← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 100

Sashe 28

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Itako Nasrim ko yatsan ta takasa d'agawa duk jikin ta yayi tsami kuka kam har tayi ta gaji tun tana sa ran ganin Agrif har tacire tsammani to me Agrif yake nufi da ita yamata irin wannan illar amma ba temako yafice yabarta haka
Zahra tace'' kuyi sauri ni wllh sonake naga idon Nasrim ko ya zata kalli idon mutane dariya Izza tayi tace'' yako zatayi kina gani tama kasa shigowa break
kasan cewar basu ka kowa a parlourn ba yasa kai tsaye suka haura steps direct bedroom din Nasrim din suka shiga amma ba alaman an sake shiga tun ranan da sukayi jere suka fito suka nufi na Agrif "Humairah tace'' what meye haka Nasrim da sauri ta haura bed din a dai-dai lokacin Nasrim tabude idon tare da fashewa da kuka me cin rai
Humairah tace'' Nasrim meye haka?
Nasrim cikin kuka tace'' Humairah ku d'agani na gaji da kwanciyar bayana ciwo duk jikina ciwo yake min".
ahankali suka d'agata tareda jinginar da ita cikin murya ta dayake fitowa d'aker tace" dan Allah kudu ba min meye a k'asana Zahra tayi saurin yaye blanket din da take rufe dashi da sauri ta sake tana fashewa da kuka Izza ma da Humairah da sauri ka bude ganin jini meyawa
" inna'lilashi wah inna'ilai'hi rajuun" suka fada a tare Humairah ta fashe da kuka Izza " tace " me ya Agrif yayi haka Nasrim kinga yanda jini ya bata ki da bed shit din kuwa".
Nasrim cikin dauriya da dashewar murya tace" Izza ku temakamin banyi sallah ba kuma fitsari nake ji".
ahankali izza da Zahra suka sa hannun su cikin kafadun ta biyu suna d'a gata tasa wani irin ihu ta zube suma kukan suka saka sake yun k'ura tayi cikin dauriya amma sai ta kasa takoma da gudu humairah ta fita
a inda tabar iyayen anan ta samesu cikin kuka tace'' Mama Nasrim ce Nasrim ce sai nuna kofar waje take atare suka mek'e dukkan su suna tambayar meyafaru ina take'?
" Mama bata da lafiya ko iya tashi batayi".
agigice Kamal yace " tana ina".?
"Part din su".
da sauri sukayi hanyar fita Mama Abu Hajja Aiban da Abbaty Kamal ne akan gaba
Mommy da daddy kawai aka bari suma de sun zauna ne saboda kara
girgiza kai Kamal yayi yafita a bedroom din yana cewa "Humairah ku kintsa ta ku daukota mota muje asbitin".
Hajja fada sosai takeyi dan da ita aka gasa Nasrim sai de Abu ya hana akaita hospital sai da mommy tazo tagani tace "ai justice dole sai ankai ta asbitin dan za amata dinki".
Kamal ne ya dauke ta suka tafi asbitin mommy da kanta tashiga theaterroom ta mata dinki mekyu ta tausayawa y'arta ta dan ba k'aramin ai ka ai ka aka mata ba afili ta shafi fuskan Nasrim da take bacci tace'' lalle namiji wazaiga Agrif yace shi zayyi wannan aika-akan'.
Wanda badan ta samu kulawa ba zai iya janyo mata matsalan yoyon fitsari
***************
kwana biyu aka sallameta suka dawo gida
Abu yace "Hajja dade kin bari ko a part din Aishan ta zauna kafin mijin nata yazo bai kamata a kaita batare da mijin yazo ba".
Hajja ta b'ata rai tace''
"Abdulrahaman kafa ficemin a ido kaine me ja da umarni na yanzu bawani bangaren Aishan da Nasrim zata zauna a tar katata can inda ta kai kanta aka mata yugu_yugu ko tajira an kai tane ba da kafan taje ba hakan ko akayi adole aka kai Nasrim part din ta aranan sai mommy tana warning din ta da takula da shan magun gunanta akan lokaci
Agrif kuma har yanzu wayan sa baya shiga ba a kuma samu labarin inda yake ba har yanzu
Humairah da Izza ne suka rakota
suna shiga Izza tace " ummmm dan Allah Hummee wannan parlourn k'amshin wa yakeyi".?
Humairah tace'' ai ni tun ranan da mukazo muka sami nasy akwance naji turaren Nasara amma ganin yanda nasy take yasa banyi magana ba ya Agrif ya canza turare baki ji ita kanta har yanzu tana k'amshin sa ba nina rasa wane irin turare yake amfani dashi".
ta k'arashe maganan tana d'aga hanci alaman tana son shak'an k'amshin
Nasrim tabe baki tayi tana zubewa a kujera

*bayan sati biyu*
amare suna murmurewa suyi kyau amma banda Nasrim ta rasa awane matsayi zata ajiye kanta tun tana fushi da Agrif bata neman sa kamar yanda bai ne meta ba amma yanzu ta dawo neman sa babban abin da yake bata mamaki bata samun sa awaya ashe bai jeda wayoyin sa ba jiya taji mommy tana fada wai laptop din sa da wayoyin sa suna bedroom dinsa na part dinta
suna tattaunawa akan Agrif ba aiki yaje ba
tana cikin wannan tunanin taji an dafa kafadun ta juyowa tayi taga Humairah ce murmushi tayi mata tareda kama hannu ta
mek'ewa tayi
Saida suka fita a parlourn Hajja din Humairah tace'' haba nasy duk kinsa my heart ya tada hankalin sa ko bacci bayayi yanzu ma cewa yayi na kiraki".
Ita de batayi magana ba binta kawai take a baya har zuwa part dinsu
a main parlour suka samu Kamal a zaune akan kujera one'siter kafan sa daya kan daya yana girgiza na saman dama zaman sa kenan Kamal kaman wani sarki haka yake ko yaushe
cikin sanyin murya tace " Yaya Kamal barka da hutawa".
tace tare da zama a kujeran two seater wanda yake facing din sa
kallon ta yayi na tsayon second 8
ya sauk'e numfashi tareda ajiye wayan hannun sa a hannu kujera yajuya ya kalli Humairah yace"
My one ki dan bamu waje ko zamuyi tsirri".
Humairah tace'' to abin hakane y'ar wariya ce".?

dariya yayi cikin son matar sa k'anwar sa yace "haba my wife dear ai kinsan ba abin da nake boye miki kawai dai naga ku ya kamata ku shawo kanta amma kun kasa shi yasa ni zan gwada amma ai kece k'arshe sirri my sweet love".
ya k'arashe maganan yana kashe mata ido daya cikin so mezafi Nasrim sun kuyar da kanta tayi hawaye yana shirin zubo mata gashi de Kamal da Humairah ba suyi wani dogon soyayya ba asali ma hadasu akayi amma gashi suna zaune cikin zazzafan soyayyar juna ita kuma Agrif yanuna mata so me zafi tun kafin suyi aure amma yanzu yasamu abin da yake so ya gudu ya barta tana cikin wannan tunanin taji tafin hannun sa cikin nata d'ago da kanta tayi tana kallon sa a tsugunne yake a kusa da ita yazuba mata manyan idon sa yana girgiza mata kai alaman kar ta bari hawayen ta yazubo amma ina yayi yawan da bazata iya maidashi ba sirtowa sukayi hannu biyu yasa ya shafe su cikin sannin murya yace" Kai cona mi Kamal y'ar uwata kwaya daya tak a duniya amma na barta take hawaye kuma a gabana kuma bani da matakin d'auka ban taba zatawa Agrif haka ba da bazan bari ya auri only one sisters dina ba amma nasan halin Agrif bazai tabayin hakan batare da wani hujjja ko dalili ba shiyasa nake neman alfarman ki gaya min akwai wani abu da ya faru tsakanin ku ne".?

girgiza kai tayi ta kasa magana
Humairah tace'' haba my dear wane lefi cikekkiyar amarya Wanda ta kawo cikekken budurci zatayiwa ango ai irin su nasy ko me sukayiwa ango dai_dai ne irin su ake Kira da amarya ba kya lefi".
d'agowa yayi yana kallon ta cikin murmushi yace " bana ce kibar nan ba".
natsaya ne because batun ya shafeni kasan nida my best sister bama moyewa juna komai".?

cikin kuka Nasrim tace "Yaya nima bani da wani wanda yafika Kai ne Dan uwa na wanda muke ciki daya dan Allah kasamo min inda mijina yake ina tsananin son ganin sa naji dalilin tafiyar sa nasan ya Agrif bazai tafi yabarni haka nen ba......
da k'er Kamal da Humairah suka samu nasaran lalashin ta har tayi shiru

****************
bayan wata 1
Nasrim kance take a bedroom din Agrif wanda ta maida shi nata yanzu juyi tayi ta tunanin tun fa last week ya kamata taga period dinta amma taji shiru gashi d'an d'anon bakin ta taji ya sauya ba abinda take so kamar kunun gyada alalan wanke
Knocking taji anayi
"Waye ."? tace
"Nice ranki shi dade."

taji muryar Barira me aikin Hajja
"shigo".
dan rissinawa tayi tace'' ranki shi dade ke ake Kira Breakfast."
shafa goshin ta tayi tare da mai da gashin ta da yarufe mata rabin fuskan ta tadan yamutsa fuska tace'' kai Aunty Barira bar breakfast din nan dan Allah idan ba damuwa ina son idan kika gama sallaman kowa ki dan had'amin min kunun madara".
"ba damuwa ranki shi dade yanzu zan hada miki na gama komai sai de hajiya babba tace lalle lalle kizo wajen break din sai na kai miki can ko"?.
tsaki tayi tace'' Hajja matsala".
Chapter 28 · 0% Book details