. Raslan ya juyo ya zuba mata ido yace "Annah ce?" Girgiza masa kai tayi tace "Ba ita bace daddyM ne..." Ta karashe mgnr murya ciki da rauni. Raslan yace "Kiyi picking..." Anty rukayya tace "mezance masa? Nasan Annah ce ta kirshi tasashi ya kirani, saboda naki picking call dinta..." Raslan yace "Yeah itace, Ki daga kiji mezece, ki gaya masa gaskia, nagade ai matata naci ba wataba, kawai ki gaya masa komi..." Anty Rukayya ta bishi da ido, Yana mgnr ko a jikinsa. Wato yaci dadih, ita kuwa ya barta da zullumi da faduwar gaba, shi damuwarshi dayace kawai tasamu lafiya yaci gabada lafta mata jela. Wayarce ta kara daukar ruri DaddyM ne, dagawa tayi gabanta na faduwa, zuciya cike taf da firgici. Tana kara wayar a kunne ya hau balbala mata balbalin bala'i. "Wani irin wulakncine wannan! Tin dazu ana kiran waya kinki dagawa, Hajiya Annah ta kira yafi a kirga, cemin tayi tin tsakar darw take kiranki, har zuwa asubahi, kinki dagawa, Alhalin nasan kina gani, saboda nasanki bakya ajiye wayarki da nisa, akwaide wani abunda ya hanaki daga mata waya, kinbi kin dagawa uwata hankali a banza a hofi, gaskia kin batamin rai, baki taba batamin rai irin na yauba, Wacce iriyar lalacewa wannan....kin dagawa uwata hankali" Sassauta murya tayi tace "Allah ya huci zuciyarka sarki, me mulkar zuciyata..." duk haushin daya debo nata se yaji ya dan sauka kadan. "Yanzu ina KYAUTAR ALLAH take, Tin jiya Annah tace tanata kiranki ki hadata da yarinyarnan suyi waya, Amma kikace tana bacci karshema kikaki daga wayar, wannan ai wulakncine..." A zuciya Anty Rukayya tace "Abun na Annah hadda sharri..." DaddyM yaci gabada mgna "kiyi gaggawar sanar dani mike faruwa, dan nasan ruwa baya tsami banza a hofi..." Anty Rukayya tayi jim, zuciyarta na tsananta bugu ta dago ta kalli Raslan wanda ke tsaye har zuwa lokacin, shima ita yake kallo Amma bayajin mi suke cewa. "Badake nake maganaba!" DaddyM ya daka mata tsawa. Firgigit ta dawo hayyacinta, kawai ta yanke hukuncin gaya masa gaskia. "Muna asibitine yallabai,..." A bngaren DaddyM yace "Asibiti yin me? Waye babu lafiya?" Ya jefo Mata tambayarnan data kara surar da ita. "Kyautar... Allah.. ce babu lafia..." Ta fada murya na rawa ta rintse idonta gam, kai kace a gabanshi take. "asibiti? Wani irin asibiti? Waye babu lafia?" DaddyM ya tambaya shima cikin tashin hankali. "KYAUTAR ALLAH..." Anty Rukayya ta bashi Amsa still idanuwanta a rufe suke gam-gam. Dayake DaddyM yasan problem din da KYAUTAR ALLAH kedashi na ciwon zuciya dan hk se yy zaton ko ciwon ne nata ya tashi, sam be tambaya meke damuntaba. "Shine baki kirani kin sanar daniba, inata kiranki again kikaki dagawa, wani irin abune wannan? Aise ki daga ki sanar dani kuna asibitine, kin dagamin hankali kin dagawa uwata hankali, ita kadai gareni a duniyarnan, har kinsama ta fasa Aikin hajjin ta tada balli, se tsiya takeyi, tana nema ma ta tsinemin, dole tasani siyan mata ticket, yanzu haka tana Jirgin dawowa nigeri...." Anty Rukayya bata karasa jin mezeceba wayar dake hannunta ta subuce ta fadi kasa kan tiles din dake dakin asibitin, anty Rukayya batamasan ta fadiba saboda tsabar tsantsan tsagwaron, firgici, hadi da d'imauta da zallarh tashin hankali. Raslan yabita da ido, dukda bejin me suke cewa Amma yanada tabbacin Tsananin tashin hankaline yasata wurgar da wayar tata kasa,..... *Maataaahhh!! Ina kuke! Ku marmatsofah!! akwai matsi na matse waje sa cikin gaban, mace, da saukar da zallar ni'ima, sannan akwai matsi na zallarh ni'ima Only, . Again Akwai tsumi me tsuma hnklin me gida, dakema uwar gida saurautar mata . Kede ki tuntubeni kisha magunguna na ban mamaki. 08136349646* KYAUTAR ALLAH... *PAID BOOK..500 NAIRA ONLY.. 08136349646..* SAADATU BINTU ABDULLAHI *ALLAH KA YAFEMU SABODA SHUGABA (S.A.W)*