← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 100

Sashe 16

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani dogon numfashi Agrif ya ja ya tsak'e cinkin cool voice din sa yace
" Halima ya zan yi da soyayyarki ne na rasa inda zan ajiye ki wllh Halima".
dariya tayi tace'' my heart can can ciki za ka kai ni kar ka bar a waje".
"Ai acikin kike".
gobe ina hanya kuma zan zo miki da albishir me ban mamaki me zaki shiya dan taran albishir dina".
"ko me kake so inde bai fi k'arfina ba zan maka kodan samun farin ciki ka bani da buri a duniya sai naga kana farin ciki".
"Ok thanks my love zan kira an jima kin ga tuk'i nake naji ina son jin muryar ki ga Nasara sai zab gamin harara yake by".
ya kashe wayan
wani irin suk'e fuska tayi tana fitar da numfashin b'acin rai Izza tace'' lafiya Nasy."?
kwafa tayi tana tada motar tace " Yaya Agrif ne mana muna firan mu me dadi ya kama min sunan wannan bayahuden bayan ya san bana son jin ko da sunansa ne wllh inde nasamu nasaran auren Ya Agrif zan raba shi da wannan bayahuden in sha Allah".
Zahra tace'' kin isa ma kinfa san shak'uwarsu".
Nasrim ta ce'' to ko sai de in bani ce matarsa ba in kinga ban raba su ba ban auri ya Agrif ba".
Humairah tace " me ko zai hana ki auran sa wannan soyayyar taku".
sake kashe motar tayi tana sauk'e ajiyar zuciya tace'' kunsan me har yanzu fa ya Agrif bai taba furtamin maganan aure ba sai de yace idan na gama secondary zai gaya min wata magana dana gama na nemi ya gayamin yace sai yazo yanzu de sai yazo din GOBE DA LABARI kunnuwa na zasu jiye min abin da na jima ina son ji".
Zahra ta ce'' in sha Allah za ki ji nima ba ga ya Ayman ba ya gama nuk'u-nuk'unsa ya fito kema zaki ji".
Nasrim tasa iho woow gobe akwai party dinner na musamman a 3'brother family'
ta kalli Humairah tace'' kema Humee wakika tsayar ya kamata a goben duk mufito da mazaje ita ko Izza sai ruwan ido ka mazan nan birjik a kanta".
Humairah dan ta bawa Nasrim haushi tace'' ai ni sai babban gora NASARA KO GANI GAFI MUTUM NASARA ME WUYAR FADANCI nake so".
"dariya Nasrim tayi tace'' in ma dan naji haushi kike yiwa kanki mummunar fata wllh ba ruwana idan kika fada abakin ma'lakiku".

Zarha ma dariya tayi tace'' kai wai mummunar fata auren Nasara ai sai me sa'ar gaske narasa me yasa k'iyayyar sa ba ta raguwa a zuciyar ki Nasrim bayan shi yanzu baya ma nuna yasan ki dama de inaga k'uruciya ce fa yanzu kuma kunyar abin da yayi na dane yasa yake miki haka kin kasa gane halinsa ko mu da muke gai dashi ba sai ya ga dama yake cewa Weldon shikenan bakin amsa gaisuwar kenan".
Humairah tace
"Ai ita tana jin maganan Inna Harira ne ni fa wllh ban yarda da abinda take fada ba, wai shi ya karya miki yatsa ai so nake wata rana ta zauna tana gilla miki k'aryar mommy ko shi Nasara yaji naga bakin gilla k'arya".
Zahra tace'' wllh kuwa inda da gaske ne me yasa ba mu taba ji su Mama suna fada ba ko Hajja a yawan surutunta za muji tayi koda subutar baki ne ta fada dama fa masu aiki munafukai ne duk da Nasara me bak'in haline banajin zayyi haka".?
Nasrim tace'' ita Hajja sona take da za muji a bakin ta su Ummu kuma kin san ba fad'a za suyi ba ni na yarda da abin da inna Harira take fada tun daga ranan da aka haifeni suke boyeni saboda baya son gani na har yabar k'asan uwar da ta haife ni dalilin sa ta watsar da ni yanzu waye zai ce mommy ni ta Haifa ba shi ba wllh bani da abin k'i sama da shi, kuma sai munyi shari'a agaban Allah da zaku ce k'arya ne duk da bawani cikekken sani nayi wa fuskans aba nasan cike take da k'ina Agrif fa ko waya baya iyayi dani a gabansa.
Humairah ta ce
"To Allah de ya kyauta mu de muna fatan Allah Ya kawo k'arshe abin".
Nasrim ta ce
'' ba Ameen ba wllh kamar yanda ban san farkon k'iyayyar ba bana son naga k'arshenta ni da shi har abadan"
Daga nan ba su ƙara cewa komai ba ta yi wa motar key suka ka wuce gida.

*******

Daga shi sai wani dan guntun boxer yana kwance a bakin ruwan swimming pool a kan wani dan gadon k'afe wasu siraran kyawawan yan matan India ne suke masa tausa idonsa akan Agrif da ya kama dimaucewa a kan rubuta kalaman soyayya jikin wasu flour murmushinsa wanda ba ya sakin sa sai yatuno da mugunta ya yi, sannan ya yi wa 'yan'matan alama da su ba sa waje
mik'ewa y ayi zaune ya sa hannu ya janye floor din da Agrif ya dafe a k'irji Agrif buɗe lumsassun idonsa yayi a kansa ya ce
"Why"?
Murmushi yayi yace "wai bro me kake shirin yi ne".?
Shi ma murmushi yayi yana mek'a hannun alaman ya bashi abinsa amma Nasara ya hana sai Agrif ya ce
"Abin da nake shirin yi ko na gaya maka ba ganewa za kayi ba tunda baka san sa ba. Ina shirya kallaman da zan gaya wa Nasrim ne na burgeta na kuma saurin dilmiyar da zuciyarta ka san Nasrim ba jigari-jigarin macce ba ce".

A hankali Nasara ya sakar masa fulawar ya koma ya kwata dariya Agrif ya yi ya ce
"Ai dama nace ba za ka gane ba, da dai harkan business ne dai kum...."
Sauran maganan ya tsayewa Agrif ganin wani irin hawaye da yake bullulawa a idon Nasir wanda tun suna yara bai taba gani hawayensa ba sai a mutuwar Abba, akwai ranan da ya karye a ball amma murmushi ma ya yi a maimakon kuka. Da ya ga Agrif yana masa kuka da sauri ya k'arasa inda yake ya kama hannunsa cikin firgici yake tambayar sa me ya faru, cikin wani irin sheshek'ar kuka Nasir ya fara bayani
"Haruna ban san yanda za ka d'auki al'amarina ba amma al'amarin yana da girma da rikitarwa Agrif a ranan wanka an ce ba a ɓoye cibi, wllh na fika son Halima tun kafin ta zo duniya dan Allah dan'uwa ka min alfarman bar min ita".
wani irin zabura Agrif yayi ya mek'e tsaye
"What! wllh NASURUDDEEN k'arya kake ba sonta kake ba ka sha fada ka tsane ta mai sonta ma ba ka so, ka sha bani shawaran na rabu da ita wllh Salo kawai kake son canzawa wani manufa kake da shi a kanta ba So ba.....

Shi ma mik'ewar ya yi yace "Agrif tunda nake da kai na taba maka k'arya".?
Agrif ya ce
"A a amma na san yanda k'iyayyar Nasrim ya ginu a cikin jininka za ka iyayin komai dan ka cutar da ita".

Nasir cikin laushin murya ya ce
"Shi ke nan dama na san ba wanda zai yarda da ni sai kai, dan kafi kowa sani na ka san ni bana furta abin da ba zanyi ba amma tunda kai ba ka yardani ba abar zancen ma na san ko mommy ta sani amma ka sani wllh bazan rayuba in ban aure ta ba, amma na bar maka inde ba za ka iya sadaukar min ita ba gobe tare za mu tafi kamin alfarman neman gafaranta na cutar da ita shiyasa Allah ya jarrabeni da sonta".?
haka de yayi ta yiwa Agrif kalamai kamar gaske har ya yarda zai sadaukar masa da soyayyar ta amma da sharadi
da sauri yace "meye sharadi wllh ko na mutum ne zanyi".
Agrif yace" Nasrim tana mugun k'in ka dan haka idan har ka shawo kanto na bar maka ita har abadan idan kuma kuma ta k'i to ba dole".
Murmushi Nasara yayi yace thanks brother amma kafin nan sai kamin wata alfarman wanda shi ne na k'ashe so nake acikin yaran gidan kace kana son wata ka ga zata ji zafi ta ce ka ci amanar ta daga nan ni zan fara kafa nawa fadan aguntq."
Agrif yace " ai gidan mu babu wasu y'an mata sai Zahra da Izza ita Zahra ta Ayman ce sai wannan Izza ni kuma gaskiya bana ra'ayin ta farinta bai min ba kamar zafiyan nake ganin ta".

Nasir yace " yawwa ita zaka so zaure kazo Nasrim zata fi jin haushi ta yi saurin karb'an ta yi na dan tarama abin da kayi mata ka auri aminiyarta ka ga ita ma za ga ce zata rama ta aure ni".

Agrif yace "okay zanyi tunani akai".
ya d'auki tar kacen sa yayi gaba

wani irin murmushi irin Nasir yayi yana binsa da kallo sai kuma ya murtuke fuska afili yace ni Nasuru na AURI wannan yarinya kamar yanda bana son ta bana son wani nawa ya rab'e ta zan baka mamaki Agrif yarinyar nan sai ta zama abin kwatance a duniya ta yanda ko kare ba zai shinshina ta ba balle mutum sai na tarwatsa rayuwar ta tunda na rasa ubana a kanta. Ya yi murmushi yana tuno kukan da yayi a fili ya sake cewa ashe zan iya shirin Film
to Allah ya kyauta Nasuru

Kano

"Izzatu kin sani a gaba sai kuka kike me yake faruwa kukan ki yana ta damin hankali".

Cikin kuka tace'' Baba nika bar ni a cikin dibin masoyana na fitar da wani a waje kai ka kafe sai yan cikin gidan nan Wllh bani a gabansu ba samarin ba har y'an mata Humairah Kamal yana son ita ma Zahra nan y'ar karere Ayman dan gidan Dr hafsa k'awar mommy yake son ta NASRIM Agrif ne yake sonta ni kenan ba Wanda zai soni na gaya maka kabarni na zaba a cikin masu sona idan kudi ne ai Khaleed ko Shamsu duk masu kudi ne dama fa tun ina yarinya Hajja ta ce ita ajikokin ta bawanda zai aure ni tsintacciyar magi ce Agrif ya zaunar da yan uwan sa ba bu irin wulak'ancin da basu min ba bazan manta wannan ba ni na hak'ura
Chapter 16 · 0% Book details