← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 100

Sashe 51

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

murmushi yayi yace " ba munafiki bane akan aikin sa yake".
"Dr Hafsa tace'' shikenan yanzu yakake son ayi"?
"Mom baki ji police yace za atafi dake ba Ina neman hakkin na ne akan kazafi da kika min dan k'azafin kisan kai ba k'aramin cese bane".
Dr Hafsa tace'' Nasir kai ba mutum bane butulu azzalumin maci Amana ban taba ganin azzalumin irin kaba Dr Fanna kayiwa haka matar da har yanzu bata yarda kaine kake kulla mata duk wannan abun ba yanzu gashi ni da nake k'ok'arin akan naga tafidda ta nima kajefani cikin wani hali to wa zai tsayewa Fanna bata da kowa".
cikin sauri ya k'atse ta
"Ah Ah Ah Mom kika jefa kanki de Sharri na miki baki fada ba to Nasara baya yafiya kuma ba a sabawa umarnin sa."
ya k'arashe maganan zai ja kofar motan yarufe Amira da take cikin gida tafito da gudu tace'' haba Ya Nasir Mom cefa idan bakaji nauyin ta haifi irinka ba ai zakaji nauyin ya Ayman ko Ya Aliyu".
wani kallon kekuma awa Nasir ya mata
yace "ta shiga cese din kidan mune cese din gidan mu kuma hatta mommy ban ragawa ba balle ita cese din gidan mu family issue ne idan bare ya shiga bazai masa dad'i ba dan haka cikin ku duk Wanda yace zai shiga to zai gama rayuwar sa agidan prison
bayan haka Ina kuma Wornig din ku duk Wanda yayi gan gancin zuwa acikin ku da sunan zanyi belling din Dr Hafsa to shima zai gama rayuwar, sa a prison
Yana gama fadan haka yaja kofar yarufe direba yaja
Kuka Amira ta fashe dashi tana gani akayi cusa momn ta amota aka tafi

*Ummmm wannan rikicin na gidan manya ne Dr Hafsa kin kain ki sai Allah yafiddaki*

*Tofa masoya muje zuwa ko ya Izza da Humaira zasu kasance ko ya ya Nasrim take a* furzin
BATUL

*ban taba kuka acikin labarin na iran na yauba idon har dishi dishi yake dak'er nayi typing wllh pg yau yaman tausayi Sosai mommy tana cikin wani halin mutanen duniya akan dukiyar ba abinda bazasu iya ba wani lokacin kai talakan kafime kudin kwanciyar hankalin*

*BJ*
*08062383027*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
_rikicin babban gida_

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

*masoya Ina godiya sosai da comment din ku Allah yabar kauna* 🤝

17

*Prison*

"kai kai kai ke dan uban ki haka ake surfen marara kiga ko dusa bai faraba shine kika bari kika zauna dan uban ki bayin kine zasu miki surfen da za a dafa abincin abaki".
ta k'arashe maganan tana d'aga kulkin hannun ta zata dokawa Nasrim da sauri Nasrim ta mek'e
tace'' ma'am dan Allah kiyi hakuri wllh hannuna ciwo yakeyi tayi maganan tana nuna mata tafukan hannun ta da yaduru ruwa sabar rike Tab'arya ".
"ke ki fa kiyayeni baki sanni bako ina miki sassauci nefa akan ke bak'uwa ce amma naga ke zumace sai da wuto dan haka kiyi surfennan tas yafita gacan wankin barguna na mokofta na na nazo dashi kezaki wanke tsaf Nasrim sake zubewa tayi a gaban shrgegiyar matan da tasha stocking cikin uniform na ma'aikatan gidan prison "Dan Allah dan Allah ma'am bani da lafiya Wllh".
kallon ta matar tayi tace'' rashin lafiya kike ke ba rain ma gaba daya kika dauka ba dan Allah ya d'aura miki dan rashin lafiya zaki damu mutane ke ko ba kece Halima 3Afull ba wanda labarin ki yacike duniya oganniyar marassa Ima'ni ashe gado kikayi gashe can uwar ki ma taso kashe kakar ku uwar mijin ta
ta hanya saka mata poisonin acikin abinci wai dan bata goyi bayan ku ba kai ni da zuma naji a cikin a daidata a nacewa ma tsohuwar ta mutu kinga gada kikayi awajen uwarki kisa saboda kuna da kudi".
"Paison mommy Hajja ta mutu to ina mommy me aka mata ita kulleta akai .?
tana magana cikin sauri kamar zata janyo amsan abakin matar
tabe baki matar tayi tace'' ai an kulle shegiya ashe anguluce da kan zabo kullum ita kenan a gidajen radio rerere da baki tana tallata aikin al'kairin da takeyi kowa kaji Dr Fanna three brother kamar ita dayace me kudi a duniya ashe de wai kudin nata bata hanyan halak ta Tara ba haba ai dama wannan dukiya da ayar tambaya akansa shi kansa Abdulsamad din fa cikin dama cikin shekaru kadan yayi kudin da duk duniya aka Sansa dukiya kullu zakaji anyi kaza an gina ismiya agu kaza an ankaiwa marayun jaha kaza tallafin gashi daga k'arshe hau ai ya gama fadawa kan ki da uwar taki yanz..........
katse ta Nasrim tayi dacewa "Dan Allah yanzu ina mommy tana ina".
tana can cell mana tana ta kanta daga k'arshe nan za a kawota ku hade ku cigaba da girban abinda kuka shuka".
wani irin azabeben Kara Nasrim tasaka ta zube a wajen summemiya
asbitin cikin prison din aka kaita doctor din ita ma ma'aikaciyar gidan prison din ce
tace'' haba madam Timona nafa gaya miki yarinyar nan ki bita a sannu tana da k'aramin ciki sannan bata ma cikin nutsuwar ta gaba daya ni wllh duk da tana da lefi tausayin Haliman nan take bani badan komai ba sai yanda magan ganun ta ya baza duniya ko Ina ita kamar ita tafara kisa kowa da abinda yake fada bayan kisan nan ko yau anyishi amma dayake ba sanannu bane shiru kakeji kai shahara da kudi masifa ne Allah mun gode maka da kamar a haka".
Madam Timona tace'' ke Safiyya ni wllh baruwana dawani kudin ta ko cikin ta duk abinda sauran sukeyi itama shi zatayi uban ta ma ya yanke mata hukuncin balle mu kuma ya rubuta horo me tsanani ajiki da bai rubuta ba da bazamu saka taba".
ta k'arashe maganan tana ficewa
Chapter 51 · 0% Book details