← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 100

Sashe 42

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummy Papan mu ne fa yafada ke meye naki da zaki hana wllh nide ba Wanda ya isa yahana ni zuwa London makarantan mekyu ne ai Papa ya furon videon makarantan ke dama bakya sona muta....
marin da yaron ya sha awajen Nasrim shi ya dakatar dashi maganan defe k'unci yayi yana kallon ta ido cikin ido yace "kika mareni wllh sai na fadawa papa kuma agaban Abban kika dakeni bai ce komai ba".
ya k'arashe maganan tare da taka steps da sauri ya haye da alaman de waya zaije yayi".

ba afi mintuna 3 wayan agrf yayi ring Nasir ne dauka yayi yana murmushi yace "a a papa ankai k'aran ummy kenan".
"dakata Agrif ba wannan ne damuwar ba ina ga lokacin da nabaka kafito ka gayawa matar matsayi na awajen yarana yayi wllh ba barazana nake ba Kai kasani".

dariya Agrif yayi yace"kayi yanda kaga yadace".
ya kashe wayan yana kallon Fayyat da yake masa magana Fayyat yace " Abban wai kaje inji Hajja kai da ummy".

Hajja tace'' to dalilin ta raku anan shine Ina son hada aure tsakanin Izza da Haruna Wanda ina fatan yazama alkairi ".
Abu yace" Hajja aure kuma ".?
"Eh wllh kuma duk Wanda yayi yunk'urin hana auren nan to mut zai mutu ayi bashi saboda ni naga ishara akan auren Abdulmajid da Fanna rabo ya kashe Abdulsamad yanzu inda nayi kishin d'ana na hana ayi auren da rabon Nasrim mut zai kashe ni ashi bani".

shiru daddy yayi amma gaban sa yana faduwan dan shima yasan kishin y'ar sa
Abu yace " gaskiya Hajja wannan bame yu"
"Kai gafara can rufemin baki meyasa sanda Abdulmajid zai aure Fanna baka ce bazai yuwu ba saboda ita Aisha ba y'ar gida bace ba sai yanzu da abin yazo takan y'ar ku wato bakaso ayiwa Nasrim kishiya ko t.......
tashi Nasrim tayi tsaye tanawani girgiza kai tace'' wllh awannan karan ikon ki da isar ki bai samu gurin zama ba kuma gigin tsufanki bai gaya miki gaskiya ba wll......
marin da daddy ya wanke ta dashine ya k'atsar da ita wani irin ihun murna Khafulan ya saka yace "yeeeeee daddy yarama min marin da tamin bari naje na gayawa Papa...........

*Mu hadu a 14 Insha Allah*
*ina sake baku hakurin rashin jina a akan lokaci wllh Ina da uzuri sosai ne*

*08062383027*

[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
( _rikicin babban gida_ )

NA

*BATUL ADAM JATTKO*

*14*

Agrif ne ya mek'e tsaye yace "daddy maza ne suka k'are a duniya zan auri suruka ta matar k'ani na dade ace nine na rasu sai Aiban ya auri matata amma ni babba ai da kunya kuma ba ga Abbaty ba shi ya dace ya aure ta.....

kuka Hajja tafara Sosai tana cewa
"Abdulrahaman kun gaji dani kungaji dani agaban ku yaran ku suke nunawa ban isa ba Allah sarki Abdulsamad tun Halima tana y'ar tasisiya Haruna yaba sa ita godiya ma yamasa amma gashi ku kun nu na ni ban isa da yaran kuba......
Daddy yace "Hajja dan Allah ki dena fad'an irin wannan Magan ganun taya zamu gaji dake Insha Allah ki bamu nan da kwana biyu zamu shayo kan abun".
tana jan majina tace''
ni bawani wanaki da zan baku nagama yanke hukunci ba inda yarinyar nan Izzatu zata fita tana gidan nan yo Allah na tuba idan Izzatu tabar gidan nan ai na banu ai saide na bita abin da take min akwai mai yimin shi cikinku da yaran naku yanzu gashi bazawarai sun fara fito mata za su rabani da ita akan me bazanyi abin da yadace ba".
Agrif jan hannu Nasrim yayi suka fita
su daddy kuma suka zauna lallashin Hajja

"haba my wife nifa ban amsa ba kuma wllh duk yanda za ayi Sai de ayi bazan taba yarda ba".
cikin tsawa Nasrim tace
"ai wllh Kai ma da lefin ka yanzu ta isa ta tukari wancan bayahuden jikan nata da take tsoron sa ne tun shekarun baya da ya mata ta tas kaji ta sake masa magan yayi aure ne
wllh ban taba jin na tsani Izza ba sai yanzu wai duk wannan abin da ake ko ta d'ago kanta ta naji".
"Please Sadiya ko mutuwa kikayi bazan auri wata ba zan cigaba da renan soyayyar ki ta isheni".

numfasawa tayi tace'' to yanzu ya za ayi kasan matar nan idan tafara abu sai tayi shi yanzu zata sako sau Abu agaba har sai sun mata yanda take so".
shiru yayi can yace " kiyi hakuri nan da sati 4 zan gama aikin da yakawo ni ba dan Kamal magan daci bane ma da yanzu munci k'arfin aikin muna gamawa zan daukeki mutafi tunda kin gama karatun idan muka tafi ai basai ta ganmu ba ni yanzu jikin Aiban ne yafi damuna har yanzu bai dena aman bane?".
"Eh Wllh bai dena ba zazzabin ne ma ajikin sa itama Zeenat banajin dad'i a part din mommy ta kwana".
"Subbahanallah meyake damun ta".?
"Wllh ban sani ba mommy ce take gayamin jiya amm.....
kiran wayan Nasrim ne ya katse ta tana dubawa taga mommy ce tana picking mommy tace'' kizo ki same ni yanzu ke daya a sama".
jin yanayin muryar mommy yasa gaban Nasrim faduwa tace'' mommy lafiya?".
tayi maganan tana mek'awa tsaye
Agrif shima ya mek'e yace "lafiya".

Nasrim tace" mommy ce tace'' nazo ni daya ina zuwa".
tayi maganan tana ficewa
mommy ta zuba uban tagumi Nasrim ta shigo har ta zauna mommy batace komai ba kanta a k'asa
Nasrim tace "mommy dan Allah kece kadai kika san yanda zaki shawo kan daddy dan Allah karki bari ya yarda da abin da Hajja tazo dashi wllh zai iya zama babban matsala a gidan nan".
Mommy kamo hannun Nasrim tayi ta d'aga kai ta zubawa Nasrim idon ta da suka gama canza kalan ja
Nasrim tsorata tayi da ganin yanayin yanda idon mommy ya kumbura yayi ja cikin in nina tace'' mommy me yake damun ki akan maganan auren Izza ne wllh nim.....
"Nasrim ba wannan ne damuwa ta ba kinsan meye dalilin jinyar Aiban da Zeenat".?
'Ah Ah".
Ahankali mommy tace
"To GUBA aka basu".
"What mommy guba waye zai bawa yarana guba me nayi da za amin haka wa nacuta wllh bazan yarda ba".
tayi maganan a gigice tana mek'awa tsaye kamo hannun ta mommy tayi tace'' please Nasrim wani abun yafi gaban a bayya nashi dan idan baka iya kama barawo ba shi b'arawo zai kamaka ke lawyer ce kin san komai ki nutsu sosai bana son kowa yasan wannan batun dan idan meshi yasan mun sani zayyi kokari sake sirrace kan sa amma idan mun nuna bamu gane ba zamu fi saurin gano me lefin".
Kuka Sosai Nasrim take tace''mommy ina Zeenat ina Aiban din mommy mutuwa zasuyi ko"?.
cikin kuka mommy tace'' insha Allah Zeenat baza ta mutu ba dan yanzu an samu kan abin kuma ita bata ci dayawa ba kinsan ita bata wani cin abinci sosai so bai higa jikin ta kamar Aiban ba tana gidan Dr Hafsa anjima za adawo da ita amma Aiban kam sai adduar".
"yanzu mommy wa kike ganin zai iya min wannan".?
"Nasrim ke lawyer ce ke yakamata ki gano ko ma meye amma nafi jin duk wanda yaso ai kata hakan ba akan komai bane akan dukiya ne ganin bani da kowa sai ke ke kuma Allah ya al'barkace ki da y'ar dan haka ma kusan tan mu sune abin tuhumar mu".
Nasrim ta gyad'a kai tace
"Mommy idan ko hakane ba Aiban da Zeenat kad'ai za aso halla kawa ba hadda ni dake da sauran yaran".
"wannan shine tunanina nima Nasrim amma dan Allah dame muka raji mutane"?.

Nasrim tace "mommy bazamuyi saurin zargin mutane ba sai mun zauna da yaran mun binciki waya basu wani abinci ko sha zai iya yuwama ko a makaranta suka saya ko kuma wani akasin aka samu".

girgiza kai mommy tayi tace'' Ah Ah duk nayi binciken wannan guban me tsadane sosai da gayya aka saka kuma yana iya kaiwa watanni ajikin mutum bai fara amfani ba amma idan yafara yana kisa sosai".
"Mommy nashiga ukku dan Allah mommy kisan yanda zakiyi kar na rasa Zeenat ko Aiban Allah Agrif yafi sonsu fiye da su Khafulan ma".
" insha Allah zasu tashi amma inason ki kula dasu Khafulan Sosai duk yan da akayi yanzu su ake hari akan su zamu d'ana tarko zasu koma part dinki gaba daya akwai camara da za'a saka musu ajikin rigunan su kinga ke kina da kula sosai kuma part din ki ba ma'aikata ajiye wani batun kishin ki kula sosai da wannan matsalan".

"tab ai mommy batun kishi ma abin dubawa ne dan wllh zan iya kashe duk wani wanda yaso yakawo min cikas arayuwar aure na wannan *FURUCI NA NE* ".
"Nasrim baki da hankali meya hadaki da irin wannan FURUCIN baki san yana da illa ba wannan furucin naki ma zai iya janyo miji abinda bakya so din ai".
"Kai mommy ke dama haka kike bakya so ki yiwa mutum addua mekyu".
"Ummm Nasrim shifa rayuwa yanda ka daukeshi a haka zai zo maka musamman kishi duk ta yanda kika daukeshi ta haka zai zo miki idan kin daukeshi da sauk'i zai zo miki da sauk'i idan kika dauka da zafi haka zai zo miki ba wani adduar da zan miki Wanda zai canza k'addara sai muyi fatan yazo da sauk'i dan haka ki shafawa kanki lafiya ki dauki Izza amatsayin abokiyar zama dan Hajja bata magana batare data yishi ba..........

"to wllh mommy awannan karan ta tafka kuskure dan wllh inde Ina raye ni kad'ai ce matar Agrif".
"Nasrim wai dama haka kike amma abu kadan kice Allah yace annabin yace kina da sani amma kina takewa".
"Mommy inde akan kishin ne koma meye a fadam.......
Chapter 42 · 0% Book details