← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 100

Sashe 99

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasir murmushi yayi yana sake shigewa jikin Nasrim tare suke cigaba da dariya basu zaci Hajja zata kunna wutan ba kawai sai ganin ɗakin sukayi ya kaure da haske salati tafara tana tafa hannu ta dungurar da yarinya a katifar ta fita da sauri zuwa falo
tsabar bacin rai batayi ma la akari da dare neba ta daukin wayan ta ƙira Mommy tare da fashewa da kuka
Mommy meƙewa tayi dafe da ƙirji taba Innalillashi Allahumma ajirni fimusifati
da sauri Daddy yace Dr lafiya".
Mommy tace "Daddy ban garen Hajja ba lafiya". tace tayi hanyar fita aɗakin da sauri a tunanin ta wani abune yasamu Nasrim ko jaririyar ta
Daddy yayi saurin riƙe mata hannu yana cewa pls dr bawani abin da yafaru ki nutsu yace suna ratsa compound din gidan harzuwa part din Hajja
zaune take a palo akan kujera tana faman jijjiga kafa da sauri Daddy yace "Hajja lafiya "? .
"ina ko lafiya Fanna na ƙira ta fita min da tantirin ɗanta anan ni ina taƙama nakawo yarinya kusa dani wai danna kubutar da yaran nan daga saɓo ashe shi hoto yake daukana kodayake ita tafishi fitina gasu can manne da suna jinin biƙi bai tafi ba mahaifa bata koma ba".
wani dogon numfashi daga mommy har Daddy sukaja Mammy ta shiga ɗakin shikuma Daddy ya tsaya bada hakuri ita kuma Mommy ta wuce ciki
suko NN sarai sun jita dama ba baccin suke ba dariya suke mata ganin ta fita yasa suka dauki ƴarsu suka koma kan gadon Hajjan a tunanin su ko Hajjan tayi fushi ta barmusu ɗakin ne gaba ɗaya kawai sai jin muryar Mommy sukayi akan su tace "haba haba my son karasa wajen shigowa sai ɗakin Hajja gashi yanzu duk ta tadamana hankali ita ka kirata zuwa part dinka mana kumama kwana nawa ne za a baka matar ka am srry kayi kakuri ka fita kaga tana can tanayiwa Daddyn ku faɗa".
ta ƙarashe maganan tareda karɓan NI'MRA hannun sa ta kwantar da ita tana ɗagosa tana wurga idon neman inda yacire kayan sa dan daga shi sai boxer hango jallabiyar sa tayi a gefin katifan dauko masa tayi tana meka masa "saka ko de ni zan saka maka ne Habibi".?
turo baki yayi alaman shagwaba
Mommy ta kalli Nasrim tace "ok Ammin Aiban karbi ki saka masa daure my son idan gari ya waye sai ta ɗan leƙaka a part dinka ni zance na sata aiki ne kaji sorry".

"MOMMY nide banaso yanzu ne fa nake bukatar ta bana iya bacci sai ina jin bugun numfashin ta shi yake zame min AC kwana biyu bana iya rinsawa idan banji ni a j........

sai kuma ya kasa ƙarasawa ya tsaya yana kalon yanda kirjin ta suke sheki alokacin data ɗaga hannun dan karɓan rigan da Mommyn take meƙa mata sai da tazo zata saka masa hannun hahu wanda shine na ƙarshe cikin kunnen sa ta raɗa masa
" daka ƙarasa mana yaushe kafara jin kunyar Mommyn ka ka dubi tsabar idon ta kace mata kai bazaka iya bacci ba sai kaji tudun boobs a cikin hannun ka".

shi kuma cikin ƙarfi yanda Mommy zataji yace ƙinaga bazan iya hakan bane".

dasauri ta yanke zancen da cewa Mommy na ƙarasa saka masa

Mommy ta kama hannun sa tace "muje."

suka fito daidai lokacin da Hajja take cewa ni ƙaton gardin nan zai shigowa a sirara Daddy de sai bada hakuri yake
har suka fice tade kasa yiwa Nasir da yake ta faman jifan ta da harara magana har suka fita kafin taje tabi ta kan Nasrim din data raina kuma

washe gari tun kafin a fito breakfast Izza ta shiga har cikin bedroom din Hajja ta samu Nasrim tana shirin fitowa aɗan kunyace tayi sallaman ta shigo zama tayi abakin katifan tana kallon yanda Nasy tayi kyau sosai cikin doguwar rigan wani kwancecen super holland mai zanen ja da yellow da baki ya zauna das ajikinta hannuta ta sake kaiwa bayan ta tana laluman zip din da dauri Izza ta tashi takai hannuta taja mata zip din ta cikin mirror suka hada ido Nasrim tace " thanks"
Izza tace "not thanks".
dan gajeren murmushi Nasrim ta sakar mata
Izza tace "dama ke mai kyau ce basai na bata bakina wajen cewa kinyi kyau ba kin sha jin sa awajen mutane da ace company wannan atumfar zasu san dake da sun daukeki ki musu tallah ".
juyowa Nasrim tayi tana shafa kumatun Izza
tace "haba my gangariya ai kin fini kyau kefa farace kalan maza kalan zamani"
Izza kama hannun Nasrim tayi zuka zauna bakin katifar sun kuyar da kanta tayi sai gashi yar hawaye shiru Nasrim tayi tana kallon ta saida ta dau lokaci tana wannan kukan can ta ɗago idon cikin na Nasrim tace "Dan Allah sister kiyi hakuri wllh bansan shi aka auramin ba kunyar ki ce tasa nake guje miki nake ƙin kulaki dan Allah ki yafemin".

girgiza mata kai Nasrim tayi tana cewa
"Ah Ah Izzatu hakance tazo a kaddaran mu nima gashi kunyar Ya Agrif ya hanani sakewa ko gaisheshi banyi ba".

hakade suka ci gaba da fira har lokacin breakfast din yayi suka fito yaude ba lefi Nasrim ta dan ware har suna fira da Agrif anan Agrif yake cewa shi idan ya tashi da Khaflan Da Abdul da lil Agrif zai tafi switzerland su kuma su tafi da matan Zeenat Muwadda Musatat Ummda

yau kwanan Nasrim ashirin da biyar da haifuwa tuni am mata kyaran jiki na mussamman wanda ahalin yanzu babu lolacin da zan muku bayanin sa

Idan kuna son jin cikekken tsumi na binnau wanda ake binne shi yayi wata shida ko ukku wanda akeyiwa amare masu jego da uwar gida first class ku tareni cikin littafina na *MAI GURI YAZO*

*ɗan daurin kai*

misalin ƙarfe shaɗaya na dare ya shigo Nasrim tana zaune tana shafa mai Hajja tana gasa marar yarinya zama yayi daf da Hajja har idan ta motsa jikinsu yana gugan na juna ya zubawa jaririyar ido yanda idan Hajja ta daura mata yatsan ta mai dumi take wani lumshe ido kamar Uwar ta taji ummmm
murmushi yayi ya ɗaga ido ya kalleta yayi sa'a itama shi take kallo da hannu ya yafito ta tasowa tayi daga ita sai sleeping dress din ta amma maidan kaurine saboda yanayin jikin jego
tsugun nawa tayi tana kallon sa nuna mata Baby Ni'mra yayi yace "kiga abinda Baby takeyi".
Nasrim tace "zafi ko ai dama nagaya mata ya isa takiji kai ka gaya mata tunda tana tsoron ka zataji yarinya kwanta ashirin da biyar amma ba adena gasa taba".
murmushi yayi yace "ba zafi takeji ma ki kalleta sosai idon ta yana kama da naki idan kikaji miss ko".?
fincike hannun ta tayi ta juya tana hawa kan katifar ta
Hajja da tunda Nasrim tace tana tsoron Nasir ta bude baki tana kallon ta har taje ta kwanta
cikin ɓacin rai tace "ni Maryama ni nake tsoron wani abu wai Nasuru Uban sa Abdulsamat ma banji tsoron sa ba balle wani yo ni badan maraicin sa nake dubawa ba ya isa wani abu awajena".

Nasrim tace "kina fakewa da maraici de amma waye ya isa acikin jiko kin ki ya ratsa main parlour ki ya rasa free palo ya haura sama yaratsa falon sama ya shigo miki har cikin bedroom yanzu ko Daddy yana shigowa nan ne ba iya kar su palon sama ba amma ki zauna kina bakewa da guzuma kina harbin karsana ina aka tabayin ƙaton mayara kamar wannan".

ta ƙarashe maganan tana jan barkon ta

dariyan mugunta Nasir yayi ai dama yana meman kofar da zai hadasu faɗa wanda zata korata Part din Mommy ko Ummu wanda komai zai zomasa cikin sauƙi
yace " ke Hajjar kike gayawa haka uwar Three A full ashe bakida kunya Hajja ta wllh yariyar nan badan jego takeba wllh yau ba me rabani da ita agabana take zagar min uwar uba ".
ya ƙarashe maganan tare da daure fuska kamar irin da gasken nan yaji haushi

"rabu da ita dena ɓata bakinka shalele na maganin ta kishiya aure zaka ƙara".
"Ah Ah Hajja koranta zakiyi a part dinki".

kallon
ka raina ni Hajja ta masa tace kai yaro nifa kakar bariki ce yo ni zaka gayawa zamani wannene ban gani ba nifa duk wani salallaben soyayya kar nake kallon ku yo nida nake karatun littatafan hausa tun tala taini damu aka fara yanzu ma sa idon Agrif ne yasa na dena karatun dan kasani nasan komai ni kakar bariki ce'.

Nasir kansa ya kwantar a ɗaya cinyar Hajja yace "to ai barikin ki banyi amfani ba gashi kin kasa bawa lovers jikan ki abinda yake so Hajjata nifa duk duniya ba nida kowa bayan Mommy na sai ke ina son ki musamman da kikayi kama da Abbana akullum fuskar Abbana nake kallo a naki ina son Allah yamiki tsowon rai sosai kakata".

shafa fuskar sa tayi tace "nasani Nasuru tun kana yaro nake ganin tsantsan na so a gareka nima ina son ka fiyeda yanda nake son raina jikana nasan kana son matar ka kuma tasamu cikeken tsarki ka dauki amarka gata can yarinya cede ni sai nayi kwana arba'in ina gasawa yarinya mara saboda yayi kwari kasanta ya saba da dubi shiyasa kikokina basa boranci shiyasa ka mannewa Halima kaga itama Humaira mijin yagama susucewa a kanta ga Kamal can agidan yari yana haukan shide ko zai rasa komai bayason rasa Humairah da ita yake son karasa rayuwar sa idan yafito

Bayan shekara ashirin da biyu tuni kamal ya fita an aura masa wata yaranya a dangin Mommy yarinyar uwar ta shuwa ce baban ta kanuri kaf three brother ba mai kyanta ta haifi ɗanta namiji an saka masa sunan MALA yayan Mommy

ahalin yanzu Nasrim yaranta bakwai wanda haifuwar ya tsaya mata tun shekaru takwas tana da yara biyar da Nasir bayan auren su NI'IMA sai hasan da susaini wanda ake kiransu FAYYAT KHALDUM
sai mai sunan SHARIF yayan Mmomy sai mai sunan Alhaji Hamza abokin Abban Nasir wanda suke ƙira da HAZEEK

Izza yaranta shida wanda da Agrif harda yan biyun da ummda yakama tana da yara tara cif
Chapter 99 · 0% Book details