← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 100

Sashe 87

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nana ba ina nufin zina ba yanzu zansa adaura mana aure ne".

"ummm ga ƴar tsana Nasrim ko to tsaya kaji ko maza sun ƙare a duniya ba abinda zanyi dakai bazan soka ba kashi na kuma wllh yafi ƙarfin ka lashe wllh dan nafi kowa tsanan ka babban burina na ga ka wulaƙanta ƴan yahoor din sun kwashe kudin su ka koma ga bara akan titi ai kudinne kawai darajan ka badan suba bame kallon ka".

"NANA kina nufin baki tausayamin ba dakika ga ina gadi agidan mutane Allahn da ya hallicemu ma ya yana tausayawa wanda da yanada arziki daga baya yazo yarasa yafi tausayin sa akan wanda dama talakane".

"wannan kuma duk kai kasan su nide na sani zuciyata bazata taba rarda ta so koda mai irin halinka ba"
ta ƙarashe maganan tana takawa inda step din yake
numfashi ya sauke yace " ni na godewa Allah dayabani dama da ikon sauƙe nauyin da yake kaina na sauƙe dakon da nayi sama da shekaru dayawa ayau ban damu ko ki soni ba"

sai da yaga shigewart ya zauna akan kujera ruwan da yakani acikin goran mai sanyi ya dauka murfin ya fincika da ƙarfi ya saki ruwan a kansa yanajin yanda sanyin ruwan yake ratsa jikin sa sai da yaga ƙarewar ruwan yayi jifa da roban ya kwantar da kansa jikin kujera yana sauƙe numfashi can ya tashi yana taka step azafafe ya shige ɗakin sa bathroomr ya shigo ko kayan jikin sa bai tsaya cirewa ba ya fada kicin bathtub sai da yajima sosai cikin wannan halin ya cire kayan jikin sa ya cillar ya jawo shower ya dauraye jikin sa ya yafito ya jawo tawel ya dara a ƙugun sa ya fito ahaka ya faɗa gado yafara juyi sai da ya hada da magani kafin yadan samu ya nutsu
yayi shiru ya dinga tariyo abinda yafaru tsakanin sa da Nasrim wani uban asher ya maka yace "(ni me yake faruwa dani ni ) tashi yayi zaune da karfi yace "impossible me yasa na kasa control din kaina na dawane ido zan kalli wannan ƴar renin hankali na sayawa kaina raini awajen ta why why".

Nasrim tana shiga ta farajuyi akan gado tarasa wane fassara zatayiwa kanta najin tausayin Nasir da tafara ji tuno da yanayin da ta kansa yasa ta rintse idonta da ƙarfi tanajin wani abu tana mata yayo tabbas tasan ita macce mai kusan ci da sha'awa tun tana budurwa so tari azumi takeyi ita made kasa baccin tayi tana tuno kalaman da ta dinka jifan Nasir dasu tabbas tasan bata kyau taba koma meye ai yanzu mijin tane nisawa tayi afili tace uummm
to yanzu ko ya yake anya idan tace zata barshi a haka bata cikin fushin Allah kuwa to idan yaje ya sauƙe buƙatar sa awaje fa
jitayi gabanta ya faɗi sai kuma tayi tsaki tace sai yaje ai dama halinsane nide an hadani da jaraba kawai
tashi tayi ta shiga bayi dauro alwala amma tana dubawa taga wanka ya hau kanta tsaki tayi tacire kayan ta tayi wankan mai shaɗe da alwala tafito ta dinga rafka lafila da bata san adadin cikin rukku'u da sujjadan ta tana meman zabin Allah har akayi ƙiran sallah a masallacin jikin gidan da yake Nasir yasa an masa masallaci ya temakin musulmai ƴan angurawar kuwa dan dama suna da nisa sosai da masallaci ga idan ba irin su Nasir din da gommati take lallabawa ba wa ya isa yayi masallaci ajikon gidan sa kuma har yasa speaker a cikin americas
ta dauko Qur'ani ta fara karantawa sai saida taji an tada i'ƙama ta tashi tayi raka'atul fujjr tana idar da sallah ko shijabi bata tsaya cirewa bata faɗa gado batasan iya lokacin data dauka tana jan bacci ba

jin cikin ta yafara murdawa yasa ta tashi wani irin yunwa take ji idon ta ma wani dishi dishi take gani tsabar yunwa a hankali ta sauƙe kafarta ita tama banta da rigan baccine jikin ta adaddafe take tafiya Allah ya temakata tasamu dining da abinci kamar ma guntun da akaci aka rage ne

sosai taci abincin da batasan ɗanɗanon saba ta
batan da mutum a bayan taba sai jin waya yana ring tayi bata juyo ba dan ta san yana falon kawai yunwane ya hana ta gansa
wayan ya dauka yana cewa "ran Baba ya daɗe lefiya a su Hamza wlllh Baba basa karatu yanda yakamata shine na kai su makarantan kwana kuma na ƙwace wayoyin su yanzu sai ranan saturday zasu dinga kawo min ziyara sosai ma kuwa Eh Baba najira baka dauka ba ai jiyan wajen 5 na asuba ko Baba akan maganan sadiya ne 3 weeks yayi min yawa dan Allah ranan friday zan saka wata Aunty a maiduguri zata zo zata zo da ita gobe ko jibi kasa adaura auren kawai
shiru yayi can yace ok Allah ya ƙara rinma nagode BABA kashe wayan yayi dai dai lokacin da Nasrim ta saki wani uban tsaki zata tashi

cikin mugun ɓacin rai yasa ƙafar sa ya saƙalota sai gata yommm ta faɗa kansa

da sauri zata meƙe ya riƙota yace "dawa kike tsakin ".?

cikin kakkausar kurya yace "nace dawa kike".
da sauri ta dago tana kallon sa dan jin muryar asalin Nasir din sa nada dasauri ta dauke idon ta ganin yanda annurin faskan ya bata bat

cikin in ina tace "ba dakai nake ba".

"ok nazaci dani kike dan yanzu ina cikin hayyacina ba irin jiya ba danazo a buge kika zamu daman gaya min abin da ranki yake so ya karashe magana yana turata gefe

da sauri tayi hanyar sama yasaki murmushin cin nasara dan abin kunyane awajen ta dinga kallon sa da abin jiya gwara ta masa kallon ma shayi

Nasrim zama tayi tana tunani yanzu dama duk hakuri da sonta dayace yanayi ashe acikin maye yake lalle tabbas Nasri acikin hankalin sa bazai ce yana son ba bazai ba taba WANNAN FURUCIN BA tana cikin wannan taji ring din wayan ta jawo wayan ta kara akunne ba tare da ta duba waye ba
daga can bangaren Humarah tace "shejiya bacci ma kike mutumiyar yan kingama samun duniya wllh bako motsinki to yaya Bag brother ashe ke haka kikayi baban kamu.....
Nasrim tace "banason rainin hankali idan wanan gulman ne yasa kika kira to ki kashe dan banida kolacin sa".
"bashi bane an samu sabon labari ne kinsan wa izza ta aura kuwa kinga yanda izza ta koma cikin kwanki 3 dan Allah ki daure ki hau online ina no zan turamiki wai ta mayar da sunan ta A'I kin ga yanda take goki dan Allah ki hau kiga abin farin ciki da mamaki.............

*Sai mun hadu a pg 34 sis kumin afuwa daganan har ramadan inde posting yakama ranan saturday ko sunday to bazai kasance mai yawa ba saboda muna da biki har karshe wanan nan nagode insha Allah zamu lalaba mu karasa kafin ramadan*

bj
[4/8, 1:49 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

*_________________________________*

*34*

"dama ina ta tunanin ko yatake ciki ko wa aka aura mata tunda de tana cikin farin ciki Alhamdulillah am happy bari zan hau yanzu amma kinsan Izza mahaukaciya ce bata da Al'kibula ki tuna tana budurwa Ya Agrif yace yana sonta tayi ta farin ciki daga baya da yafiyi karatu Ya Aiban yace yana sonta shima ta amince to mai wannan ina taga kai zan hau naga ko waye".
dariya sosai Humaira tayi tace
"wllh ki duba WhatsApp hau ki ganta na tura miki gaskiya tana happy sosai
yanzu ke nafi ji badan kince ba ƙya son ji ba danace wani abu shawara kawai zan baki".
numfashi ta sauƙe tace "ina jinki".
yawwa my Nacyn mu kinsan de mafi ƙyan aiki aikin da akayi shi tare da shawara tamkar an haɗa ilimine da hankali a waje ɗaya Nasrim ina shawarar tarki da kiriƙe mijin ki abin da yamiki acikin ƙaddaran gidan mu gaba ɗaya yake kuma kaso 80 cikin ɗari ba lefin Ya Nasir tunda kika ga Iyayen mu da kansu sunyi amanna ku zauna tare wlllh da abinda suka hanngo muku na farko de saboda rufin asirin ƙaddaran Khaflan na biyu Ya Nasir yana mutuwar sonki soyayyar kine duk yajefashi.......
"dakata Hummy a ina ya taba cewa yana sona kinji abinda yadinga faɗa jiya harda durkusa min yana bani haƙuri har kasa har nafara tausaya masa kai saura kissi in bashi kaina ganin yanayin yanda yake ashe shi giya yasha a haukace yake kin ji magan ganu kamar gaske".
"Nasrim so tari mashayan giya fa idan suka bugu abinda yake can cikin zuciyar su suke faɗa amma naji abakin da bazayyi ƙarya ba yana sonki".

"yana son nawa zayyi maganan auran wata wai wannan yarinyar gidan Ladan ko wayake sabon familyn sade ita yake so nikuma duk abinda yamin na karban
vagnity abanza ".

"Ah ah Nacy kar kice haka shawaran da zan baki ki rungimi mijin idan kince zaki ja abin kece a ƙasa shi namiji naya da daman ƙara aure ya huce haushin sa akan wata so idan kika gyara kanki"..

"Humee kinaga ba aure zanyi kuma dan Allah na dace da zama matar mashayi ".?
Chapter 87 · 0% Book details