← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 100

Sashe 49

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamal ya samu daddy a parlou sa yana duba filet din wani cese me zafi da zayyi shima na lefin kisan kai ne Kamal yashigo ya zube a k'asa ya gaida shi yayi shiru daddy ture littafin gaban sa yayi yace Habubakar sadik Baban Hajja Abban Abdulsamad d'an Aisha mijin Aisha me yake damun kane duk karame ka k'ara duhu".
Kamal kamar yanajira ya fad'a jikin daddy yafashe da kuka yace "haba daddy yanzu y'ar ka zaka yankewa wannan hukuncin daddy Nasrim ba ita tayi wannan kisan ba dan Allah daddy ka ceci rayuwar y'ar uwa ta ita daya gareni".
shiru daddy yayi can yacire farin gilas din idon sa ya janye Kamal daga jikin sa ya dafa kafadun sa biyu yace Kamal nake yanke hukunci akan y'ay'an wasu ma balle y'ata da tayi abin agida nasan komai ai alkalanci agida ake farashi ba kana hawa Media ba ai kana ganin abinda mutane suke fad'a ko inda nabawa Nasrim gaskiya me duniya zata cemin wannan abin fa duk duniya yanzu zancen da ake kenan kasani".

cikin kuka Kamal yace'' to Daddy akan wasu mutanen duniya za kayiwa y'ar haka a koreka a aikin mana saime da de ace k'arasa y'ar ka".
"to Kamaluddeen Allah yawuce mana gaba amma idan ba Nasrim bace tayi kisan waye yayi ? Kai ne makotan su ko dawani Wanda kake zargi ".

"ni daddy bana zargin kowa amma dan Allah asake bincika wa kuma daddy dan Allah Ina neman alfarman amaida auren ka da mommy".
Daddy ya kalli Kamal yace "ikon Allah wai Kamal meye damuwar ka da auren nan neka kafa matsa da yawa".
"Daddy dole na damu ganin halinda mommy take ciki yaka mata ace an sassauta mata tawani fannin bawai a gujeta ba".

"Ok Kamal ba agaban ga mahaifiya ta tabani umarnin na sake ta ba kuma kaga tace na maida tane itama Fanna ai bata kyauta ba bakaji FURUCIN da tayiwa Hajja ba wai Hajja zataga aikin tubebbiya".
"
Kamal yace amma Daddy dan Allah kayi hakuri ka maida ta".
cikin k'osawa da maganan daddy yace Kamal bazan maida Fanna ba bani ba ita har abadan....
cikin wani irin razana Kamal yace "inna'lillahi daddy komai ya tashi kenan......
shiru yayi bai k'arasa ba".
cikin mamaki daddy yace meye ya tashi".?
cikin in Ina Kamal yace "ammm ummm Daddy sa santon da nake son nayi".
"Ok bahali bazan iya bai da taba".
Kamal gaban Hajja yaje yazube yana kukan a maida auren daddy da mommy
Hajja tace'' niko yaron nan ko uwar ka Aisha aka saka bakin abinda zakayi kenan nake ganin kamar duk damuwar gidan nan bai dameka kamar mutuwar auren kishiyar uwar ka ba kajini da yaro da jaraba kode kwadayin dukiyar ta kake saboda idan ta mutu uban kane mijin ta shi zai gajeta kai kuma magajin uban ka ko shiyasa ka damu a maida auren ko".?
"Subbahanallah Hajja wannan din wane irin magana ne Allah ya sauwake mommy tafi haka a guna ita ma uwace ke sai ana maganan arzik'i ki ballo topic na wargaza kwakwalwa".
ya k'arasa maganan yana mek'ewa tsaye
Hajja ta harari bayan sa tace'' ka kawo min wani maganan banza wata tubebbiya ai ni ce dai dai da ita har ta zauna tana FURUCIN zanga aikin tubebbiya ai saide naga al'kairi ni dinnan Ina nan har sai naga jikojin NASURUDDEEN nawa ikon Allah Nasara me wuyan fadanci ".
ta k'arashe maganan tana cewa wai Zaliha ina abincin nawa ki kawo min nan tunda gida de a hargitse yake kowa gaban sa kawo min nan duk dama abincin ba shiga yake ba."

Izza cikin takunta na isa take takawa zata wuce ta compound din Humairah
Humairah tana zaune nata chat ta d'ago kanta ta kalli Izza tace'' ke Izza zo nan".
murmushi Izza tayi tana maimaita zonan "wannan Kira haka Hajiya Humairah sai kace a secondary kin samu Junior's ko irin kin samu girls house din nan to gani".
Humairah ajire wayan ta tayi a akan kujeran da ta tashi ta jefa idonta cikin na Izza tace'' Izza me tsakanin ki da Ya kamal jiya da yau na ganku atare".?
murmushi Izza tayi tace'' idan macce ta cika macce bata damuwa dan an rab'i mijin ta
Dariya tayi taciga da cewa'' Ko da yake da gaskiyar ki macce kamar ni dole ko wacce maccen taji tsoron na rab'i mijin ta".
Humairah tace'' ke jaka akuya karya dabba annoba aike anno bace ba wanda zai so ki rabeshi kin wari Yayana ya mutu anyi maganan auren ki da Yayana shima ya mutu yanzu na ganki da mijina dole nayi magana saboda ke guba ce".
murmushi Izza ta sakeyi tana juya Ido tace'' wata kila ba rabon a jikin su saide ai maza ba k'arewa sukayi ba a gidan nan kuma ba mijin yarinya ba ko uban yarinya badan na auri d'an sa ba aure tsanani na dashi ba da nayi wuf dashi dan ni bana sake kuma bana wasa da DAMA TA .......

Wani irin uban asher Humairah ta lalo ta maka tace'' kutuma lalle yarinya a wanan Karan zaki taffa kurkure wllh abinda Nasrim tayi kadan ne akan abinda ni zanyi surprise wllh wllh abin ba zayyi kyau ba".
"Ok Humairah kema kisan zakiyi nikuma na miki alk'awarin insha Allah nice zanyi surprise dinki".

Humairah tace '' haka ki kace to wllh zaki gani".
"Al'kairin zan gani dangin ma kisa wllh saide kuyi ta kashe kan ku wahalalu
ba abinda ya shafeni ni de Wanda yace Yana sona to tilas aganmu tilar abarmu Koda za ace ransa fansa ne inji masoya
tayi maganan tana juyawa tayi
hanyar part din Baban ta

"Ai Baba nasake danno wani born din fa ga Humairah can na barta tana hauka akan wai ta gan ni da Kamal"..

dariya sosai Baban yayi yace " me nagaya miki ai nace duk mutuwa zasuyi mu ka dai ne zamu rayu sai yaranki Muwadda da umdatu da Musanat su zasu gaji tulin dukiyar 3AFULL".
Izza tace Baba wllh naga alama kaga fa Humairah yanzu tayi FURUCIN zatayi abin yafi na
Nasrim gashima nayi mata Recorder a waya ta dan zan dinga tun zurata har sai ta fusata tayi FURUCIN da zai mata illah a rayuwa nikuma ina tara bayanan cikin wayata
haka mommy tayiwa Hajja Furucin zataga aikin tubebbiya da Hajja bata daukin abinda mushimmanci ba ni na zugata nace wannan FURUCIN NA mommy bashida kyau aiko ta dauka ta hau kai ta zauna daram yanzu tace ko ciwon Kai tayi mommy ce".

dariya Baban Izza yasake yi yace aikin ki yana tafiya dai-dai ya'r Cuna anan kuma wai Mustapha ni ban ma San inda na samo wani Mustapha ba yanzu abinda nake so dake kije ki min binciken ya Dr Fanna take ciki shiru banajin labarin ta".
Izza tace Baba ai wllh wannan Fannan bata da lafiya ni ko duba ba banje ba rabona da ita tun a kotu Ina jin kunyar hada Ido da ita ayanda na dage sai da mukayi nasaran nan kasan fa duk nafi sauran lauyoyi dagewa."
b'ata rai Baban Izza yayi yace kina y'ar Cuna kike jin kunya wuce ki tafi kizo ki bani labari Koda zuwa dare ne".

Izza zubewa tayi agaban "mommy anwuni lafiya dazu naji Barira dace bakida lafiya yajikin".
cikin dauriya da kawar da komai bayabo ba fallasa mommy tace'' lafiya Al'hamdulillah Umman Muwadda yasu Musanat yau basu zo mun gaisa ba".
"Wllh mommy nima yau ban gansu ba da safe ance Ya Abbaty yafita dasu yanzu kuma inaga sun wuce islamiya ne".
gyad'a kai mommy tayi tare da cewa
"Ok madallah."
shiru mommy tayi ita ma Izza haka can Izza tace "mommy dan Allah kiyi hakuri akan abin da yafaru wllh naso ni nazama lawyer me kare Nasrim y'ar uwa ta wanda tamin dukkan halaci arayuwa to abinne wllh yafi karfina anbiyo ta inda a kafi k'arfina ne bayan da zanyi amma dan Allah mom......
"Please Izza wacece y'ar uwar ta ki ai Nasrim ban santa da wata y'ar uwa mafi kusa ba sai Humairah kuma Al'hamdulillah Humairah ma lawyer ce amma bata ce zatayi ba wanda ya dauke ki yasan zaki iyane kare Nasrim kuma dan bakiyi me yene Nasrim uban da ya haifeta ne ya yanke mata hukuncin balle ke da bama kece babban lawyer ba temakawa kikayi so bana son k'ananun magan ganu mu barwa Allah ikon sa zaki iya tafiya nagod........
Mommy bata k'arasa zancen ba Zaliha me aikin Hajja ta shigo arikice cikin in nina tace'' mommy mommy Hajja zata mutu".
Mommy tace'' meya sameta tana cin abinci kawai sai tace cikin yana ciwo bakin ta kumfa yafara fitowa yanzu ma asbiti za akai ta".
Izza tace" wayyo Hajja gatana nashiga ukku....
tayi maganan tana ficewa da gudu
Mommy ma tabi bayan ta kafin su k'arasa har Kamal da Ummu sun shiga motar mommy taja
Izza ta hau nata motan ko mayafi babu ta fita a guje arikice mommy da Mama Adamu driven mommy ya dauke su
Asbiti
duk suyin cuku cuku a kan Hajja har Nasir da Abu da daddy
Daddy ya numfasa yace " kamar yanda Dr yamana bayani Hajja guba taci to a gida an bincika wanda yasa a bata a bincin kuma an gani ta hanyar CV tv muje gidan munafiki ya bayyana ita kuma Hajja Allah yabata lafiya Al'hamdulillah Allah ya yafiyar mu cikin wannan duhu da muka shiga asiri ya tonu mujede gidan tukun".
Mommy zubewa tayi a k'asa tana sujjidan shuran cikin kuka tace'' Alhamdulillah Allah na gode maka da kafitar mu a duhu Nasrim zata yiwa mijin takaba a gida".
Chapter 49 · 0% Book details