← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 100

Sashe 60

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy tamatsa kusa da Kamal sosai tace'' sorry my son amma de ba abin da yake damun ka ko".
"Eh mommy Ina lafiya".
"Ok dan Allah kayi hakuri Allah yakiyaye gaba
dama yanzu doctor din sa yakirani yake cemin wai gobe za afita dashi abin yaban mamaki dazu mukayi waya yace ba komai amma yanzu wai za afita dashi nace zan nemi me kai shi yace ah ah shi zai kula dashi jirgin asuba zasubi".
Mama tace'' mommy amma bai dace abawa doctor kawa yatafi da Shiba sai kace marar gata wacce k'asane za akai shi ma ".?
Mommy tace'' wllh ban sani ba".
Hajja tace'' to de Allah yabashi lafiya ya fada mana inda danginsa suke musan asalin Halima ita wancan k'edarar ta Lagos kuma yau she zakuje mata ai ni wannan abin kunyar har Ina ni Maryama ce da hada jini da k'edaraye Haruna ka hadani da aiki".
Ta k'arashe maganan tana ficewa tare ta toshe baki tana rufe hamman da takeyi

Daddy yace'' Dr Fanna muma a goben zamu wuce da Abdulrahaman JIDDA zamu tafi da Aisha da Abbaty yayi magana yanayin gaba Mama tace'' gaskiya alk'ali ba inda zani y'artawa tana cikin wannan hali ankusa zaman kotu na bari na tafi Ina ai bazai yuwu ba".
Daddy zuyowa yayi Yana kallon ta yace'' ba jimawa zamuyi ba bai fi 2 days ba zamu zo saboda cese din".
Mama da daddy suka fita ita ma
Humairah ta kama hannun Kamal tana cewa " kai me yakawo ka ai da kashe kan yayi da ya kashe banza za afake da mahaukaci dangin makasa kawai Allah sai ya isar mana jinin ya Haruna bazai tafi abanza ba sai an kashe Nasrim ko ajikin gol aka sassak'o ta".

Kamal yace"Humairah na gaya miki gaskiya zamu iya samun matsala idan kika cigaba da fadin wannan kalaman naki shifa Shari'a sabanin hankaline wai Nasrim da kikafi kowa sanin ta kike gayawa irin wannan Magan ganun".
Har suka fita mommy ta sauk'e ajiyar zuciya ta kama hannun Baba Nasuru ta kwantar da shi taja blanket ta rufesa ta tofa addua a kowacce kusurruwa na d'aki tafita Taja masa kofan
A parlou ta zauna tayi tagumi tana tuno irin matsin rayuwar da suke cikin duk tunanin da tayi yana tsayawa ne akan Nasir ya aikata duk wannan ta asan dan ya tsani Nasrim tunda har zai iya mata fyade ranan auren ta a daren tana farko kuma ya hana mijin sake kusan tar ta to meye ma bazai yi ba tunda dukiyar ta yake hari
girgiza kai tayi afili tace'' why why Muhammad Nasir me zakayi da abin duniya kaidin d'anane jinina d'aya nake daukar ka da Nasrim meyasa kayi kisan kai me nayi maka".
cikin kuka da yazame mata abinci da sha duk Wanda yasan mommy ada a yanzu idan yagan ta dole ya tausaya mata gaba daya a birkice take tama rasa meyake damun ta dafe k'irjin ta dayake mata matsanancin ciwo tayi tana fadin inna'lillahi

atare suka fito daga wankan nasa kayan tafara daukowa ta bashi yafara sawa ita kuma ta juya tana kallon cikin wodrop din da alaman akwai abinda take dubawa har yagama saka kayan ya k'arasa mirror Yana shafa Mai har ya gama yajuya yace "ai kin kasa zaban wanda zaki sane kome dare yayi bacci nakeji".
juyowa Humairah tayi tace'' kasan me my money wllh sleeping dress dina wanda ya Agrif ya kawo mana nida Izza da Nasrim a zuwan sa na k'arshe shi nake ta nema ban gani ba Wanda de Nasrim ta kashe su ajikin ta".
cikin basarwa Kamal yace'' ok kina da irin sa kenan kema ".
"wane irin tambaya ne wanna Kamal da akwai wani kaya da Nasrim take dashi ni banida shi naga idan kaine katashi sayo mana tare kake sayowa haka ya Agrif tun muna yara kata ba ganin an ban ban tamu da wani Abu ne? ".
"haka amma ai kaman sleeping dress in naga wanda yamin ai ina iya sayo miki musamman idan na kunya ne sosai ko".
Humairah tace'' Eh amma ina dashi nawan naraa shi".

kai my heart kisa wani mana dolene sai shi
ko kuma ya b'ata awayen wanki ne dan nima Ina neman wasu kayan Ina rasawa".
ajiyar zuciya Humairah ta sauk'e tace'' ah ah bana tunanin haka dan gaskiya ni ban taba sa shiba ma Kai ban fitar shi a ledan saba ma gaskiya balle yashiga kayan wanki
sannan akwai wani shijabi na marroon color wanda shima de irin me nikaf din wanda shima dashi Nasrim tayi kisan gaskiya ina son sa mommy ce takawo mana a saudia bana ganin sa shima kuma nasa sade amma ban ma sa acikin kayan wanki ba bazan manta randa na sakashi ba zamu Kai kayan sa rana na ya Abbaty na fara sa shi ina zuwa anan na rataya kuma kasan washe garin ranan Wednesday abin ya faru sai takalmin da yake k'afan Nasrim a video din da tayi kisan bazan manta ba Nasrim tayi kyauta da nata ko sakawa batayi ba tabawa Nabila ina na Izza kuma bak'i ne namu yellow to abin yana daure min kai".
Kamal k'an k'an ta Ido yayi yana kallon Humairah yace" to me hakan yake nufi kenan".?

Humairah ta sake jefa idon ta cikin nasa tace'' meko kawai de neman kayan nake daga shijab din har takalmin da rigan ban ganshi ba".
tsaki yaja yace "yanzu Humairah har kedin ce kike neman kayan da yayi kusan shekara kituna ko kin bawa wani de dan mutur su Agrif mafa wata shida kin manta ne dare yayi bacci nake ji idan kuma baki da niyar kwanciya sai da safe yayi magana yana hayewa kan bed din yaja wutan gefin sa ya kashe yaja blanket yana sake jan tsaki
gyad'a kai Hummee tayi ta dauki wani rigan bacci tasa ta haye gadon

Da asuba doctor yazo yatafi da Baba Nasuru shima daddy shida Abbaty suka tafi asbiti dan wucewa da Abu India

" Kamal kana nufin kayan sun bata kuma da jinin ajikin sa ya akayi hakan ta faru dama tun ranan ba nace kafita da kayan a gidan ba wannan abin fa ba karamin abu bane idan kayi wasa wllh zamu iya kwana ciki fa yanzu dama daga takalmin har rigan da shijab din da safan hannu da nabaka ka fita dasu aranan a cikin daki kaje ka ajiyesu inna'lillahi Kamal ka b'ata komai".
Kamal dafa kan sa yayi yana feso da iska me hucin zafi ta cikin bakin sa yace'' wllh Mama ban samu dama ba aranan kinsan yanda gidan nan ya hargitse shine naje na daga katifa nasaka a k'asan bed shine na manta gaba daya yanzu kuma na duba ban gan shiba".
Zama Mama tayi ta dafe kanta tace'' shikenan dama binciken da Humairah take yawan yi maka akan sane tasani Humairah tasan komai amatsayin ta na cikekkiyar lawyer wannan kayan kadai ya isa hujji awajenta Kamal yanzu ya za ayi gashi saura 6 days ayi zaman kotun ".
azabure ya tashi yace'' Mama yau Humairah zata mutu baza ta kwana da rai ba".
zai fita Mama ta kamo hannun sa
cikin tashin hankali tace'' Kamal kar kaje ka sake tafka kuskure bamu sani ba ko Humairah ta sanar wa wani kaga idan ka kasheta kamar ka kashe macijine ba ayanke kan ba dan haka yanzu abin yi dauke Humairah za musa ayi akaita wani gu abata azaba ta fadi wanda ta fad'awa sai musan abin yi amma bayan ta fad'a mana sai mukashe ta
ga mata dayawa agari kazabi zabin ranka ba wanan matar cushe ba".
shiru yayi ya gamsu da abin Mama tace'' masa
Mama tace'' Kamal har yanzu ka kasa gane inda Barira take ko wllh bamu kadai bane muke ai ki acikin gidan nan tunda kaga bamu muka saka abawa Hajja paison ba mahaukaciyar tsohuwar nan bata gabana yanzu abar ta tun da tana mana aiki ai ita take k'ara hura wutan Shari'a Nasrim kaga ai tana mana temako yanzu ga wannan shege doctor din Baban Nasuru yafita dashi kuma wai yaki fadan k'asan ma da zai kai
nifa yanzu abin duk ya dagole min".
Kamal zanyi magana yaji shigowar message cikin wayan sa
yana gani azabure ya mek'e tsaye yace'' what!!!!!!!!!?
A take wani irin gumi yafara karyo masa Karatun ma yakasa
Mama ce ta k'arba ta fara karantawa kamar haka
_slm ya abin kauna na dan Allah Ina neman izinin tafiya amatsayin ka na mijina amma fa ba zaka san inda zan jeba kasan duniya abin tsoro ne Ina gama sai ranan Wednesday zan zo da misalin 11 na safe mu hadu high court I love with all my heart by_

Mama tace'' shikenan Kamal komai ya tsaya asirin mu zai tonu".
" Ah ah Mama hakan bazai taba faruwa ba basu da wani hujjan daura mana ba agan mu Ido da Ido ba yanzu fa nabar Humairah a part din mu Ina zuwa".
Yayi magana yana shirin ficewa Mama tace'' ah ah Habubakar dawo bazaka samu Humairah ba mu samu mafita yanzu ni na yarda zan dauki duk wannan al'hakin kisan da sharrin a kaina kai karayu a hukunta ni".

"Ah ah Mama kwara mu gudu zan kwashe duk kudin mommy na account nata dana Nasir ya shihemu rayuwa zamu gudu k'asar maggep Ina da account ancan kuma da gida da takardan shedan zama a k'asar na har abadan idan muka je zamu shafa assets a fuskan mu kinga daga nan musa a canza mana fuska muyi zaman mu cikin kwanciyar hankalin shi kuma Abdul mu barwa daddy zai dinga tunowa dani".
Mama tace'' good hakan yayi ".
ka ahiya mana tafiyar kawai amma kasa duk company da yake waje akasuwa mu saida dan mu k'ara guzuri".
Chapter 60 · 0% Book details