← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 100

Sashe 41

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya k'arashe maganan yana shegewa tare da rufo k'ofan
Nasir kwantar da kansa yayi yana karanto inna'lillahi dan haka kawai yaji gaban sa yana mugun faduwan da bai san dalili ba
wayan sane yayi Rig a sanyayi ya jayo acikin a'ljushun a kasalance
yace
"Shateema ya akayi".
cikin kuka shatima yace
"Yallabai Aiban Aiban ya mu tu.....
azabure Nasir ya tashi "me what kace me".
"Sir saide muyi hakuri wllh duk wani kwaje kwaje anyi har yanzu bamu gano meye mussababin mutuwar tasa ba ni ya ai'kani airport ina masa cuku cukun tafiya kawai sai Akkram ya kirani yana kuka wai yallabai Aiban ya mutu wllh klau muka rabu dashi....
"k'arya kake shatima Aiban dinmu ba yanzu zai mutum ba...
Agrif jin sunbatun Nasir yasa shi fitowa da sauri Nasir sakin wayan yayi ya zube a bak'in gagon tare da mek'e kafafuwa Yana cewa "! Allahuma gafurni'walhamni".
Agrif yace" Nasir da gaske ne inna'lillahi'wa'ain'na'ilaishirajju Ummu Ummu Ummu ya Ummu zatayi yau me kunnuwa ki zasu ji......
Humairah ce tashigo da gudu ya Agrif Dan Allah kazo dan Allah kazo ka hana ya Kamal wai kuka yake ance masa ya Aiban ya rasu Dan Allah ai bazai rasu yanzu ba ko? Dan Allah kazo ka hanashi kar Ummu taji". ta k'arashe maganan tana fad'awa jikin Agrif din
cikin k'an'k'anin lokacin mutuwar Aiban yagama ras'a iyalan three brother kowa kaga abin tausayi ba me lallashin wani Allah sarki Izza masoyi ya tafi sai cikin dare aka samu daman isowa da gawan Aiban dan haka tsutura sai washe garin Nasir komai nashi ya tsaya cak yazama kalan tausayi dan Aiban yana da babban mushin manci a cigaban duk company sa shi Aiban mutum mai Amana da aiki da zuciya daya duk yafisu horuwa a aiki
aran da akayi sadaka bakwai aranan Nasir yasamu Agrif har cikin d'akin sa ahankali yake takawa hannun sa zube cikin aljuhon wadon sa fuskan sa tattare da damuwa ya k'araso kujera yaja ya zauna suna facing juna da Agrif da ya zuba uban tagumi Yana tunanin dan uwan sa Aiban me damuwa da damuwar kowa Sarai yasan Izza ba zabin sa bane amma yana cewa ya aure ta dan yasamu shi ya auri Nasrim ya karbi abin da hannu bibbiyu goge guntun hawayen da yazubo masa yayi ya dago yana kallon Nasir da yazuba masa Ido
Nasir numfashi ya sauke yace am sorry my brother munyi rashi muyi rashi ashe dama haka mutum yake lalle lokacin da Abban yarasu bamuda wayo bamu San meye rashi ba sai akan dan uwan mu yanzu shikenan yaran sa Muwadda da umdatu da Musanat duk sun zama marayu Allah kamamu ikon rik'e su da amana insha Allah inde Ina raye yaran Aiban bazasuyi maraici ba Aiban ya bautu a gidan nan".
ya k'arashe maganan yana dauke guntun hawayen da yazubo masa
Agrif yace" mutane masu yawa ne suka mutu a wannan yammacin mu ma da Allah ya jin k'ir ta mana Allah yasa muyi abubun da zai zama fujjan da zai sa daman mu zai rinjayi hagun mu duk Wanda akace daman sa tarinjayi hagun sa to shine mafi girman dacewa
Allah ka gafurta mana".

gyad'a kai Nasir yayi yace
"Agrif mutuwan nan yagama sanyaya min jiki Agrif yanzu Agrif yazamuyi dasu Fayyat da k'addaran su yazo da haka Agrif na tsani abin dana aikata tun randa naji labarin cikin Nasrim na tsani ZINA yanzu idan da NI NE na mutu mezan gayawa ubangijina dan Allah Agrif kayarda musanar da iyayen mu 3 brother yarana ne nasan duniya zata zageni zagin da za'a min shi zai rage min wani zububin sannan ko bakomai yaran idan sukasan nine uban su zasu yafenin tunkafin mubud'i Ido mugan mu agaban ubangiji".

Agrif yace" hakan bazai yuwu ba saboda kare mutuci gidan mu da rayuwan Nasrim idan Nasrim taji wannan abun ni kaina sai ta tsane ne sannan idan mukace su Khafulan mazane zasu iya jurewa rayuwa duk ta inda yazo musu ita Zainab macce ce ito abin zaifi damu kuma zai shafi rayuwar ta sosai".

Ido Nasir ya zaro cikin sanyi murya yace"
wai kana nufin ka yarda Zainab ma y'ata ce wllh ni rabona da nasa Nasrim a idona tun washe garin haifuwar 3bro Zainab yar kace halaliyar ka abin da yasa da ka tambayeni na amsa maga da eh wllh saboda ina son kaje kayi ta kuntatawa Nasrim ne amma wllh Zainab ba y'ata bace na gayama natsani Zina tun ran da na san Ina da d'an shege".
Murmushi Agrif yayi yace' kadena kiransu y'ay'an shegu sud'in y'ay'an k'addaran ne Allah yariga ya k'addara rabon ka ne a farkon nawa
da Allah bai k'addaran ba baza ka samu daman hakan ba kuma Al'hamdulillah Allah ya rufa asiri".
"Agrif kana nufin ka yafemin duk abinda namaka ".
shiru Agrif yayi can yace "na yafe dan nima ina son Allah ya yafemin amma sai ka dage wajen neman yafiyar ubangiji
"Agrif Ina neman yafiyar ubangiji amma bazan iya hakura da yara na ba kome zai faru nide na maka alk'awarin na rabu da matar ka amma yara dole koma me zai faru za a ban su".
Agrif yace" hakan ma bazai faru ba ai kai baka gudun abin kunya ne".
mek'ewa Nasir yayi tsaye cikin b'acin rai yace" Haruna bana gudun duk wani abinda mutum zaice ai nafi son ma a zageni".
Agrif yace "to ni Ina gudun abin kunya dan haka yara anan duniya de yarana ne alashira su tashi da sunan ka".
"Agrif baka isaba wllh ka kwace min dama biyu lokaci daya mata da yara".
Dariya Agrif yayi yace "anzu wajen dama ai najima da sanin son Nasrim ka ke wawanci ya hana da mallakan ta a lokacin da na baka dama kak'i AMFANIN dashi da ka aure".

Kallon sama da k'asa Nasir ya masa yace " Haruna inda Ina ra ayin hakan tun farko baka same taba amma kasani a kwai gagarunin rikici akan yaran na ka ba yanzu ba".
shima Agrif cikin b'acin rai yace"saide duk rikicin da za ayi ayi ni ma ina son yaran bazan bada ba".
Nasir yace
"Ok shikenan".
tare da juyawa yafice Agrif zubewa k'asa yana furta Al'hamdullah Allah ka fitar ni a duhun da nake son fita Zainab y'ata ce

*******************
" Izza cikin kuka tace "Baba dama abinda kace kana hangowa mune zamu fad'a ciki Baba bokan cinka bayyi min amfanin komai ba gashi nice na tashi amatsayin bazawara yanzu shikenan idan nagama tagaba maza zasu dinga fito min ace nayi aure nabar gidan 3 brother".
"Ke dakata IZZA kina abu kamar ba jini na ba tabbas banyi aikin bokanci akan kowa agidan nan ba saboda na hanko abinda yafi karfin tsafina amma awai rigima Sosai kozuwa gaba ne dan daren jiya ma sai da nayi duba kin tuna tun gafin kuyi aure da Aiban nace miki Ina mamakin gani akwai aure tsakanin ki da Aiban sannan akai a tsakan ki da Agrif amma na Aiban yafi al'kairi to jiya ma duban da nayi tabbas akwai maganan aure tsakanin ki da Agrif amma gaban abin kuma rikici ne amma bansan dalilin rikin ba zanci gaba da dubawa na tabbatar bai shafemu ba mutanen gidan ne fa masu shegen sadaka da kyauta duk wani masifa yana zuwa musu da sauki".
dariya Izza tayi tace'' Baba kace akwai maganan aure tsakanin na da Agrif amma idan hakan ta faru zanfi kowa jin dad'i wallashi Agrif yafi Aiban iya soyayya kaga yanda yake yiwa Nasrim ne wllh dama Nasrim haushi take bani iko da gadaranta yayi yawa komai fa itace kan gaba agidan nan daga Mama har Ummu komai saide suce Nasrim atambayi Nasrim ni Baba inaso kasa tsanan Nasrim azuciyar kowa agidan nan fiye da yanda Nasara ya tsaneta".

dariya Baban yayi yace "kai Izza lalle ke jina nace yanzu Nasrim din da itace silan zuwan mu gidan ta kanta zaki fara".
"Eh baba bari nakoma kar wannan kini bebbiyar shohuwar can ta fara nemana dan tana takuramin wai macce me tagaba bata yawa nagade takaba kwana 40 ne sauran watannin idda ne a Ina akace me idda bazatayi yawo ba tana abu kamar jashila".
ta k'arashe maganan tana mek'awa tayi gaba

akofar shiga part din Hajja suka hadu da Nasrim tana Shirin fitowa tana ganin Izza tace ''yauwa dama ke nafita nema mutumiyar tun dazu take fadan ina ki kaje".
murmushi Izza tayi tace'' wllh naje wajen Baba ne kinsan jiya yadan yi zazzabi".
"Ok ankai shi asbiti kuwa". Izza tace
"Ina bai je ba".

Nasrim wayan ta da zaro tayi K'iran Bala sarkin gida yana dauka yace " ran madam ya dade".
"Sarkin gidan dan Allah akira dr yaduba jikin baba Mustapha kuma dama Ina son dan Allah a dauke shi a cikin ma'aikatan gidan tunda shima yana cikin ahalin gidan nan a gyara Koda bedroom da parlou ne a part din Baba Nasuru amma yagirmi zaman cikin ma'aikata".
"Ok ranki yadade baki da damuwa".
tana kashe wayan Izza ta fad'a jikin ta tasa kuka tace'' Nasrim kin gama mana komai a duniya bamuda bakin gode miki".

*******************
*Agurguje*

*bayan shekara biyar*
Nasrim tasake haifuwa d'an ta me kaman Agrif an mai da sunan Aiban shekaran sa 3 a yanzu

a kan ALLAH wllh a wannan karan sai kafito kanuna Kai mafa kana da iko akan yaran ka haba ya komai sai yanda wani yace akan yaran mu makarantan k'asan nan duk bai isa ba sai ya d'auke min yaran da ba sufi sheka bakwai ba a duniya yakai su wani k'asan dama yanzu ma kana ganin yanda muke fama da Khafulan duk kokarin tarbiyar mu yaro kamar ba mayi baya jin magana bawan da ya isa ya hanashi ga daurin kai da iko da isa baya tsoron kowa ace afita dashi k'asashe turawa ya sake lalacewa wllh idan kaga an fitamin da yara to wllh mutuwa nayi ko zasu fita abari sai sun mallaki hankalin kansu kum......
Chapter 41 · 0% Book details