Sashe 156
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read
hannaah. "Zan fita ne.." Ya fada idonshi na kaina, dagowa nayi na kalleshi kana nace " ina zakaje?" Shafar sumar knsa yayi yace "ihsan ce babu lafia tana asibiti, zanje inga yaya jikinnata..." Ido na bishi dashi harya gama mgnr, seda ya idar na dauke kaina a knshi saboda ji nakeyi kamar in tashi in haushi da duka, kishinshi ya turnikemin zucia, dauke kaina nayi daga gareshi,, inajinshi yayima Anty Rukayya sallahma ya fice a falon, Dai-dai Annah ta fito daga bedroom dinta tazo ta dauki hannaah dake cinyata, na mike na bar falon na nufa bedroom din Annah saboda zuciata zafi takeyimin kmr zata fashe, kwancia nayi a kan bed a zuciata se ayyana abubuwa da dama nakeyi, gani nakeyi kmr inyaje zeyi sex da ita ne har ina ganin abun a idona wai yana cinta rinte idona nayi gam inajin kaina na azabar ciwo,..Anty Rukayya ta shigo dakin ta zauna a gefen bed din duk bansaniba, ta tabani, firgigit na bude idona a kanta, hannunta rige da Meead wadda keta bacci ta kwantar da ita akan bed din. Kana ta zuba min ido, tin tasowata ta kula da abinda ke damuna shiyasa ta gaza hkri ta biyoni. "Me kike tunani?" Anty Rukayya ta tambayeni, shiru nayi na wasu yan daqiqu kana nace mata "bakomi mommy.." "Ba gaskia bane.. Gayamin me kike tunani?" Na kara ce mata ba komi. "Ni nasan me kike tunani mijinki kou?" Na zuba mata ido taci gaba da magana "Kishin mijinki ke damunki kou?" Ta kara jefo min tambayar idanuwana suka shiga kokarin kawo ruwan hawaye na shanyesu kana nace " kinaji fa Anty Wai zeje gun matarshi..." Kawai na fashe da kuka. Ta shiga rarrashina danta kula ina cikin jerin mata masu bala'in kishi. "Kukan me kikeyi? Me kike nema a gun dana miji da baki samu ba a rayuwar aurenki dazaki zauna kina kuka a bnza a kan kishiya? Meye ba yayi miki, kullum a gigice yake saboda ke, shine zaki damu kanki a kan wata kishiya? Tin wuri ki kwantar da hnklinki inba hkba seki rame a bnza a hofi..." Shiru KYAUTAR ALLAH tayi tana sauraren kalaman Anty Rukayya, haka kawai taji zuciyarta tayi sanyi.... "Ki kwantar da hnklinki knji?" Anty Rukayya ta kara fada mata cikin tafshin murya KYAUTAR ALLAH tace "to mommy shikenan..." Tin kafin ya karaso maryam ta shiryawa ihsan tuggu iri iri saboda maryam tafi ihsan wayau ta wannan fannin, ita gam take rige da mijinta A hannu... Yusuf ne ya kawoshi asibitin seda suka tsaya a gun siyayya ya siyo mata kayan dubia masu dunbin yawa, kana suka iso asibitin... Yana shigowa dakin ta kara langwabewa yusuf ya gama shigo da kayayyakin dasuka siyo ya gaidata ko amsawa batayiba, daman be tsammaci hk daga garetaba ya juya ya fice a dakin. RASLAN ya karasa bakin bed din datake kwance se kara narkewa takeyi ya zauna haka kawai yaji tausanta ya ratsashi , yace mata ya jiki ta amsa da dasauki dakyar, irin ita a dole mejin jikinnan. RASLAN ya juya ga maryam suka gaisa ta tambayeta ya jiki ta amsa da dasauki,,, ya miqe kmr ana tsungulinsa da zumnar ya tafi ihsan ta riqoshi tace "ai dr yace yanason ganinka, pls karka tafi ka bari ya dawo ya fita ne, tin safe yake tambayarka..." RASLAN yace okay, ya koma ya zauna se shafarshi takeyi ita a dole ga karuwa,, shiko nan da nan jikinsa ya fara saki, ya mace ma gabaki daya....Da kissa da kisisina ihsan ta rikeshi a nan har tsakiyar dare ga bacci na idonshi karshede nan bed din datake kwance ya raba ya kwanta bacci ya kwasheshi, ihsan ta saki murmushin mugunta, ta koma ta kwanta da wayarshi a hannunta ta danna screen din taga picture dinsa ne shida KYAUTAR ALLAH da cuteness dinsu , dukda ita makiyiyace Amma tasan sunyi kyau sosai, kmr a sacesu, Ammafa kasan zuciarta ji takeyi kmr ta kashesu har lahira...dubawa tayi taga Maryam tini tayi bacci a kan gadon me jinya. Har dare KYAUTAR ALLAH taga be dawoba, se dubawa takeyi Amma ina har kowa yayi bacci ya batta tana jiran dawowarsa be dawoba, har 2:am, ta dauki waya ta kira lambarsa bugu daya biyu akasa mata busy ta kara kira, akasa mata busy, kira uku tayi anasa mata busy kuma duk aikin ihsan ne bakin ciki ya turniqe zuciar KYAUTAR ALLAH saboda ga zatonta RASLAN dinne kesa masa busy... ranar fa kwana tayi bata rintsaba kawai ta riga ta ayyanawa kanta yanacan yana making love da ihsan ne shiyasa yaketa sa mata busy hk ta kwana bata rintsaba zuciarta kmr zata fashe... 5:am ya farka daga baccin daya kwasheshi yana bude idonsa yaga a asibiti yake, shaf ya manta yasha a gida yake, tashi yy jiki na rawa ya dauki wayarsa ya fice a dakin, time din ihsan da maryam duk suna baccih. Seda ya tsaya yy sallah a masallacin asibitin kana yusuf ya jashi zuwa gida. Tana kwance a kan dadduma tana lazimi taji shigowar motarsa ta leka taga shine, ya nufo kofar falon ya hau bubbugawa tanaji tayi bnza dashi, se Anty Rukayya ce ta tashi daga kan daddumarta taje ta bude masa ya shigo direct dakin ya nufo, idanuwansa suka sauka a kan KYAUTAR ALLAH dake zaune bisa dadduma ga alqur'ani me girma a hannunta tana karantawa. Karasawa yayi gadon yaranshi duk ya duddubasu yaga se bacci sukeyi hnkli a kwance ya manna musu kiss tare da adduarh kana ya dawo ya gaida Annah dake zaune gefen bed da carfi a hannunta tana lazimi , Annah ta amsa a mutumce..suka gaisa da Anty Rukayya.. ya gaida KYAUTAR ALLAH taki amsawa kmr ma bata jishiba,.. "Amma de ba gidannan ka kwana ba Yau kou?" Annah ta jefo masa tambayar saboda ta saba ganinsa duk dare yana zuwa ya tofe yayanshi da adduah amma bezoba jia ta yadda akayi ta gane kenan. Sosa keya yayi yace "Eah wallahi.." KYAUTAR ALLAH na satar kallonshi. "Ina ka kwana?" Annah ta jefo masa tambayar. "Asibitih...inata jiran dr ne yace yana son ganina bnsanma bacci ya kwasheniba..." Annah ta bishi da ido ta tabe baki tace "Kawai kace ka hadu da makircin mace kawai tasaka kwana a asibiti..." Sosa keya RASLAN yy hadi da mikeqa ya fice a dakin ba tare daya ce komiba KYAUTAR ALLAH ta bishi da ido cikin bakin ciki da kunshinsa.... Coffee yasha yayi wanka ya koma ya kwanta bacci ya kwasheshi cike da bukatuwa da ita amma ynzu tinda yaga tayi tsarki se yasan yadda yayi ya dangana da gindinta... Ranar wuni tayi jikinta sakaka ko abinci kadan kadan takeci sabanin da, datake cin binci sosai, shiyasama ta fara narka uwar kiba seta danyi duhu saboda ruwan zafi da Annah ke dundumata dashi kullum 2times take mata wankan jego gashi wamkan towel. Washe garin ranar su ihsan suka koma abuja, zucia bb ddh, basu yada zango a ko ina ba se a gidan hadiza, ta kwashe komi na shagalin bikin ta sanar da ita, daman already hajiya hadiza ta gani a t.v , haihuwarma a bakin ihsan taji ba a bakin ummih ba, aiko ummih tasha wulaknci a gun Hadiza data dawo daga katsinar. Nande suka shiga shirya ta yadda za ayi ihsan ta haihu itama, suka hau kulle kulle iri daban-daban... Kwata-kwata KYAUTAR ALLAH ta daukema RASLAN kafa, ko gaisawar arziki basuyi in tana zaune a gu ya shigoma tashi takeyi ta bar masa gurin, duk yana ankare da ita da abin ya isheshi shine ya samu Anty Rukayya ya tambayeta ko yayima KYAUTAR ALLAH wani abune, anty rukayya ta jinjina kai tace "Bana tunanin hakan..." RASLAN yy jim kmr me shirin yin kuka kana yacr "to meyasa take yimin haka Anty? Ko bakiga abinda take min bane..gaskia akwai abinda de na mata dan Allah a bata hakuri ta yafemin bnsanma nayi ba, Amma de tayi hkri..." Anty Rukayya ta zuba masa ido yana mgnr kmr wani mara hnkli, har wata yar rama ya kara a kwanakin nan. "Ka tambayeta ne tace maka ka mata wani abu?" Cewar Anty Rukayya. RASLAN ya kara marairaicewa "Ta ina ma zata, tsaya in tambayeta Anty, danazo gufa seta gudu aide kina gani , kinga kuma se tayita hade rai, bazan iya mata magana ba tsoronta nakeji wallahi Anty ..." Karashen mgnr tasa se taso ta bawa Anty Rukayya daria da tausayima gabaki daya. "To shikenan zan mata magana..." Cewar Anty Rukayya RASLAN yace "Yaushe?" " Insha ALLAH yau.." Ta bashi amsa. Nan yashiga mata godia....Anty Rukayya ta samu KYAUTAR ALLAH ta mata tas tas shine tadan fara gaidashi amma da haushin abun a ranshi, aiko rnr data fara gaidashi kmr ze zuba ruwa a kasa yasha, dan farin ciki. RASLAN be bar siye siye ma jariransaba kullum cikin kashe musu kudi yake,, Tafiyar gaggawa ta kamashi zuwa abuja badan yasoba ya nufa abujar. Koda ya tafi kullum cikin waya suke ita dashi, da kuma yaranshi da yake cewa a basu wayar, seda yayita jin motsinsu ta wayar. koda yake abujar kullum hnklinsa na kan KYAUTAR ALLAH da cuteness dinsa. Wannan karon Ihsan se binsa takeyi a gindi a gindi dukda yana cikin tsakanin bukatuwa Amma sam be bi ta kantaba dan yafi tunanin akwai abinda ta kulla ne dukda kyautar Allah bata sanar dashi kiran data rinka masaba ana Rejecting, tade gaya masa dalilin fushinta dashi dan yaje ya kwana a asibiti ne gun ihsan. Zaune yake a kan kujerarsa a cikin office dinsa, se sanyin, a.c ke ratsashi tako ina, system din dake gabanshi ya zuba ma ido kawai, hannunshi na dafe da burarsa dake cikin wando tana a mike sambal, ta shigo office din cikin rangwada ba tare data nemi isoba kawai ta danno kai.zuba mata ido yayi tana sanye da riga da wando matsatstsu , sun amshi jikinta ainun hannunta rige da mini hand bag me shegen kyau, ta rufe kwayar idonta da tafkeken glashi irin wanda yaran zamani ke yayi. Karasowa tayi ta zauna tana facing dinsa ta wani saki shu'umin murmushi, "barkah da hutawah sarkih..." Tayi mgnr cikin shu'umanci. Dauke knsa yayi a knta yace "ubanwa ya baki izinin shigo min office direct..." Da sigar masifa yy mgnr. Murmushi tayi hadi da lumshe ido irin na manya manyan karuwai kana tace