← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 100

Sashe 35

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

itane Nasrim ta kanta take yanzu Kamal ne yakama hannun ta tamek'e tsaye ahankali take tagawa Kamal yana rike da hannun ta
cikin wahalallen murya tace'' "Allah Yaya bazan iya ba marata".
tace tare da rek'e Kamal kam mommy ce tafara tasowa
duk suka taso suna mata sannu mommy tace'' Mama mukamata ko wannan bedroom din mushiga da ita
Safan hannu ta zaro acikin jakar ta suka kama ta suka shiga da ita bedroom din Hajja na k'asa mommy tana dubawa jikin ta yafara rawa cikin in nina a tsorace ta d'ago tace'' Aisha mutafi asbiti".
Mama tace'' Dr Fanna lafiya".
Aisha hannu da k'afane yake shirin fitowa dole sai munje can na haska idan yakama dole ayi cs ne saide na mata".
Kwantar da ita akayi acikin motan mommy tana bata temako haka suka k'arasa hospital din suna sauk'a wayan mommy yayi Ringing tauka tayi Nasir ne ko sallama bayyi ba yace'' mommy meye damurwa ne yajikin nata".?
Mommy cikin mamaki tace'' waya gaya maka kai kuma"?.
"Mommy yanzu ba lokacin wannan tambayar bane meyake damun Nasrim ".
Mommy tamasa bayani halinda ake ciki
cikin rawar murya yace" mommy mommy Dan Allah ku temake kar ku farka min Nasrim kubani two hours
ya k'arashe maganan kamar zayi kuka
hakan ko akayi mommy de tafara bata temakon gaggawa tana jiran zuwan Nasir da yace mata gashinan a private jet
yana sauk'e direct hospital din ya wuce cikin tafiyar sa kamar zai tashi sama yau ba tafiyar k'asaitan labor room din yawuce Hajja suna parlourn ko kallon su bai tsaya yayi ba ya wuce Nasrim tana ganin sa ta fara yun k'urin zata tashi da sauri mommy da Dr Hafsa suka mai data
cikin wahalalen murya tace'' mommy ku rufe min jikina mommy me wannan bayahuden zan min yafita".
Mommy tace'' haba Nasrim dan uwan ki ya damu dake tun daga Dubai fa yazo yanzu dan ya temaka miki".
"wa mommy ni wllh ko zan mutu idan wannan banzan ya taba jikina ban yafe ba kubar ni na mutu kawai."
ahankali Nasara yake takawa idon sa cike taf da hawaye afili yafurta mommy haka cikin Nasrim yaka haka yamai data haka yabata wahala mommy me yasa baku gaya min ba".?
ita ko Nasrim sai k'okarin rufe jikin ta take ganin zata masa tijara yasa yayi wani irin daure fuska ya goma Nasaran sa sak ya janye zanin da take k'ok'arin rufe jikin ta dashi ko safan hannu bai tsaya sawa ba ahankali cikin kwarewa ya tura hanun da k'afan cikin mommy da Dr Hafsa yan kallo suka zama suna mamakin yanda akayi Nasir ya k'are wajen sarrrafa k'arban haifuwa
shafa goshin ta yayi cikin taushin murya yace " ki yi Nishi".
kafin yarufe bakin sa taji nishin yazo da kansa sai ga d'a yafado zata sauk'e numfashi taji wani sabon nishin yana taso mata wani d'an dan ne yasake fadowa ba ad'au lokacin ba sai ga wani dan d'an
cikin kan k'anin lokaci Nasir ya yanke musu cibiya sai faman kallon yaran yake yarasa murna zayyi ko bak'in ciki yasunan yaran nan yan halak ko Haram ko y'ay'an k'addaran bai ta bajin yayi nadama kamar yau ba
jiyayi hawaye ya sirto masa atake yaji wani irin son yaran yashige shi
Mommy ta kalli Nasrim tace'' kiyi shiru kidena motsi dan mahaifar ki tasamu ta koma dai-dai".
Dr Hafsa sai kallon Nasir take da jariran ta kasa hakura tace "ikon Allah Dr Fanna kin ko ga yanda jariran nan suke kama da Nasir"?.

Mommy ta sake kallon jariran da Nasir yake shirin daurasu girjin Nasrim tace'' sosai ma kuwa ai kamar sanda aka fito da Nasir aka bani nake kallon su".
shide Nasir bayyi magana ba yafice gaba daya yarasa meyake masa dadi dan wani irin tausayin yararan da soyayyar su ya mugun shigar sa lokaci k'alilan
Ummm
Zokaga murna awajen Hajja da sauran mutanen gidan three brother
Agrif ba Wanda yagaya masa sai a status din Nasir yagani atake yabincika aka sanar masa ai Nasir nema ya karbi haifuwar aiko bashiri shima ya dauk'o jet din ana shirin sallaman su a asbiti yashigo jiki a sanyaye yake kallon kowa har aka shishiga mota aka fara watsewa shima motan daddy yashiga ana shirin shiga sallan magariba suka k'araso dan haka iyayen maza a masallaci suka tsaya bayan an idar da sallan Agrif yace " daddy Abu dan Allah ku gafirceni akan abinda nayi da wanda zanyi yanzu daddy ni Haruna nasaki matata Nasrim alokacin da take da ciki batare da sanin ita kanta ba gashi yanzu ta haifu hakan yanuna ta gama idda kuma yanzu inason Mai da auren mu dan haka ga sadakina amai da mana auren mu yanzu batare da sanin ta ba bana son iyayena mata su sani".
ya k'arashe maganan yana fito da kudi a al'jihun sa
yace ga sadakin ta malam liman dan Allah katayani bawa iyayenan hakuri nayi kuskure kuma zan iya daukan kowace irin hukunci amma banda na kin maida aurena a wannan lokac......

wani dogon ajiyar zuciya Nasir ya sauk'e yace " Al'hamdulillah anzo wajen amma Haruna kayi kuskure idan kana tunanin zan sake barin ka mallaki Nasrim dama so daya tak take zuwa mutum arayuwa Nasrim ta *saku* ba wani batun maida auren tunda ba iddar ka akanta ayanzu Nasrim iko na ce ni zan aur......................

*to masoya muje zuwa gar kuka ina gudu batare da na fayya ce muku kamai ba labarin FURCIN NA NE labarin ne me tsoyo Sosai shiyasa nake saurin dan kurzu cikin labarin kar ku manta rikicin babban gida ne ta ko ta Ina rikin zai b'ullo dukiya soyayya sai munshiga cikin labarin de Dan har yanzu shinfida ake*

*Sai naji comment din ku*

*ban baya ko cin gyara ko kwarafi 08062383027*
*Bj*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
( _rikicin babban gida_)

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

*11*

Ni nake da ikon aurar da ita awanda ya dace kai baka da ca da ita ba".
Agrif ko kallon idan Nasir yake bayyi ba ya cigaba
yace' "Dan Allah liman idan har baka bawa iyayena hakuri an maida auren nan anan yanzu ba idan munshiga cikin gida za a iya samun babban matsala Dan Allah ka dubi wannan buk'atan nawa".
Abu juyowa yayi cikin wani irin b'acin rai yana kallon Nasir yace' Nasir wakake son ka aurawa Nasrim".
kafin Nasir yayi maganan daddy yace " ah ah Abdulrahaman ba ayi haka ba idan akace baza amai da auren nan ba ba ayiwa Baban gidan adalci ba kayi duba da tsoron Allahn sa amasa adalci
yayi saki batare da sanin kowa ba sai shi sai zuciyar sa amma yaji tsoro Allah yakawo kansa dan a halatta masa matar sa bai kamata mu masa haka ba ida yacigaba da zama da ita ahaka wayasa amma tsoron Allah yasa yakawo kansa ni dama na san Baban gidan me tsoron Allah ne da bin dokokin sa kuma basai mun bincika dalilin sakin ba ni dama tun auren sa nasan cewa da abinda yake damun sa".

Abu yace" to yafadi akan me yasake ta shida ko zaman kirki bayyi da ita ba".

Murmushi daddy yayi yace "shi zurfafa bincike a tsakanin maurata ba zai kawo na matsa lahaba ba nide ya burgeni da yaji tsoron Allah nawane ake saki ukku amma matar da mijin su rufe abin su azauna ahaka ayita haifan yara shegu acikin gidan aure shiyasa zaka samu mutum da uwa da uba amma tantiri ya daddabi iyayen da dangi yawanci aka bincika ba y'ay'an sunna bane".
Man liman yace" hakane alk'ali ku kuke jin abubuwan da dama nima yaron ya burgeni Ina shawar tanku da amaida masa matar sa tunda dagani koma meye yayi nadama Allah yakiyaye gaba".
Abu de bai soba dan gani yake Agrif yana samun Nasrim a arahane yasa yake duk wannan abubuwan
Daddy ne da kansa yabada sadakin dubu shamsin mutane suka shafa fatiha wani irin kallon nayi nasa ra Agrif yadin gayiwa Nasir
sosai man liman yayiwa Agrif nasiha akan saurin sakin aure yana kawo da nasa kuma ba a saki cikin b'acin rai duk abinda matar ka tayi maka wanda yakama na sakine kada kayi alokaci kabari ka nutsu sosai kafin ka furta saki dan gujewa danasa".

Agrif yace" nagode Baba malam insha Allah aurena da Nasrim awanan Karan ba saki".
hakade kowa ya watse
sai Agrif da Kamal da Nasir da bashi da niyar tashi ma Kamal ne yafara mek'ewa yana kallon Agrif yace" Haruna kasamu dama fa daya dama Kai bayan tafiya da kayi kabar da harda saki kamata kwata kwata Nasrim bataji dad'i aure ba Dan me zaka maida had'in gida haka wannan ai yazama had'in muguta ni ina zaune da taka k'anwar lafiya amma ni tawa tana Shan wahala wllh badan Allah yariga ya k'addara rabon wadan nan yara har ukku a tsakanin kuba da bazan bari amaida auren ba".
dariya Agrif yayi yace " shegen sama wai Kai Yaya ko to nagode da naci al'barkacin yarana kaga tun daga yanzu sun faramin amfani Allah ne kadai yasan AMFANIN da zasumin zuwa gaba na gode Allah da ya bada yaran nan da sunana kuma har abadan sunanan zasu amsa".
Ya k'arashe maganan yana yiwa Nasir wani kallon k'eta
shima Kamal dariya yayi yace" amma fa mutumina kayi mugun iya zubi yara ukku lokaci daya three brother sun dawo congratulations".
ya k'arashe maganan yana mek'ewa Agrif hannu kama hannun sa Agrif yayi suka fita suka nar Nasara awajen

****************
Acikin gidan
sai da akayiwa jaririn wanka aka kin tsasu cikin fararen rigunan su over roll sai asannan kamansu sak da Nasara yasake fitowa Izza tace'' kai masha Allah yaran nan kyawawane amma mamaki na mugun kama da sukeyi da ya Nas ".
Chapter 35 · 0% Book details