← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 100

Sashe 82

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali ya zame ya zube a gabanta
"yace Mommy so ne nayar da so masifa ne Mommy Son Nasrim shi yake sarrafa rayuwata Mommy tun tana ciki na sha gaya miki macce zaki haifa kuma ni zaki haifawa kuma idan kika haifeta ni zan fara daukan ta sai kawai na ganta a hannun Agrif mai makon naji haushin Agrif sai naji haushin Nasrim
Mommy a duk sanda nayi yunƙurin zan nuna ni nake son Nasrim sai AGRIF yayi min wani abin haushin da zanji sai kawai na huce akan Nasrim da farko Mommy wllh ƙuruciya ce daga baya kuma borin kunya ne ban gayawa kowa ina son Nasrim ba amma ina gayawa Allah nasha zuwa hajji da umara ina DAWAFI a ɗakin Allah dan na samu NaNa ta cikin sauƙi har aka saka ranan auren su da Agrif Mommy nasha yiwa Nasrim kyauta ba tare da sanin taba nasha turamata kalaman soyayya Mommy ki bani dama akwai abubuwan da zai gaskanta wannan abin da nake gaya miki Mommy ki yarda dani nasha bawa Nasirm kyauta cikin shikima ba tare da kowa ya gane ba dalilin yi mata rapping a tunanin na Agrif zai hakura da ita yabar ta ne sai kuma cikin yaran nan ya shiga Allah yagani ban soba amma na dauka na yarda nayi babban kuskure ki yanke min ko wane irin hukunci amma Mommy dan Allah ki janye kalmanki na bakya son sake ganina kar na sake dosan inda kike nasha wahala Mommy nasha ruwan da cikina ya kasa karɓan sa naci abincin da ban zaji zan cishi ba na kwanta a inda ban zaci ɗan adam yana ƙwanciya ba Mommy ki yafemin nayi kuskure ki hukunta ni zan zama bai biyayya da umarnin ki.

zama itama tayi damar a wajen ta ɗago haɓar sa murmushi tayi tace "to na baka umarnin ka kalleni....
da sauri ya ɗaga ya suba mata idanuwan sa da suka rune kalan ja tana masa murmushi shima murmushi yayi ga hawaye yana sauko masa saida yasha kalon ta yakamo hannun ta biyu
yace "Mommy dan Allah karki sake cewa na barki nasha wahala na azabtu kullum addua ta Allah ya kawo min wannan rana da zaki janye kalman na baƙya son gani na Mommy bani da komai bani da kowa sai ke Mommy dan Allah ki cigaba da daukana a Nasir din ki na da wanda kike so da kauna Mommy ba kwanciyar hankali da farin ciki a cikin rayuwata idan ba sanya idon ki da Albarkan ki Mommy a bin barin ciki da yasameni banyi farin ciki ba sabida banida uwar da zan runguma muyi farin cikin tare tasa kamin albarka Mommy ban san uwar da akace ita ta haifeni ba amma Mommy nasan Abbana nafi son ki akan Abbana Mommy daukar ki a matsayin uwa danayi ne yajamin nauyin bakin da narasa Nasrim ina son daukan ta tamkar wanda muka fito ciki daya amma so baya shawara baya kuma duba can canta ~SO~ hatsarine Mommy So mugune so baya adalci Mommy nayi nayi na daure masa saida ya a zabtar dani yarayu acikin jini na Mommy bansan tunani ba sai na NaNa ta bansan mafarki ba sai da ita mommy nayi kukuren rashin furtashi har na rasata a karo na farko Mommy ki bani NaNa na gyara kuskurena kar na rasa ta akaro na biyu bazan iya daukan da amatsayin ƙanwa kamar yanda nake yaudaran kaina ba a matsayin matar aure na nake son ta".

"ai ko karasa ta dan saura sati biyu auren Nasrim da Izza da Humaira".

arazane ya meƙe yace "Mommy tunda har nariga na furta bazan rasata akaro na biyu ba saide ayi duk rikicin da za ayi mommy wllh bazan yarda wani ya auri NASRIM ba Mommy ki tausaya min ni namiji ne ma buƙaci inason kasan cewa da macce sosai amma zuciyata Nana kaɗai take ƙayatamin sai Sadiyan Malam Ladan da nake ganin zan iya maneji da ita saboda ita ma tana da duk abinda nake so ajikin macce amma idan ban samu Nasrim ba itama bazan iya auren taba saboda nasan banida nusuwar da zan mata adalci nafison na fara auren Nasrim kafin Sadiya Mommy mata biyu nake sonyi mace daya bazata iya dauka na ba ".

taɓe baki Mommy tayi tace "Nasir ba kunya ba rufi to itama sadiyar ta Abbaty ce saide ka nemi wasu kai....
katse ta yayi da cewa
"ummm Mommy za ayi rigima kenan ki sa a ran ki Nasrim da Sadiya matane ne tunda ina dake bani da damuwa mommy na ta saba bani duk abinda nake so".

Mommy tace " duk abinda kake so wanda nake da iko akai ba amma wanda bani da iko saide hakuri kacire son auren Nasrim aran ka Nasir a bune da bazai taba yuwuwa ba Nasrim bata son ka bazata taba zaman aure da kai ba takawo wanda take so HABIB ɗan gidan shugaban ƙasa ".

wani irin dariya Nasir ya kece dashi yace "Mommy idan za ki iya temakona ki temakeni idan bazaki iya ba ki samin albarka wllh a wannan karan bazan bari ba na farko ma na barine saboda Agrif dan uwana ne amma yanzu zan bawa kowa mamaki ita kuma Nasrim kwana ukku kawai zaki bani bayan an daura aure sai ki tambayeta idan tace bata sona na miki alkawarin sakin ta ".

"Nasir ni kuma ban baka daman neman auren Nasrim ba saboda wasu dalilai amma ada tana budurwa nafi kowa son hakan yanzu ka makara Nasir idan kaje three brother kayi FURUCIN kana son Nasrim bazan yafi maka ba".

a wani irin tsorace yake binta da kallo a hankali ya meƙe tsaye yana dafa setin zuciyar sa "Mommy da gaske kike serious baki yafemin na auri Nasrim ba ".

gyada masa kai tayi
cikin wani irin amon rauni wanda bata dama tsammannin nasir a izzar sa yana dashima yace "Mommy koda hakan zai zama sanadinyar da ƙushewar rayuwata ne zaki rasani Mommy NASRIM ce farin ciki na".

"Nasir ka koyi samu da rashi kayi hankali ba komai mutum yake so zanyi ko yake samu ba idan ka rasa Nasrim bazaka rasa wata ba kabarwa Allah kaji".

karasa me ƙewar yayi yace "MOMMY na bari ne saboda umarnin ki ita ma Sadiya na barwa Abbaty ita zanjira naka abin da ALLAH zanyi dani".
ya ƙarashe maganan yana sake danƙe setin zuciyar sa kamar zai fisgoshi

*masoya mu hadu a pg 31 danjin yanda zata kaya shi burin Nasir na ya maida Nasrrim garkuwar tada sha'awar sa zai cika ita Nasrim zata yarda da auren sa*

*Batul Jattko*
[4/8, 1:49 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
( _rikicin babban gida_ )

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

*31*

Mommy ma meƙewar tayi ta reƙe hannun sa tace" ina zuwa".?

"Mommy gidana".
yayi maganan cikin shagwaɓan sa irin wanda ya sabayi mata
juyo dashi tayi suna fuskan tan juna tace Nasir bakayi missing dina ba in da dane sai mun kusa kwana muna fira duk da bamu taba jimawa bamu hadu ba kamar na wannan karan shekara guda bamuga juna ba ba waya".

"Mommy kafin ki tafi zan dawo inason na dan hutane".
girgiza masa kai tayi
tace"Nasir yanzu zamu tafi gida yanzu haka Aliyu ya gama duk wani shirin tafiyar mu a yau zamu tafi idan akwai abinda zaka dauka agidan naka ƙafata ƙafar ka muje ka dauka mu wuce airport".
"Mommy zan iya binku zuwa next week dan Allah ina da uzuri"?.
girgiza kai tayi
tace " Nasir tare dakai zan tafi inason ganin Mama Emaka kuma Baba ya kafe wai sai da kai zamu tafi inason neman gafaran Mama."

Mommy tana shiga falon gidan
Nasir tacikaro da hotunan su wani tabkeke na ita dashi ta zubawa ido ya dafa kafaɗan ta duk suna murmushi baza ta man taba ran birthday din Zeenat ne saina shida su Fayya ya rungumo Fayyat da Khaldum a gefe da gefen sa sai Khaflan da ya lanƙayo wuyan sa ta baya duk kansu dariya suke kamar ka ƙirasu su amsa ƙarasawa tayi wajen ta shafa fuskan Khaldum da Fayyat afilin tace "Allah yajikan ku".
tana ɗaga kanta taci karo da tafkeken pic din Mama Emaka da shiganta na Igbo tana tsaye a haraban coci farinta yananan sai de ta tsufa sosai
agefen nata na Hajjane ta hakince a tsaƙiyar Parlour ta cikin tum'tum sai wani hoton family har su abu da su Muwadda Izza da Humaira da Nasrim ne kawai babu a ciki sai Aiban da tana tunanin alokacin yarasu dan ga Aiban Ƙarami a ciyar Agrif
da sauri ta juya zata tambayeshi ina yasamu pic din Emaka taga ya haura sama zama tayi acikin kujera tana bin hotunan da kallo harda wanda sukayi da Baba Nasuru sunyi kyau dagani a india ne inda yake kai shi ganin doctor
ta shagala da kallon hofunan ya futo tana son tambayar sa in da ya samu hoton Mama Emaka da kuma yanda akayi ya musu hoto ba da sanin suba dan su adaukan su Nasir baya hoto amma taga yawani sha kunu ba wasa taɓe baki tayi ta meƙe
tace "muje Aliyu na jiran mu".

haka de Mommy ta sako Nasir agaba har nigeria nasir acikin girji ƙin kula Aliyu yayi nunawa ma yayi bai san dashi ba Mommy da Aliyu suna hada ido zasuyi murmushi suna mamakin fushin Nasir kamar bashi yayi lefiba daga ƙarshema fito da laptop din sa yayi yafara aiki Mommy ko jakar ta ta zuge ta dauko Qura'anin ta tafara karantawa
Chapter 82 · 0% Book details