← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 100

Sashe 72

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daganan yacigaba da bata abinda Mamar tagaya musu wanda ba abari Nasrim tajiba harzuwa ƙarshe
shiru tayi tana kallon kowa har sunfara jin daɗi Nasrim ta dauki abin da sauki
sai kawai sukaga ta meƙe tana murmushi tace " kun yarda asiri ne ko toni ban yarda ba a video da
Habib yanuna min jiya akwai inda yace ƙaddarata ba mai ƙyau bane har yana warning din Agrig da yarabu dani duk wanda yaraɓeni to shima tasa ƙaddaran ba zatayi yau ba
gashi nan ya ɓata min rayuwa ta yaci zarafi na ya ɓata rayuwar yara na yanzu shikenan Zeenat da lil Agrif ma mutane ba zasu yanda yaran sunna bane suma duk sunbi rububun shegu tabbas yaci na saran ɓata min rayuwa da yayiwa kansa Alƙawari zayyi wannan *FURUCIN SANE*
ko Mama da kamal da suka kashemin miji da yara basu ci zarafina kamar shi ba ai su mutuwa sukayi shi kuma mutuwa yana kan kowa amma tabon haifan yaran shegu har mutuwa ta me nayi me nayi hakan ta faru akaina
a wani irin zabure tayi bakin kofa zata fita da sauri Abbaty ya kamota kokuwar fisgewa ta farayi tana cewa Adamu kabarni bade yana duniya ba wllh sai narama sai na samo shi duk inda yake nice ajarinsa sai na masa tabo mai muni arayuwa

Abu yace "kenan baki yarda da duk abinda na faɗa miki ba ko Halima
ina Nasrim taƙi lallasuwa daga ƙarshi ma suma tayi a hannun Daddy da Abbaty

sai da ta kwana washe gari ta bude ido ta ganta a gadon asbiti dafa kanta tayi tana wani irin sauƙe numfashi
"Mommy". tace cikin murya ta wanda daƙer yake fitowa
Daddy yace" my daughter sannu yanzu meyake damun ki ahankali ta kama hannun Daddy ta daura a ƙerjin ta
tace Daddy wani abune a ƙerjina kaciremin nauyi yake min sosai".
gigiza kai Daddy yayi yace "Halima kin daurawa kanki damuwa dayawa ne zuciyar ki yana barazanan kamuwa da ciwo ki daure mana ki samu sauƙi tanan zaki samu ƙarfin guwiwar Samun Nasir din kirama abinda yamiki amma idan kin daurawa kanki damuwa wani abun yasameki ai Nasir yaci bulus".
ahaka Daddy ya lalla ba Nasrim kamar yanda doctor yafaɗa har ta dinga sauƙe ajiyar zuciya
cikin muryan jin jiki sosai tace "Daddy idona idon BAYAHUDE wllh sai narama wannan *FURUCINA NE* " .

Daddy yace " Eh mana my daughter ai dole ki rama har nafara miki binciken inda yake".

Nasrim abin saida yazame mata kamar hauka hauka daƙer da adduar da lallashi tafara shiga haiyacin ta sai kuma takoma shiru shiru ko tasaka Khaflan agaba tayi ta kuka tana tsinewa Nasir yau ma kamar kullum khaflan yana zaune taje bakin gadon ta
zauna tace " my son zane kakeyi mugani home work ne".
azabure yajanye kayan sa yana turo baki yace " wai mamy banace ki dena kulani ba tunda kina zagin papa na shima kina son ki kashe sa kamar yanda kika kashe min brother na da Abba na yanzu gashi kullum ba ganin su sai Abdul ni wllh nafison Fayyat da Khaldum amma bazan ƙara ganin suba gashi papa ma bayanan kuma shima kina cewa sai kin kashe sa".
girgiza masa kai tayi tace "haba khaflan nifa mamyn kuce ban kashe maka brother din kaba kuma bazan ƙara FURUCUN ZAN KASHE WANI BA ni bance zan kashe papan kaba amma papan ka mugu ne shine kard......
da sauri ya katse ta da cewa "sai de kece muguwa NASRIM pa......
wani irin mari Nasrim ta eibi khaflan dashi tasake yin ball dashi ɗagoshi tayi ta sake zuba masa mari bakin sa hancinsa duk jini yake amma ko kusa ko alaman kuka yaron bayayi sai ma idon sa da yake jefawa cikin nata yana hura hanci itako dukan sa tashi ga yi kamar an aikota ya galabaita sosai amma ba alaman sayyi kuka Allah yatemaka mommy ta shigo

"SUBBAHALALLASHI Nasrim meye haka kashe sa zakiyi shime yasani meye lefin sa".

Mommy lefinsa shine yafiyo halin bayahude mommy ahaka shima wancen bayahuden ya ɓaci yanzu ya haɗamu da gurbataccen jinin sa".

Mommy bata sake tsayawa biyewa Nasrim ba ta ɗaga Khaflan tayi waje dashi dan bashi temakon gaggawa
Nasrim zubewa tayi awajen afili tace "sharri sharri yanzu har yanzu Khaflan yana daukana a wanda tayi kisan kai innalillashi Kamal Nasir Mama wayafi cutata ne ɗana yana zargina da na kashe masa ƴan uwa mutane suna gani na a mazinaciya duk ɓangaren binyun sun min illa ya zanyi Khaflan ya yarda ba lefina bane da wannan aƙidar zai girma zuciyar ɗana zai kinu da ƙiyayata fiye da yanda zuciya NASIR ya ginu akan nice sanadin mutuwar uwar da uban sa khaflan zai min tsanan da ko Nasir bai min shi ba KAMAL MAMA NASIR duk kun cuceni wa yafi cutana cikin ku kun ɓata min duniya ta ya rabbi ka dauki raina ".

Humaira da take shigowa tace " Kamal da uwar sa sunfi cutar dake rai yawuce gaban wasa duk wanda hassadar sa yakai har yakashe rai to yakai ƙololuwar rashin imani ko a wajen ALLAH".
cikin kuka tace
" haba Humairah shima ƙazafin zina bakin san har jikoki na ba."
Humaira tace "za adau matakin rufe bakin mutane inji Hajja".

Hajja ganin yanda NASRIM take cikin damuwa tace a shiya musu tafiya har na sati biyu zuwa island of greece duk wani abinda zai sata nishadi ana mata

*bayan sati ukku*

NASRIM ka tarame sosai tayi mugun yin duhu amma a matakan da aka dauka an ajiye masu gadin a ƙofar babban get duk wanda yace gun Nasrim yazo ta ba abarin sa yashigo macce ko namiji

ayau de tayi shirin fita aiki saboda akwai wani cese da wata sohuwa ta dage sai ta ganta koda ta saurari sohuwar cese din bai kai yakawo ba wai wata yarinya ce ta maƙalewa jikan ta kuma ana zargin mayune ta kwashe masa kuruwa yanace sai ita shine ta shigar da ƙara
Nasrim abin dariya yabata yanda sohuwar ta rikice kamar Hajja takeji shine dalilin fitan ta
har gida taje tasamu matar kuma ta shawo kan jikan nata da lallami da hikima irin nasu na lawyoyi yaron ya abince zai auri cousin dinsa kamar yanda kakar ta buƙata to Nasrim kawai matar nishadi take sakata har tafi Hajja rikicewa da fariyan ɗanta mai kuɗi ne bata magana biyu bata sako Alhaji Isya nawa komai Isya HAJJA TA SORO kenan

*NASIR*

da farko kaduna yaje yakama yawo yana kwana a masallaci har tsowon sati 5 yaude yasake dawowa kano

yawo yake acikin wani anguwa da ganin anguwar anguwar masu kuɗi ne sosai ake zafga rana da yagaji yazauna a ƙarƙashin wani bishiya kusa da wani mutum da yake kan binci yana bacci da alaman mai gadin gidan da suke jikin sane jinginuwa yayi ajikin bishiya kawai sai bacci ya kwaheshi
yana cikin bacci yaji ana tashin sa yana bude idon yaga wannan mutumin ne yace masa
"malam naga da ɗigon sallah agoshin ka kai musuline to lolacin sallah yayi aje ayi sai azo a ci ga ba da jiyar Alhajin ko".
Nasir binsa yayi yayi alwalla a fanfon masallaci bayan an idar da sallah atare suka fito da maigadin wannan gidan
suna zuwa aka fito da abincin mai gadi tayi mai gadin yayiwa Nasir har yace ba zaicima amma mai gadin yamatsa masa dole sukaci tare serious yaji dadin abincin yayi daidai da tes din bakin sa
bayan sun dawo daga sallan la'asar ne mai gadin yake cemasa

"yaro kasan Alhaji bazai zo yanzu ba dare ko da safe yagama rabon kuɗi idan yazo da daddaren ma baya tsayawa shigewa yake ciki dan haka sai da safe ake samun sa guarantee".

nisawa Nasir yayi yace Baba nifa ba maula nazo ba wucewa ma zanyi neman aiki nake ko na ƙarfi ne."
mutumin yace "ayya wllh ka kyauta ai ka ci da gumin ka yafi cida gumin wani
amma idan zaka iya da halin wata sohuwa me masifa da izza tana neman megadi dama tacemin batason baƙin mutum fari tas take so tana mugun son farin fata idan kayi hakuri da irin halinta zaka samu alkairi sosai ga ɗanta duk abinda take so shima yanaso".

Nasir sai da yayi murmushi yace ita kuma amma zanso na ganta zan iya da halita nima kakata haka take".

Maigadin yace "kai ba kamar HAJJA TA SORO ba Izza a cikin ta tsohuwar mai gadin gidan sarkice ALLAH ya ɗaga ɗanta yayi kuɗi kaga gidan da ya konkwatsa mata ita daya sai idan jikokin ta sunzo".
ya ƙarashe maganan yana nuna masa gidan da yakai gida alayin baye shi
yace" ka gani ko wani kallon ma sai kashiga ciki.

gaba yayi Nasir ya bishi abaya
gidan kam yaginu balefi tun daga compound suka kafara jin faɗan ta

har cikin parlon ta suka shiga tana zaune ta hakince akan kilishi kamar wata babbar ba sarakiya ta kishingiɗa da tumtum ana mata tausa Nasir sai dayayi murmushi tun kafin matar tayi magana dan ganin ta yayi kamar Hajja yanayi kishiɗiɗar ta

kirari mai gadi yafara mata yace " hutawan ki lafiya sogiji manyan mata uwa ga Alhaji Isyaku da Baban gida ".

mirmushi tayi tace " Malam Jafaru barni na huta yanzu na zuba ikona nima anmin a tsoro fa nagama rayuwata a Fada shikuma Amadu yakare a kariyar Dogarai duk su Isya a zaure mukayi cikin su yanzu nasamu duniya ai dole nayi mulki yanda nakeso kai wayyo Allah kajiƙan Amadu ina ma zai zo duniya yaga haifuwa ta mana rana".

Malam jafaru yace Allah yajinƙan su".

Ta tsoro sai leƙen Nasir da yake bayan Jafaru takeyi
tunkafin jafaru yayi magana tace " Malam Jafaru kai kuma a ina kasamo omer na tarkon kauna ai wannan omer ne.?

"Hajja waye kuma omer mai gadi da ki kace kina so nakawo miki kin san sa kenan?".
Chapter 72 · 0% Book details