← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 100

Sashe 2

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajja ta ce" sosai na yaba da hankalinta ganin har yanzu bai samu nusuwa ba ne ya sa ban matsa masa a kan maganarta ba, kyanta a ce an haɗa daurin auren da arba'in din Halima amma Abdulsamad don Allah a yau nake son idan Dr Fanna ta zo kamata magana ya dace ta fada mana garinsu da inda iyayenta suke mu je neman aurenta nide iya bincikena an tabbatar min da cewa aikine ya kawota ba a nan take ba na san de ba zai wuce a ce yar maiduguri bace tunda ga zanen barebari a fuskarta kuma sunanta ma na barebari ne za ta kasance yar maiduguri ko yobe ".

Cikin sanyin murya Abdulsamad ya ce "Hajja da wuri haka ni fa ko maganan ban mata ba a dan ba ni lokaci".
Hajja ta ce
"Ba lokacin da zan ba ka inason ka samu wacce za ta rage maka damuwa kuma na san Dr Fanna wayayyiyar mace ce za ta yi saurin mantar da kai ko m...... "

Ba ta karashe maganar tata ba gani wani irin gumin da Amina matar Abdulraham take tsatssaɓowa, ganin yadda ta tsorata ta tsaya da maganan ya sa duk suka kalli inda take kallo da sauri Abdulraham ya ce "ya de Amina a hankali ta da fashi tare da sauka akan jujeran ta sunkuya k'asa tana ta faman yarfa hannu daidai lokacin Dr Fanna ta shigo tun kafin ta k'arasa ta san halin da ake ciki da sauri ta koma mota ta sako safan hannu tana tafe tana sanya ta har ta karaso tana duba ta ta ga ai kan d'a ne ma yake kokarin fasowa ta kalli mazan da duk sukayi wani cirko-cirko ta ce "Don Allah ku ba mu waje" ko suna ba su ma kai ga ficewa gabadaya ba suka ji kukan yaron a tare suka juyo suka yi murmushi tare da dafa kafadun juna suka fice haifuwa ya zowa Amina da sauki sosai duk da tun dare take abunta amma dayake macce ce mai dauriya da jaruta Koda Abdulraham ya gane cewa ta yi ba wani abu dama ance ana jin haka idan ciki ya tsufa cikin k'ank'ani lokacin Dr Fanna ta gyara Amina da zankadeden jaririnta. Zo ka ga murna a wajen Hajja da yaranta, Nasir ya samu aboki ranan suna yaro ya ci sunan Baban su Abdulsamad Muhammad amma Hajja tace amasa al'kunya da Araf washe garin sunan Araf Hajja ta sake bawa Abdulsamad umarni da babban murya akan yayi wa Dr Fanna magana. Bai yi musu ba bayan zuwanta sai da ta zo fita ya tashi ya bi bayanta Sai da tashiga mota yace "Dr idan ba damuwa in shigo ina son magana dake".

Kallon sa ta yi cikin tausayinsa za ta fito ta ga ya shiga shi ma rufo kofar bangarensa ya yi ita ma ta rufo nata sai da ya ja wasu dak'iku yaja numfashi yace "kin samu daman karanta wasik'ar Halima".
ta ce"E. Duk a kan jaddada alk'awarinta ne da kuma in rik'e mata kai da Nasir da mahaifinta amana".

Yace "ni ma nawa akan hakan ne to ya kiga".
Ta numfasa cikin sanyin murya ta ce "Gaskiya daga b'angarena akwai matsala ina tsoron yanayin mahaifiyarku gani nake kamar ba za ta yarda ka auri y'ar gidan christian ba ".
A firgice ya kalleta yace what Christin kuma ke din dama a kanuri akwai arna".
girgiza masa kai tayi ta ce
"Ni ba kanuri ba ce kamar yanda mutane suke dauka bace nagaji da bawa mutane amsa a a a ne yasa nabari a ni kanuri ce har naje nayi University dina a garin maiduguri dan na koyi irin yaren dan ance a can suke na gaji da jayayya da mutane akwai sanda ina yar secondary a logos wani malaminmu dan kanuri har marina yayi wai ina boye yarena tun daga ranan na bincika ina ne wannan k'abilan ta kanuri suka fi yawa zan je na iya yarensu dan tun ina yarinya na gaji da wannan tambaya da mutane suke min".

Dakatar da ita ya yi yana cewa " kin gane duk wannan bayanan naki bana ganesu sai kin bani labarinki ko zan tsinci wani abu ina cikin firgice Fanna jin ke ba kanuri ba ce".

Wacece Fanna?
" sunana Fanna emeka ni y'ar k'abila ibo ce a cikin garin Legos a anguwar pester na samu kaina sunan mahaifiya ta emeka dalilin zuwana nan arewa bayan gama secondary naga wani da irin zanena shi ne nayi ta nace masa har na san masaukinsa ashe irin ciranin nan ya zo shi dan maiduguri ne wasa-wasa muka kulla soyayya da Sharif ba tare da sanin momyna ba ina kokarin boye mata ne saboda ta tsani musulmai kuma tun ban gama sanin kaina ba momy take koyamin ak'idan k'in musulumci kullum gargadinta da nasihartta akan na guji musulmai duk inda suke momy duk inda taga musulmi sai ta zage shi ta ce mana amma sai ga shi nayi saurayi musulmai a dare daya muka yanke shawaran mu gudu da Sharif zuwa garin su maiduguri iya takardun secondary da primary dinna kawai na dauka muka kamo hanya Sharif shi ma yaji tsoron nuna ni ga mahaifansa, dan haka ya nemi gidan haya ya sani ya kuma nema min makaranta kasancewar takadduna sunyi kyau sosai ba a sha wahaln sama min gurbin karatu a jami'ar ta maiduguri ba shekara bakwai na zama cikekkiyar likita duk da kananun shekaruna a lokacin muka shirya aure da Sharif dan yasamu rufin asiri sosai ya bude shagon kansa a Lagos shi ya gina min wannan gidan da kaga Ina ciki a anguwar sardauna crystal muyi dashi zamu yi auren a boye har mutara yara lokacinda iyayensa ba za su iya cewa ba sa sona ba shi ne dalilinsa na nema min aiki anan zuwan mu kano dan ya tsara a nan zai ajiyeni yas ha fama sosai kafin yasama min aki anan malam aminu kano Iya abinda nasani kenan a tarishina ban taba sanin ina mahaifina ko danginsa ba dan duk sanda nayi gigin tambayar momy emeka Ina Babana to zanci na jaki kuma za ta yi sati bata ba ni abinci ba da kudin makaranta kwata-kwata ba ta bani daman in san waye ubana ba sai de kuma ina wayo Ina gane duk yanda akayi ubana musulmine kuma dan yaren kanuri shi ne yamin wannan zanen da kuma sunan kanuri duk yanda aka yi akwai wani abu me girma da shiga tsakanin su shi ne ta tsane sa."

Abdulsamad yace "baki gayamin ya matsayin ki a adini ba ko kin karbi musulumci".

Ta yi murmushi ta ce "Ai tun a Lagos Sharif ya sa na karbi musulumci ka san duk wani tarbiyar da iyaye zasu bawa yarinya idan ba ayi sa a ba cikin second k'adan soyayya yake rushe shi muna zuwa maiduguri yasani islamiya ta matan aure".

Abdulsamad yace to yanzu ina shi Sharif din".
ta sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu ta gode hawayen da yadade yana kwaranya a fuskan ta
tace" Sharif yayi hasarin mota alokacin da muke tsaka da shirye shiyen auren mu saura kwana biyar a hanyar sa ta dawowa daga Lagos".
ta k'arashe maganan cikin fashewa da kuka sai da ya bari ta yi iya yinta dan shi ma kukan zucin yake na rashin matar sa sai da suka dauki tsawon lokaci cikin sanyin murya yace sorry Dr Fanna namiki alk'awarin za ki same ni fiye da Sharif a rayuwa ke din zabin Halima ce zan iya sadaukar da komai a kan zabinta musamman tunda kika nuna min kina son Nasir kin gama min komai a rayuwa ni sunana Abdulsamad kamar yanda kika gan mu, mu yan ukku ne yan'uwana Abdulmajid Abdulraham.

Asalinmu iyayena duk 'yan nan kano ne a sani yan kofar na'isa amma Hajja wato mahaifiyata tana da dangin mahaifiya a Dardum wani k'wauye a jahar zamfara iya mu ukku nan suka haifa shakara daya da auren su Allah basu mu yara ukku maza a lokaci daya daga kanmu kuma ba ta Kara ba ni Abdulsamad, Abdulraham, Abdulmajid.

Mahaifinmu malam Haruna baza a kira shi me kudi ba sai rufin asiri dan sana ar dinkin maza kawai yakeyi ni Allah yamin nasibin tun ina shekara 9 nake bin Hamza wani abokina shagon Babansa muna taya shi auna kayan masarufi alokacin muna primary ne Allah yayi wa Baban Hamza rasuwa kasancewan suna da yan uba suka raba gado daga nan kasuwa ta rushe adan kudin da nake Tarawa awajen Hajja na ce tabani na sari kayan aleyoyin na yara idan nazo daga makaranta zan dinga kasawa a kofar gida hakan ko akayi Allah Ya sawa abin da na fara kamar wasa albarka har kofar gidanmu ya zama matattaran tara yara saboda ina da fara'a da saurin sabo tun ina bazawa a barantin Hajja har Baba yasa aka bugamin yar benci ina bazawa tun a lokacin ko ina a jikin bencin na rubuta
3brothers ajiki wanda yanzu haka shine 3brothers company a fadin duniya ni kasuwancin bai barni nayi karatu me zurfi ba amma kinga yan uwa na sunyi Abdulraham Lecturer a B. U. K.

Abdulmajid kuma alk'ali abin da yasa zan gaya miki dukiyar gidan mu nawa ne saboda shi sha'anin aure ba a boye-boye na san zama ya yi zama zaki gane to ina son na sheda miki yan'uwana suna da mahimmanci a wajenana kuma sun fiye min komai a rayuwa ba na son ki dauki kanki amatsayi kin fi matansu ki dauka duk kanku ɗaya idan Allah Ya yi aurenmu da ke."

Ta ce "in Sha Allah amma ba ka karasamin ba ya akayi kayi kudi me yawa a cikin k'ananun shekarun naka Wanda har yanzu bazaka wuce shekara talatin ba amma duk Nigeria ba wanda bai san 3.brothers ba".
Chapter 2 · 0% Book details