← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 100

Sashe 100

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sai humaira ita yaran ta hudu duk maza ABID RAYYAN AMRIN sai ABDULSAMAT dinta babba

Sadiyan Abbaty yaran ta shidda amma ita yanzu ma shayarwa take dan ta nafari mai sunan baban ta wanda suke kira da Marhaf shine suke soyaya da Rumana ƴar gidan Zahra yanzu ma batun auren su akeyi sai yarda ta ukku Iman

a cikin shekarun nan anyi rashin Hajja da Hajja Ta soro

yara matan Muwadda Musanat Zeenat duk sunyi aure Abdul ma yayi aure har lil Agrif shima yayi aure

rayuwar gidan abin koyi ne da ban sha'awa sabida inde macce aka haifa a three brother to ana yayeta awajen Nasrim zata tashi in kuma namiji ne wajen Izza
akwai haɗin kai da fashimtar juna sosai cikin family

Mommy ta kalli Khaflan da yake cika yana batsewa fuskan nan cike taf da kunci tace " tode kaji umarnin dana baka ko ".?
cikin ƙunci yace
"Amma Mommy ni wana taba cewa zamana haka yana damuna ni yaka mata na yan kewa kaina hukunci bawani daban ba".

"nade kaya maka nan da wata biyu auren ka da Iman".
da sauri Iman tayi saurin sun kuyar da kanta zuciyar ta yana bugawa lalle an hada ta da aiki Khaflan tayi ta maimaita sunan a zuciyar ta".

Hazeek ne ya sameta a kitchen tana ta faman hada coffee yace "Mami Papa yana jira fa".
ya ƙarashe magaban tareda ficewa ta kofar baya
a palon ta sameshi yana ganin ta ya meke tsaye yace "my Nan kin manta da asalin Babyn ki ko".
Rujuluss na tsaya lallashin Iman ne Allah nide Mommy bata kyauta min ba yaza ayi tace zata hada Iman mai hakuri da hankali da wannan yaron wllh Iman tana mugun tsoron Khaflan hadin bayyi ba".
kamo hannun ta yayi yace "niko nayi mugun yabawa da zabin Mommy akan kaina ma balle ɗana da yayi dace da yarinya mai cikekken nutsuwa da asalin kyau kuma naya mugun sonta fiye da yanda ni nake son uwar sa".

da sauri Nasrim ta rufe masa baki da tafukan hannun ta tace "no bawani namijin da zai so matar sa feye da yanda ni mijina ya soni duk gatan macce kar nake kallon ta amma my dear seriously fa Khaflan yafi karfin Iman because idon yaron nan a bude yake sosai yanzu makaga lallashin da nayi wa yarinyar
ga tana mugun tsoran sa".

"muna furcine irin na goggan ta marikiyar ta kin manta itama haka tayi ta burgan bataso kinsan ance idan daɗi yayiwa mutum yawa sai yace Allah gani kasheni badan Mommyn ta dage sai Iman din ba mutane nawa ne suka min maganan dan Allah ga ƴarsu nan ta kafe sai Khaflan kinsan de idan irin Iman dubu yake so my son zai samu ko".
dukan ƙirjin sa tafara tana cewa ni ni zaka cewa munafurcin mariƙiyar ta sai nace nafasa tunda gashi kayi furfura".

"furfura adone ki fasan man nima Babby dina ya huta da yawan matsa dama kin damar min shi".
ya ƙarashe maganan ya na daukan coffee dinshi yayi sama cikin sauri itama ta rufa masa baya tana cewa Allah sai nayi sati ban kulasa ba ai zanga mai damuwa
"psl my nn kona yau bazan iya ba ai kingane ". yayi magana yana ɗaga mata gira daya
tura baki tayi tare da fanko
ƙofar kafin ya shiga

Khaflan
aika Harun ɗan gidan Baba yakumu ya kira masa Iman iman ƴar wajen Sadiya da Abbaty ce
tana shigowa ta samesa zaune a kan cushion ya meƙe ƙafar sa akan santa table da remote a hannnu sa fuskan nan nashi a mugun murtuke Iman adduar ta dingayi ganta a ƙasa ta ƙaraso sallama tayi tareda duƙawa
tace "Big bro barka da war haka ta ƙarashe maganan bakinta yana rawa bai ko juyo ba a hankali ya sauƙe numfashi yana cigaba da kallon kwallon sa
Iman tun tana durƙushe jin ƙafarta yana neman sajewa yasa ta zauna tare da kwantar da kanta a kan hannnun kujera tasan tunda ya shareta sai sanda yaga dama
sai daya tabbatar tayi bacci ya sauƙe ƙafarsa a hankali yana murmushi ya taso ya durkusa a gaban ta ya zubawa kyakyawan fuskan ta ido yana murmushi
ahankali yakai hannu kamar zai shafa fuskar ta kuma yayi saurin janyewa
cikin taushin harshe
yace "nutsuwar ki kunyar ki hakurin ki kyawun suffarki zubin dirinki abin so da alfaharine ga ABDULSAMAD NASIR ABDULSAMAD
I love you with all my heart amma kidena tsorona ina son muyi rayuwa kaman friend to friend ina son muyi rayuwa kamar Mami da papa zamuyi koyi da rayuwar su abin birgewa hakan bazai samu ba sai kincire tsorona nima mutum ne kamar kowa im so sorry babu wata macce a zuciyata .....

Iman da baccin ta bayyi nisa ba tun saukowar sa ta farka amma tsoro ya hana ta bude ido jikin tane yadau wani mugun rawa wanda yasa Khaflan ya gane idonta biyu
" open eyes ".
yace da sauri ta bude ido yace " ya zanyi ai dole nace I love you tunda an liƙa min ban sani ba ko ke kin shirya rayuwa da *mai idon ƴan iska ɗan duniya bai zubin samudawa*."

cikin tsoro da mamaki ta ware banyan idonta dama yasan tana ƙiransa da wannan sunan
giran sa daya ya ɗaga mata alaman ita yake jira ta bashi amsa

cikin in ina tace "dan Allah kayi hakuri YAYA".

"ok zanyi hakuri amma akwai sharadi zakije awannan daren ki roƙi Abu da Daddy akan gobe da asuba adaura mana aure jirgin tara zanbi tare zamu tafi in kinyi haka shike nan

"YAYA bazan iya b................

*ALHAMDULILLAH ALAH KULLI HALIN*
*masoya anan yakamata mu dakata dan gudun kada mushiga rayuwar yara bayan munga na iyaye da kakanni ma*

*BATUL ADAM JATTKO*
Chapter 100 · 0% Book details