← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 100

Sashe 83

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motoci ne sukaje taryansu airport dare da bodyguard sai faman fuɗawa Nasir ake shiko cikin Izzar sa yake takawa idan kagan shi zakace baƙin cikin zuwan yake nan ko farin cikine fal aransa ayau zayyi arba da Nasrim Khafalan Abdul da su Ummda drive yanayin parking scurity sukayi kan motan da Nasir yake bude masa sukayi Nasir ajiyan zuciya ya sauke yana ƙarewa haraban gidan nasu kallo shekara guda rabon sa da gidan uban sa shikenan yanzu yadawo cikin ta gyara zaman black glass din sa yayi yana dan sakin fuskan sa hango Baba Yakubu dayayi yana ta zuba masa kirari ahankali yafito da ƙafarsa ya fito yana dan sakin murmushi Baba yakubu yace " garo da garo sai rabo duk wani babba sai Babba wanda yagaji bai saba ba ai ai'kin da wuyar sabawa sai ɗan gado arziƙi jini yake bi NASARA KO GANI KAFI MUTUM NASARA MAI WUYAR FADANCI GOSHIN JIRGI MAI WUYAR KARAU
SAI DAN GADO".

Nasir bin ma ai'katan yayi yana basu hannu suna nuƙewa amma yana sake matsawa cikin sakin fuska yake amsa gaisuwar su daga ƙarshe ya rungumo Baba Yakubu yana tsakar masa murmushi yade kasa magana har Mommy ta shige parlurn Hajja shima sakin Baba yakubu yayi ya dauru bayan Mommy
Hajja rungumo Nasir tayi ta saki kuka tace "oo ni Maryama Nasuru kaine farin cikin gidan nan me yasa ka gujemu". zamewa ajikin ta yayi yana lalashin ta
ya zube agaban Abu da Daddy yace "Daddy Abu.......
sai kuma muryar sa ta fara rawa yakasa ƙarasa maganan kawai ya kifa kansa a ciyoyin ABU yana sauƙe numfashi shafa kansa Abu yayi yace "please my son karkayi kuka kai jarumine jarumai basa saurin kuka musamman cikin yaran su"
yaƙarashe maganan cikin tsigar wasa".

"Abu kugafar tamin kaida Daddy wllh ban wulaƙan taku da son raina ba saide kawai dan banason kuce zaku tursasani zuwa gida ne wanda nasan hakan halakane a gareni dan zan sabawa umarnin Mommy na Daddy ku yafemin duk lefukana Daddy na san na ɓa ƙanta maka nayi Repping din ƴarka aranan auren ta Abu na ɓa tawa ɗan ka AGRIF dare mai mushimmanci nayi sanadiyar jefa ka cikin rashin lafiya Abu idan baku yafemin ba Allah bazai yafemin ba kunje ne mana na wulaƙanta ku na nuna ban san kuba nacuci ahali ........

da sauri Abu ya girgiza masa kai tare da sa hannun sa na dama yatoshe masa baki Daddy saukowa yayi akan kujeran ya ja Nasir jikin sa
yace" my Son mu mun yafe maka dama ba kaine mai lefin ba an hukunta masu lefin..........

"Daddy nima mai lefine na rasa me yasa nayiwa ƴan uwana da banida kamarsu NASRIM da AGRIF haka yasaki kukan da yake dannewa tun shigowar sa gidan Khaflan da Abdul ne sukazo suka faɗa jikin sa suna murnan ga papa wayyo ga papa

hannu biyu yasa ya rungumesu yana tambayar su ina su Muwadda sukaje
su kace uncle yaje daukosu a gidan gyaran gashi Izza da Humaira cikin ladabi suka zo suka gaida shi haka Fajji ƴar gidan Mala yayan Mommy na maiguguri wanda zatayi kusan sa a dasu Nasrim amma budurwa ce itama cikin ɗoki tace "my brother ga sister dinka da baka santa ba."

Nasir kallon ɗaya yamata yagane eh family su ce dan ga kamanan da Mommy har farin ta farace tas kamar Mommy amma dayake ita yar zamanice ta hada da mai tazama kamar zabiyan gyaɗa kansa Nasir yayi yana son yace ƴar wajen waye amma miskilancin sa ya hana
kawar da kansa yayi yafara magana da su Musanat da suka shigo yanzu da gudu suna rige riken faɗa fasa ya kamo hannun Musanat
yace "my daughter kin girma me kike cine murmushi yarinyar tayi tace "papa bakomai....

Ummda tace " wllh papa musanat cine da ita komai ci takeyi sunan tafa ci TARA Allah har yafi so 9 ma takeyi".
murmushi Nasir yayi yana kallon tsantsar kaman Ummda da Aiban hatta maganan su iri dayane jayo yarinyar yayi yana shafa kanta
yace " daughter ai kwara tayi ci taran bakiga tafi Muwadda ba".
ya ƙarashe maganan yana kai hannun sa wuyan Musanat
Musanat tace "Allah Papa ka hana su cemin ci tara".

yace " daughter barsu su fada ai ci lafiya ne wani a gadon asbiti yake sai de ayi ta saka masa ruwa kinga keko kina da cikekken lafiya yanzu koda Boss zaki iya karawa."
ya ƙarashe maganan yana sauƙe idon sa akan Khaflan wani kallon raini Khaflan ya watsawa Musanat amma bayyi magana ba
Hajja tace ina Aisha ina wannan wanda akayiwa rowan imani".

Nasir yace "har yanzu bai dena dukan suba Son kadena sune fa manya yayun ka ne Ummda ce kawai ƙanwarka".

Khaflan yace "ni ina ruwana dasu".
yayi maganan yana rungumo Mommy yace welcome my Mom nayi missing naki thank kinzomin da papa na,"
tureshi Mommy tayi tana meƙewa
tace "dallah ɗagani ni naje nawatsa ruwa sai yanzu ka ganni".

Hajja tace "dama ko ƴan maiduguri sunzo suna can part dinki".
cikin murna tace "har sun ƙaraso gobe sai lagos kenan".

ta ƙarashe maganan tana me ƙewa ta kwashi tarkacen ta tafice

Nasir sauƙe numfashi yayi yace "Daddy Mama Emaka fa ta mutu na kasa gayawa Mommy yanzu idan munje ya zamuyi'".

Hajja da su Abu sun jajanta mutuwar Emaka saboda Mommy ta kwallafa rai akan tanason ganin mahaifiyar ta
Hajja tace " tun yaushe tarasu ".?

Nasir yace "zatayi shekata goma da rasuwa ayanda ƴan uwanta suke gayamin".

Mommy taji daɗin ganin su Baba danginta dayawa suka zo Mala Sharif da sauran su

Humaira da gudu ta faɗa jikin Nasrim tana murmushi tace
" He loves me and I love him very much wllh bayan Khamal ban zaci zan fada soyayya haka ba Zarran yacika namiji wow wllh yafi ya Kamal iya soyayya kodan damafa Kamal haɗin gidane".

tureta Nasrim tayi tace"
Lallle Humaira ko kunyar idona baza kiji ba ki fito a hannun dan uwana ki zauna agabana kina ambaton kina son wani".

Humaira tayi murmushi tace "koke da kukayi soyayya da Agrif kamar zaku cinye juna naga yanzu kin bawa Habib dama.

"cikin sauyin yanayi Nasrim tace "ya zanyi Aisha a take taken su Abu tabbas idan ban fitar da miji ba wllh zasu min dolle da wanda ban sani ba amma wllh habib baya cikin jerin mazajen da nayiwa kaina buri kuma ma nifa soyayya da aure ahalin yanzu basune agabana ba du du du shikara daya da rabi da mutuwar mijina awani matsa sai na fitar da miji akan me".

Humaira tace "pls sis wllh ganin mu duk kan mu ukku a zaune a gidane ya janyo hakan yanzu ba ga Izza ba shekaran Aiban biyar da rasuwa ai basu matsa mata ba saida mu muka ƙaru yawan mune yakawo hakan kuma idon mutanen duniya akan mu yake saboda wannan abubuwan da ya faru especially make amma kinsan wani magana danaji ɗazu a falon Hajja wai an baida kudin auren ki dana Izza ke da izza an muku miji baza abawa Habib kema itama Izza baza a bawa Zayyat ba an fasa saboda wasu matsaloli da suka ɓullu wai abin yaban mamaki to suwaye mazajen naku kuma fa shirye shiryen biki ake daga anzo daga lagos za a daura aure".

Nasrim tace "ban gane ba anayiwa bazawara auren dole ne kuma yama za ayi a ce an bai da kudin auren mu mu ba muji ba".

Humaira tace "kude zuba ido tunda bamu san manufar hakan".

duk gidan kowa yace sai yaje lagos har Hajja da take kushe arna dayake safgar yawone tana wajen ga gaiyar yan maidukuri awani ɗan ƙaramin jiri nasu na family maicin mutum 34 suka shirya tafiyan gasu suda yaran su har ƴan maiduguri su arba'in da ɗaya ne dan haka yaran yawanci a cinyar mutane suka zauna

Nasrim itace kusan ta ƙarshen shigowa dan haka tana shigowa saura seat din mutum biyu kuma ajere dan haka adayan da zauna bayan ta Bukar ne ɗan gidan yayar mommy da matar sa sai daga gaban ta izza da Fajji

tana shirin gyara zaman ta kawai sai taga mutum yana shirin zama a gefen ta cikin ɓacin rai ta fara kalle kalle amma ina ba wani seat sai ƙwaya biyun zama tayi tana daure fuska shiko ko kallon ida take bayyi ba ya zauna cikin izzar sa
Nasrim zama tayi tacigaba da wayan da take ƙamshin turaren sa yana tariyo mata wani abu jitayi gabanta yafadi domin bazata taba banta wannan ƙamshin ba a take taji wani irin ɓacin rai ya ziyar ceta amma ta daure tacigaba da waya da Habib har jirgi yatashi Nasrim tajima tana waya tunkun taji networks ya ɗan dauke bata jinsa sauƙe wayan tayi tana murmushi Fajji da take gaban su tajuyo tace "kai sister irin wannan dogon wayan haka ba sararawa kewai baƙya gajiya dawaya ne baki da wani lokacin sai na wannan koɗaɗɗen meyasa ba kya gajiya .?'
murmushi Nasrim tayi tace "
because my souls and spirit boid with his blood".

zaro ido Fajji tayi tace "rushin ki da jinin jikin ki hade yake da nasa lalle kam ba gajiya cigaba yar uwa

Murmushi Nasir yayi ya kwantar da kansa sosai ajikin seat din yakai bakin sa setin kunnnen Nasrim idon sa alumshe ahankali yanda ba meji sai ita
yace" most of the time whats ours heart desired may not happened
So tari abinda zuciyo yin mu keso bashi yake tabbata ba

wani irin mugun kallon ta watsa masa amma ina ido sa alumshe kamar ma bashi yayi maganan ba

wayan tane yasake rin Habib dinne kuwa dauka tayi tare da gyara zaman earpieces din ta tacigaba da sauraron zaƙaƙan kalaman Habbib

a lagos Mommy tasha kuka jin Maman ta tarasu sai ƴan uwanta wanda yanzu Nasir ya gama wadata su dayawa daga cikin matasan yabasu aikin yi wasu a america wasu anan nigeria su Mommy sunga kar ramawa awajen wadan ba addinin su daya ba kwanan su ukku ƴan maiduguri suka wuce sai ƴan kano ma suka juyo

ƴan gidan malam Ladan sunkawo wa Nasir ziyara Nasir sai tambayar ina Sady yake Ummu tace da yamma zasu zo ita da Zurfa'u
Chapter 83 · 0% Book details