← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 100

Sashe 8

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsaki Abba yayi yace "toh wai ya suke son wadannan mutane nayi ne nifa ba dan zasu ce ina takama da abinda Allah yaban ba dasai nace kowa yaji da kansa wllh duk abin daza ayi sai dai ayi bazan rage ba, musamman shinkafa da taliya da fulawa ni yanzu shikafa ma ba nawa bane madam ita keda iko".
Alhaji Nuhu yace" shikenan yallaɓai amma dan Allah ko a gurguje ne kazo dan idan kana nan zakafi yimusu gwarjini".
dole Abba yasa driver yakoma baya anyi meeting an tashi lafiya amma Abba bai samu fita daga Kano ba sai wajen 2 na rana.
Ajiyar zuciya ya sauke sanda yaji sun fita acikin gari yana jawo wayar sa na family ya kunna saƙon nin ne suka fara shigowa amma na Fanna ya fara ɓudewa
_barka da wannan lokacin hubby idan ka samu waje mai network ka kirani na kira ban sameka ba_
Murmushi yayi ya kirata jin yanayin muryar ta yace
"dama dan naji ya hanya nakira ka amma kun kusa ko?"
"A'a my wife ai yanzu muka bar kanon ma na halarci wani meeting ne wanda ke ma ya shafe ki Dr. Idan kina da ra ayin yin aikin kiyi da kanki bazan hanaki ba tunda ba irin na da bane, wannan kina da ƴancin da wanda kika ga dama in dai kina da ra'ayi idan kin haifu zaki fara fita kafin nan kibar komai a hannun Ahmed kamar yanda yake ayanzu yana da amana".
cikin sanyin murya tace "a'a a yanda hutu ya gama ratsani gaskiya ba zan iya wani aiki ba balle ma irin wannan aikin ya man nauyi".
dariya yayi yace "hakane gaskiyar ki madam kisha hutun ki mijin ki a wahale, ke a wahale ai ki huta rayuwar duniya dai baku da matsalan sa ko da za ace rabin al ummar Kano yara na ne da jikokina wllh kuda talauci *ruwa tasha* inji yara....
Mommy cikin sanyin murya ta dakatar dashi dacewa "Niko Abban Nasir wani lokacin kalaman ka suna bani mamaki, kamar ma kana mantawa da ƙaddarah ne ko FURRUCIN ka na ɗazu na cewa kai motar ka baza ta fadi ba kuma Koda ta faɗi da matakan kariya anya ba kuskure cikin FURRUCIN ka".

shiru can yace "ni ba wani kuskure cikin FURRUCI NA please my wife jikina yana bani kamar kina cikin damuwa please what's happening ? Please just let me know tell me what is going on".?
Numfasawa tayi tace". gaskiya ne ina cikin damuwa dan ji nake zuciyata ba daɗi".

"Ayyah Dr .dama yanzu ai kina matakin da zakiji kowane irin sauyi tunda kina tare da 3brother's kinga ko nida Abdulraham ba halin mu daya ba haka Abdulmajid ma halin sa da ban dole kiji ban banci a kulum".

murmushi tayi "tace kama bani 3 nima kenan?".
yace "haka nake fata kinga kin cike gurbin shekara 7 da mukayi ko?"
Murmushi tayi ta ce" abinda yafi bani tsoro Nasir ya gaya min wai ka nuna masa PIN ɗin laptop dinka yanda zai sararrafa ta sannan kanuna masa yanda zayyi amfani da agogon ka wajen gano me dukkan company ɗinka suke ciki bayan da ko bathroom zaka shiga baka cire agogon ka amma yanzu sai naga agogon ka a ƙatsan filo shine son yake cewa wai ka koya masa anya lafiya kuwa?"
"cikin sanyi yace lafiya ina son Nasiru yasan sirrina ne ta yanda koda bani bazaku sha wahala ba ke da shi".
cikin damuwa tace "ai kaji irin abin da yake sawa nake shiga damuwa yanzu Nasiru har ya kai wannan matakin bayan ga yan uwan ka su yakamata su sani Nasiru yarone bazai iya rik'e sirri ba"?.

Numfasawa yayi yace" ki daina damuwa Fatima na ba komai NASURUDDEEN kuma nasan halinsa duk da yaro ne yasan abinda yakeyi, Sam ƙwaƙwalwar sa bana yara bane zai iya riƙe sirri sosai,
yan uwa na kuma ɗan cikina ya fisu can-canta yasan sirri na tunda inada ɗa shi ne magaji na ba su ba."
cikin sanyin murga tace "Allah ya dawo dakai lafiya."
"Ameen yarabbi my dear kar ki damu I love you".
yace daga nan sukaci gaba da fira jikin su a sanyaye musamman Dr. Fanna dan wasu daga cikin furucin sa kamar yana bar mata wasiya
ne har sukayi sallama.
daga nan ya kashe wayar ma gabaɗaya yana cewa driver yasa masa wa'azin Dr. mansur sokoto suna cikin sauraron wa'azin ne
dai dai zasu shiga kwanar Dardum motar man fetur ne a gaban su, sai wata mota da take bayansu ta danno overtaken da shirin shiga tsakanin su da motar man amma wajen bai isa ba sanadin da yasa motan ta haɗe dana man kenan atake motan man fetur ɗin yaf ashe yana fashewa man yayi wani irin tashin wuta yafara bulbulowa wanda hatta motar Alhaji Abdulsamad da ya liƙe da jikin daya motan bai tsira ba cikin second 5 wuta yayi wani irin mamaye wajen wanda har motan bayan Abdulsamad ya kama
nan da nan motoci suka dinga ja da baya wani irin tashi wutan yake wanda ba wanda ya isa ya tunkare sa ahaka mutane suka ƙone, motocin nan guda 4 sukayi ƙurmus amma motan da bodyguard ɗin Alhaji Abdulsamad suke sun tsira kasan cewar wannan wanda ya hassada Accident shiga tsakanin su yayi, lokaci daya har direban bodyguard zai fara faɗa sai kuma abin ya afku ashe de ƙaran kwana ne cikin razana su Usman suke kiran Sir amma ba daman tunkaran wutan nan

Wayyo mommy ya zataji da wannan mummunar labarin ƙaddarah kenan Hajja abdulmajid, Abdulraham
*NASURUDDEEN*

*Ku biyoni a page3*
*B JATTKO*

[4/8, 1:46 PM] Batul Adam Jattako: *FURRUCI NA NE*

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURRUCI NA NE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*fatan alkairi gareki HAUWAU USMAN JIDDA jiddota Allah ya sa kaffara ce*

*Page3*

Bayan mutuwar wutan dak'er Jami an tsaro suka samu nasaran fito da kawawwakin su Alhaji Abdulsamad da aka gane wanne ne shi kasan cewar akwai escorts biyu a seat din baya Alhaji shine a tsak'iya sai direba da wani escort din agaba su 5 ne a motar

ba tare da bata lokaci basu Usman suka nemi abasu gawar wakin su tare da rakiyar yan sanda su ka kama hanyar Kano
jin jiniyar ambulances a cikin gidan ba k'aramin rikita mutanen gidan yayi ba a compound din hajja a ka kantar da gawar wakin
arikice Laure tashiga tana ihu
"hajja kifito kiga k'addaran data fado gidan nan yau".
Hajja da tun da taji jiniyar ta kasa mek'ewa bakin ta yana furta Abdulraham ne ko Abdulmajid ko Abdulsamad yau me idanuwa da kunnu wana zasu jiye min Allah kar kasa naga gawan daya daga cikin su nafison su subinne ni bazan iya daukan wannan k'addaran ba!!!!!
Laure waye kar kicemin ABDULsamadu nane
Mommy da taje tsaye ajikin window kamar an dasata komai ya tsaya mata kawai kallon gawar da aka ware gefe take amma tabbar na mijinta ne ta tana kallo Hajja dasu Mama suka fito suna kuka suna fisge fisge amma ita ko d'aga lebinta ta kasa wani irin jiri dushu take gani ita bata zube ba ita bata fadi ba kanta da gan-gan jikinta ta zura ta window zata fado ta saman benin da sauri Khadijan me aikin ta ta tareta tana kwallah wa asabe me aiki Kira tare suka kama mommy da ba tama suma janta sukayi suka kantar a k'asa suma suna cigaba da kukan cikin k'an kanin lokacin babban rashin Alhaji Abdulsamad ya mamaye Kano da duniya baki daya

a islamiyar su Nasir mlm Hasan ne yashigo yace "an arufe makaranta yau sai zuwa jibi insha Allah saka makon babban rashin da akayi na wanda ya bude makarantar wato Alhaji Abdulsamad a gobe za ayi Jana'izar da misalin 8 na safen gobe Allah yaji k'ansa halayensa na gari su.....
ai Kamal da Agrif basu gama jiba suka sa ihon kuka shiko Nasir shiru yayi yana tunani wai mutuwa da yaji anacewa idan anyi ta shikenan ba a dawowa Abban sa yayi wani irin zabura yayi waje yayi da gudu bodyguard din sa suka bishi amma basu kama shiba kasancewar bawani nisa tsakalin gidan da makarantar duk girman gidan amma yacika dan k'am dak'er yake gurtsawa yana faduwa yana tashi a lokacin har anzaga da kawar baya inda za a musu wanka falon Hajja ya nufa nan ma cike yake da
mata ana ta bawa Hajja hakuri sai mai maita Allahumma gafurni wal'hamni take Mama ce tafara hangoshi kuka tasa Hajja mata d'aga kai ta kalleshi tamek'o masa hannu da gudu ya k'arasa rungume sa tayi ta saki kuka "Muhammad Nasir shikenan ka tabbata MARAYAN da yarasa uwa da uba ya Allah ka rayamin wannan yaron shikenan shikenan Nasuru har abadan muda Abdulsamad".
"Hajja wai Abba na yamutu?
"Nasuru hakuri zamuyi "
cikin kukan da kamar ba d'an shekara bakwai ba yace
" dama sai da nacewa Abba kar yatafi". kowa kukan yake an rasa me lallashin wani
Hajja ta kalli Ummu tace"Amina ina Fanna".?
cikin kuka Ummu tace"anyi anyi bata farfado ba Dr Hafsa ta wuce da ita asbiti".
aiko Nasir yasa kukan shide akaishi wajen mommyn sa kar itama ta mutu
Allah sarki Abdulmajid yarasa inda zai sa ransa iya dauriya yayi amma yakasa saide Abu yafishi shiga damuwa dan shi acikin jirgi sai suma yake ana shafa masa ruwa dan suna Lagos sai 5 jirgin London din zai tashi wannan labarin ya riskeshi
Chapter 8 · 0% Book details