← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 164

Sashe 139

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

hofinkiba...." Ya fada a hasale saboda maganar data gaya masa ta ya fara neman matane.. ta mugun bata masa rai. "Ni kake gayawa kishin bnza da hofi ..ashe sonka da nakeyi da kishinka da nakeyi duk na bnza ne a gareka..." Ta fada cikin kuka, me cike da soyayyarsa da kaunarsa. "Yeah! Look tashi ki fitarmin a side kinajina kou, tin bn karyakiba!!" Ya fada a mugun hasale kmr ze daketa. Ganin ya hasala sosai tasan yana iya karyata kamar yadda yace, tana kuka tana maimaita sonta garesa shine bnza da hofi, ta fice a falon... Rintse idanuwansa yayi a zuciyarsa yakeji be kyauta mataba ko ba komi ihsan na sonshi dukda bata da gurbi a zuciyarsa ko kadan Amma yana tausanta saboda yasan zafin so, da ace ihsan zata natsu da ko babu yawa ze iya mata gurbi a zuciyarsa saboda darajar son datake masa, duk iskncin ihsan yasan tana sonsa soma na haqiqa kawaide matsalolinta nada yawane, sam batada tarbiya shine babban abinda yafi bata masa game da ita. Miqewa yayi ya nufa toilet yayi alwala kana ya fice a gidan zuwa masallaci dan sallarh isha'i da asham, zuciyarsa cikeda tausanta ya isa masallacin. Suna yawan yin waya da Anty Rukayya Amma sam bata sanar da ita bata da lafia ba. Dukda kullum cikin rashin jin dadih take, Amma sam bata sha azumi ko dayaba, kullum seta dauka kuma seta kai da kyar, da aka fara sallarh tahajjud ma kullum seta tashi tayi, kuma ta kira RASLAN shima ya tashi yayi wata rana shike kiranta, ko ita ta kirashi, kullum de se sunyi sallarh tahajjud, sosai Aiki ya rikeshi a garin Abuja, dukda yana cikeda kewarta amma beso yazo saboda yasan muddin ze ganta baze ita haquriba, seya tabata hakan kuma barazanace ga azuminsa, ko yace ga azuminsu, dan haka yaketa daurewa, sede kullum suna maqale a phone da daddare. Ana saura 1week sallah ya turawa ihsan 2:million a account dinta na kayan Sallah, dukda tagani Amma sam bata kirashi ta masa godia ba, inda sabo RASLAN ya saba da halin ihsan. Ya bayar da sadaqa a masallatai da dama na temakon marayu da marasa karfi game da hidimar sallah sosai ya fitar da kudade a jikinsa yayi saboda ALLAH, Haka yayima duk ma'aikatansa ihsani kama daga tin farkon fara azumi har zuwa ynzu da ake gab da sallah...Yabi dangima ya musu sha tara ta arziki, masushi da marasa shi da abokanayen arziki,. Hatta iyayensa dasuke dashi yayi musu sunata sa masa albarka. Wata irin riga ya gani a online me kyau yama KYAUTAR ALLAH other dinta daga dubai sosai rigar ta hadu kimanin kudinta ya kai dubu dari hudu, dayake harkace ta kudi ba jimawa rigar ta iso garesa... Daman tini ya siya mata laces manya kala biyar ya bada an dinka mata, se atamfofi kala hudu suma, se shadda kala biyu, duk ya bada an dinkasu yau aka kawo masa su. Ya shiga shagon ummih ya zabo mata wadansu rigunan masu kyau, kaloli shida, da bags guda shida. Annah kuma kala goma ya mata atamfa kala biyar se shadda kala biyu, se lace kala uku, se takalma masu kyau kala biyar, da hijjabs kala biyar da mayafai kala shida da bags kala shida, KYAUTAR ALLAH kam takalma plat yase mata kala goma, se hijjabai suma kala goma, sam bese mata mayafiba saboda beso tana sawa, yase mata perfumes masu kyau, dukda yaga bata using dinsu sede humra take using Amma ya siya mata saboda sunyi masa, yase mata sarka da dankunne da zobuna da agogo da warwaro kala biyu na gold, se fashions kala biyar, Annah ma yase mata gold din kala biyu da fashions kala biyar. Ya siyama ihsan gold din itama kala uku, ya kawo mata ta amshe ko godia bb se aikin cika take tana batsewa, sam bebi ta kntaba saboda beda time dinta, gaf hnklinsa naga KYAUTAR ALLAH. Ana saura 6 days sallah ya nufa garin katsina ba tare daya sanar da itaba, babu abinda yake mafarki a kullum se ita, kullum tana mine dinsa, soyayyarta garesa kullum kara hauhawa takeyi dabadan ya kai zucia nesaba da sam baze iya wadannan uba uban kwanakin ba, be gantaba. Kasancewar 7:am suka taso daga abuja shida dreva da yusuf, basu samu damar isowaba se 2:3pm motarshi tayi packing a harabar gidan, fitowa yayi suka shiga gaisawa da ma'aikatan gidan, suma ya musu sha tara na arziki duk suka hau jero masa godia hadi da addu'ur'i babu iyaka. Yusuf da imran dreva dinsa suka fito da akwatuna manya guda uku, suka ajiye a kofar shiga falon. Godiya yayi musu kana yasa kai cikin falon bakinsa dauke da sallama... Annah ce zaune a falon tana kallon wa'azi a tashar sunnah tv, hannunta riqe da charbi, se lazimi takeyi. KYAUTAR ALLAH kuwa tana sama, kasancewar Tin jia aka basu hutun isilamiyya da boko na sallarh, dan hk yau wuni tayi bacci daman ta dena sakkowa kasan sam koda tana gida ne, dan kullum cikin bacci take kamar kasah, Annah de ta zubawa sarautar ALLAH ido dukda tana ankare da ita, sannan tana nan a kan bakarta na tana boye mata wani abune. Dagowa Annah tayi ta zuba masa ido hadi da amsa sallamar tasa, kallo daya ta maza taga ya rame. "Kune a garih..." Ta fada still idonta na kansa. Karasawa yayi ya zauna yace "haka de makiya baki sukace ..ina wuni kuna lafia ya azumi?" Annah ta amsa da"Alhamdulillahi...haka kazo kuma hannu rabbana atina hassanatin..." Ta karashe mgnr tana lalleka hannayensa. Murmushi RASLAN yayi wato Annah de bazata taba dena halintaba sema abinda ya karu. Kame baki yayi yace "Wane ni inzo hannu rabbana, ai da kin koreni.." Annah tace "Ahtouh wannan ai halin rowa ne kuma ni duk Zuri"arhta babu marowaci kaima sede ko in ka fara ne, zama da zainabu ai dole ka fara rowa..." RASLAN yayi murmushi yace "tou naji na fara din ne..." Annah ta yatsina fuska tace "Amma ko bakaji dadihba, da harna fara murnar ganinka ashede kwara murna ta koma ciki tinda ba komi ka kawoba se uban kamshin turare, kaman dan shuwa'arab, Gaskia bnji dadin zuwan kaba..." RASLAN yayi daria se rarraba ido yakeyi a falon tin dazu burinsa kawai ya ganta ko zeji dadih.... RASLAN bebi ta kntaba se maganganu take gasa masa wai marowacci ya gada rowa gun uwarsa. Karshede RASLAN miqewa yayi ya nufa kiching ya kira Jummai tazo ta taimaka masa suka shigo da akwatunan cikin falon, nan Annah ta fara washe 32. Kafin ace zoki duba ta matso ta fara bubbude kayan tana gani itada jummai, Annah ta rangada gud'a dukda duk yayanta da Abdullahi sunyi masu kayan sallah itada KYAUTAR ALLAH amma dukse taga basu mataba da RASLAN ya kawo mata wadannan se taga sunfi mata kyau nan ta shiga zunduma masa adduarh shida uwarsa da ubansa, RASLAN de daria yayi yace bayan ta gama zage masa uwa kuma zata dawo sa musu albarka... Annah tayi mirsisi, se kallon kaya takeyi, taga na KYAUTAR ALLAH yafi nata yawa, nanma seda tayi korafi wai meyasa RASLAN be siyo Mata irin rigar dayasewa KYAUTAR ALLAH a dubai ba, dan rigar ta mata kyau ainun. Ido Kawai RASLAN ya bita dashi hadi da daria duk hnklinsa bayama gareta yanaga KYAUTAR ALLAH dukse ya farajin zazzabi saboda be gantaba. Annah tasa jummai ta dauki akwatunan KYAUTAR ALLAH guda biyu ta nufa upstairs dasu. Ba haka RASLAN yasoba yaso Annah ta kirata nan ne tazo ta gani shi kuma ya gnta ko ze samu sassauci a ransa. Miqewa yayi zucia babu dadih ya nufa bedroom dinsa. Tashinta daga bacci kenan ta shiga wanka ta fito daure bathrobe, ta shirya cikin riga doguwa mara nauyi ta saka hijjabi dmn already tayi alwala, sallar azahar tayi domin batayiba saboda baccin data rinqayi, gashi ynzu ana neman uku. Tana idar da sallarh jummai ta shigo dakin da uban akwatuna ta ajiye a kasan dakin tana fadin, "zo...zo.. zo..kiga kayan Arziki KYAUTAR Annah..." Miqewa tayi daga daddumar ta cire hijjabin jikinta ta ajiyeshi a mazauninsa,, ta karaso tana fadin "Menene zan gani Anty jummai..." Jummai tace "hmmm kede bari, zoki ga kayan arziki..." KYAUTAR ALLAH ta karaso ta zauna gefen bed din jummai ta bude babban akwatin, ta shiga nuna mata kayayyakin dake ciki, ita knta taji son kayan a ranta, jummai na fara daga kayan ta jiyo kamshin jikinsa a jikin kayan, dan haka ko ba a fadaba tasan shine ya kawo kayan. "Kin gani kou...kai wannan kaya sunyi masha Allahu! Alhaji karamine ya kawo muku baki ga na Annah ba masha Allahu.." Cewar Jummai KYAUTAR ALLAH tace "ALLAH sarki, mungode ALLAH ya kara bud'i..." Jummai ta amsa da "Ameen de KYAUTAR Annah. ..." Seda ta gama zazzage mata kayan ta gani kana ta mayar dasu akwatunan tasa su a Waldrop. Kana ta fice a dakin danci gaba da ayyukan azumi. Tana fita KYAUTAR ALLAH ta koma ta kwanta kan bed din ta lalubo carbinta ta fara lazimi, wayarta taji tayi ringing dubawa tayi taga shine kin dagawa tayi, dan tasanshi data daga ze fara sakin layi, tayi typing message na godia da kayan daya siya musu ta tura masa ba jimawa ya mata replying. *Ki bar godiyarki zakiyimin ita anjima ...nide burina ki bani abun dadin nan.."* saurin rufe message din tayi ba tare data gama karantawa. kiranshi ya kara shigowa taki dagawa ya tura mata da message *wai meyasa bazata dagaba* ta tura masa da *Ba komi..."* ya mata replay data daga dan Allah, kin dagawa tayi karshema ta kashe wayar gaba daya, . daya kira yaji a kashe dole ya hakura. Da akasha ruwa dagashi se Annah sukasha ruwa a dining itakam bata saukoba, sede Jummai takai mata kayan fruit kawai dan a halin ynzu su kadai take iyasha, sam bata iyacin abinci tin rnr datayi aman nanma tace a dena kawo mata kosai da abincin ta sanar da jummai ba tareda sanin Annah ba dan tasan inta sani seta tsareta da tambayar meyasa ita kuma batasan daliliba kawaide taji ta tsane sune fruit kadai ke mata dadih a baki. Jummai ta kawo mata fruit din dai-dai ta idar da magrib ta taso ta amsa jiki na rawa ta zauna gefen bed ta farasha, Jummai de ta bita
Chapter 139 · 0% Book details