← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 100

Sashe 43

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowar Mama da Aiban a hannun tana kuka ne ya k'ase su mek'ewa tsaye mommy da Nasrim sukayi Mama kwantar da Aiban tayi agaban su mommy tazube tana kuka "Dr Fanna shikenan Aiban ashe ciwon ciki bana tashi bane". Nasrim ma zubewa tayi tana d'aga hannun yaron tace'' mommy yamutu mommy Abdallah na ya tafi mommy waye ya aikata min haka meyake so awajena.......
Mama dafa Nasrim tayi tace'' Halima bar fad'an haka addua zaki masa Allah yasa macotane Allah da yabaki shi ya kwace muma duk zaman jiran sa muke ".
Nasrim fisgewa tayi tace'' Mama ba Allah bane baruwan Allah gub......
da sauri mommy ta rufe mata baki tana janta kan gado tace'' Nasrim kar na k'arajin kinyi magana ki barwa Allah".
"Cikin wani irin k"araji tace'' mommy bazan iya ba wllh d'ana d'ana Agrif ne yashigo a gigice yana " Ina Aiban din Ina yake Mama na shiga part din ki a na kukan mutuwar d'ana wllh bai mutu ba.........
Abu da daddy ne suka shigo sai Hajja da Ummu kowa yayi kukan rashin yaron dan yaro ne me fara'a da shiga rai irin de halin Agrif

**************************

*bayan sati 2*
Zainab de ansamu anshawo kan abin Al'hamdulillah da nisan shananta
ta warke amma har yanzu de ba tayi normal ba dan kullum ciwon ciki duk tarame abin tausayi tana part din mommy cikin kulawar ta sosai ko aiki ta dena zuwa in yakama taje office to tare suke zuwa tana kula da cita da Shanta sosai
**********************
" haba Halima Allah da yabamu Abdallah shi ya karbi abunsa kuma baga su Khafulan ba dan Allah kiyi aiki da taushidin ki shi k'addaran baya shawara da mutum idan zai zo
Ai kin ga misali ya Ummu taji da Aiban babba yarasu kinga tayi tawakkali".
"Abban Fayyat nasani inda rasuwa ta Allah yayi bazan damu ba amma gub........
shiru tayi tana tuno gargadin mommy nacewa duk kusan cinta da mutum kar ta gaya masa dan makusan tan sune abin zargin su duk da tasan da wuya Agrif ya cuar da ita bata zagin sa kwata-kwata sai de abin akwai daure kai to waye yake son ganin bayan su

"ki k'arasa mana kamar ya ba mutuwar Allah bane kawai wani da yake da ikon rayawa ko matarwa bayan Allah".?
"Ah Ah kawai Ina tunanin meye musabbabin jinyar Abdallah ne".
hannu ta ya jawo yana shafawa a hankalin yace' my dear kiyi Ima'ni k'aran kwana ne ajali ne Allah zai bamu wani ko....
shigowar message cikin wayan Agrif ne ya k'asar dashi wayan yana hannun kujera kusa da Nasrim a mamakin ce take kallon wayan tana kallon Agrif
cikin tuhuma
tace'' Izza!? .
hannun ta sa zata dauki waya yayi saurin dafewa cikin wani irin k'arfin da bata san tana dashi ba ta tun kud'a hannun nasa tana mek'ewa tsaye da wayan ahannun ta
taren da shiga cikin message din tana karantawa a fili

_kasan Allah ba wasa nake ba tun zuwan mu jiya ban sa komai abakina ba wllh abin da na jure a mijin baya yanzu kaina yawaye Ido na ya sake budewa bazan iya ba dole zaka waremin lokacin_
_gaskiya my heart sabo da kai na musamman ne a rai na kai d'aya ne a zuciya karik'e ka aje komai wuya na dau aniya_

Sai wanda da alaman

tun 23 minute ago ne
wanda shi yasake tunzura Nasrim inda tace

_da alaman muguwar ta hana ka d'auki wayan ko?_

da sauri Nasrim ta fice da wayan a hannun direct part Hajja cikin bugo kofa tayi Izza tana zaune kusa da Hajja tana b'are mata ayaba nata bata cikin wani irin zafi Nasrim ta cukumo Izza ta tsayar da ita tare da zuba mata zafafan Mari wani uban naushi ta Kai wa bakin Izza sai ga hakori nan atake ta canzawa Izza kamannu
Hajja komawa tayi gefe tana rusa kuka nata cewa Akira mata Abdulmajid ga yarsa zatayi kisan Kai so daya Hajja yayi yungurin shiga tsakanin su Nasrim ta tunkudata gefe nan take ta kama konkoso tana wayyo ta garya ni zata kashe y'ar mutane ku kiramin Abdulmajid ".
Daddy yana wajen aiki aiko daga Mama har Ummu da suka shigo kasa banbare Izza sukayi a hannu Nasrim gashi da k'er take sauke numfashi sai maza mutum hudu ne ma'aikatan gidan suka samo na saran kwatan Izza da tagama jigata kuka Baban Izza yasaka yana cewa "shikenan Hajiya ta kashe min Izza dama ita kenan dani".
sarkin gida ne yasa aka tarkata Izza zuwa asbiti

daddy da Abu zube suke agaban Hajja sai hakuri suke bata a kan tayi hakuri ta kafe dolle sai an daura auren Izza da Haruna in ba haka ba zata fita tabar gidan kuma sun rasa ta kenan har abada
Nasrim ta doka tsalle tace'' Wllh Wllh in ko akace za ayi haka saide cikin ukku a rasa daya koni ko Izza ko Harunan".
Daddy tashi yayi zai cakumo Nasrim tayi kofar fita da gudu sai da taje bakin kofar tace "aide rigiman duniya dame rai akeyi ko wllh muzuba dagowa wannan *FURRUCI NA NE* ba zan taba zama da kishiya ba".
tafice

Hajja tace'' to kaji ko Abdulmajid kaji de ko duk abinda ya samu Agrif ko Izza Nasrim ce ka sheda a matsayin kana alk'ali

Hajja tasa anyanke ranan auren Izza da Haruna wata daya
mommy ta numfasa tace'' amma Hajja da an yan ke auren da gaggawa yin auren ko da zuwa gobe ne dan asamu Nasrim ta hak'ura dan duk wannan abin da takeyi barazana ne idan taga anyi aure dolen ta zata hakuri".

Hajja tace'' sai de ta mutu amma Izzatu auren gata zan mata bazawaran da tayi shekara 5 ba miji zan yankewa aure kwanta daya a wannan zamanin da ciwon sanyi yayiwa mata yawa ai sai na gyare ta tsaf".
haka de aka tashi ran kowa ba dad'i
**********************
"Halima ki dauka wannan k'addaran mu ne k'addaran bata shawara da mutum da ban zabi hakan ba wllh Halima an biyo ta hanyar da aka fi karfina ne ba yanda zanyi ne Abu ya tilas tani kuma wllh k.........
"dagata Haruna bana son jin komai daga munafikin bakin ka kowa yayi abin da yaga zai iya".

"shikenan amma dan Halima kidena FURUCIN kisan Kai kiyi ta maimaita inna'lillahi'wa'ain'na'ilaishirajju kiyi abakota da Qu'ani kamar yanda kike da tabbas shedan yana son yayi galaba akanki ".
ajiyar zuciya ta sauke tana cije labe

ranan de kusan a zaune suka kwana daga ita har Agrif washe gari lokacin fitan sa aiki ma bayyi ba yafita acan yayi breakfast ma saboda masifar Nasrim gashi shima a mugun gajiye ya shigo cikin office din gakuma bacci da bayyi ba sai kawai ya kwanta yabar Kamal da aiki

Nasrim kam tadan bi hawaran Agrif dan kusan wuni tayi tana karatun Qur'an da yamma tana zaune tazuba uban takumi Humairah ta shigo rai a b'ace ta zauna Nasrim ta kalle ta tace'' Hummee yade.'?
Humairah iska ta fesar tace'' wani rainin hankali nagani a status din Izza da ya Agrif".
"Agrif kuma".
mek'a mata wayan Humairah tayi Nasrim hannu na rawa ta k'arba
na Izza ta fara budewa
inda tarubuta wasu kalman soyayya a saman picture din Agri kamar haka
_ina yawan kaunar ka a zuciya ba shakka komai wuya ko duka alk'awar naka na dauka_

Sai na Agrif da yasa wa saman hoton Izza kalma kamar haka

_ko rana da wata zasu dena haske gimbiya ta sai ke soyayyar ki har abada I love baby_

murmushi Nasrim tayi tana maidawa Humairah wayan tace'' tabbas rana dawata zasu dena hasken kamar yanda yafada wllh cikin mu sai wani yadena ganin gaske a yau ba gobe ba".
Humairah tace'' subbahanalla Nasrim wannan ba kalman musulmi mai cikekken imane bane".
dafa kafadan Humairah Nasrim tayi tace'' Aisha kenan ke kin sani a fannin kishi Imani na yana da mugun rauni komeye zan iya ai katawa a yanzu jina nake nida gawa daya ne ni Agrif zai tozar ta".
ta k'arashe maganan tana daukan wayan ta cikin sauri da samo hoton Izza dana Agrif ta hada ta kansale da Jan rubutu ❌ sannan ta rubuta *RI JF* ta daura a status din ta tayi murmushi ta haura sama Humairah tace'' dan Allah Nasrim kar kiyi abinda zaki janyo mana nadaman a family".
bata mata magana ba ta k'arasa hawa steps
da sauri Humairah ta fito taje tayi Ummu bayanin abinda ya faru Ummu murmushi tayi tace " bawani abinda zan iya yi amma anjima zanje na mata nasiha Nasrim akwai taurin kai".
Humairah tace'' gaskiya Ummu wllh ba amata adalcin ba bawara yaje waje yasamo ba da ya auri Izza data gama sanin sirrin ta wllh kishin yanzu ba irin daya bane danasu Mama da mommy kuma Ummu wllh seriously ba wani batun sai anjima ki tashi muje yanzu ki mata nasiha ni wllh in yakama ma araba auren ta hakura ta barwa Izza din in yaso Allah ya bata wani da wannan munanan FUFUCIN da takeyi".

mek'ewa Ummu tayi tace'' to tashi mu tafi

"haba Nasrim kamar ba me ilmi ba to meye kishin da zaki ta da hankalin ki kituna fa kece tamu ba wani gata da ni'iman da Allah bai miki ba dan ya jarrrabe ki da kishiya sai kiyi butulci".
"Ummu ki gane kishiyar fa na cin Amana ne nifa naga Izza da Baban ta da gawa agaba ruwan sama yana dukan su nasa daddy ya dauko su duk wani mataki da Izza ta taka da sa hannun na da temakona amma tarasa wanda zata ci amana sai ni".
Chapter 43 · 0% Book details