← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 100

Sashe 76

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani godon ajiyar zuciya ya sauƙe yace *YA ALLAH KAGA YANDA NACI BURIN ZUWA WAJEN FAMILYN MAHAIFIYA TA AMMA GASHI YAU ANTAFI BABU NI MOMMY YAUSHE ZAKI GANE GASKIYA KI SO GANI NA KI NE MENI ILOVE MY MOMMY*

ya ƙarashe maganan yanayin fuskan sa ya mugun canzawa ba ƙaramin missing din Mommyn nasa yayi ba

*Mai duguri Barno birnin shehu*

a gurguje

su Mommy sun sauƙa a cikin garin Alhadulillah Baba Nasuru ya samu dangi wanda suka rage wasu kuma Allah ya musu rasuwa akwai dan uwansa daya ADAMU ƙanan sane yayun sa duk sun rasu sai yaran sa da sauran dangi matar Fanna tanan da ranta yaran Bana shima yana mata biyu da yara sunka shashida Mala yayan Mommy matar daya da yara tara cikin yaran Mala abin mamaki harda zuhura yariyan da suka danyi sabo da Nasir har Mommy ta kecewa ya aure ta Girema ne bayanan yana lagos amma an ƙirashi yace gashinan zuwa aranan Mommy tayi mugun tausayawa dangin nata duk baza aƙirasu talaka ba amma de baza ace masu kuɗi ne sosai ba ashe Zuhura ma scholarship ta samu tafita DUBAI din karatu har suka hadu da Nasir din Mala principal ne nawani makarantan Secondary na mata sai Bana da shima de aikin gomnati yake bawani babban ma aikaci bane shima Girama ɗan kasuwa ne a lagos
Mommy sun sha kuka sosai duk suna zaune bayan cin abinci dare sai fira suke yara suka fara shigowa da kaya suna ihun ga Babakura ga Babakura

Girema shi ya shigo da saurin sa MOMMY ta miƙe tace SHARIF!!!!!!!

shima Girema yace Fanna!!!!??

Mommy tace" Sharif dama baka mutu ba ? .

ban mutu ba Fanna kece ƙanwata Fanna."?
itama nunasa tayi tace "kaine Yayana Girema da muke jiran zuwan ka

Baba Nasuru da su Hajjja sun nemi sanin me yake faruwa fanin Mommy ta fadi tana ta kuka Girema yace Fanna budurwa tace munkai kusan shekara 8 muna tare ni narabo ta daga cikin danginta na kawota mai duguri tayi karatu daganan na nema mata aiki akano amma sai da nasaka ranan auren mu da ita yarage sati ɗaya tak na aika mata da soƙon nayi hatsari na mutu sabo na fasa auren tane dalilin dogon nazari da nayi na ganin Baban mu yayi aure a lagos ya ƙimu ya watsar mu naji tsoron na auri ita Fanna ashe Allah yaso mu da rahama da ya zamuyi idan muka auri juna nida ƴar uwa ta Alhamdulila Allah mun gode maka da baka bari munyi wannan ƙazantaccen auren ba daga baya ina bibiyar fanna sosai ko da mijinta ya rasu naso naje amma naji tsoron yanda zata fassara abin da namata dan dama can ni zuciyata bai amince da auren fanna ba shiyasa ko sunana na gaskiya ban gaya mata ba kawai de ina son in rabata da addinin da take cikine".

Baba Nasuru yace Girema ku yafemin daga nan shima ya kwashe abin da yafaru dashi ya gaya musu

Hajja tace" ai dama shiyasa akeson bincike a aure Annabin Allah yace bincike a aure ya halasta".

su Mammy sun zaga dangi sosai kuma anata zuwa musu ka dauko kwana hudu sai da sukayi sati guda har Hajja aka zauna dan itama tace garin yamata daɗi sosai Dddy da Abbaty ne suka koma washe gari

aranan da zasu zo da kuka suka rabu shiko Baba yace ba komawa har yasa an baida masa auren sa da matar sa
su Baba an zama ango yasha tsokana ko awajen jikoki

Nasrim washe garin zuwan tafito da shirin ta sai gidan Ta soro nesa da gidan tayi parking ta fito a ƙafa ta taka knocking tayi yazo yana ganin ta
ya saki murmushi yace" lokaci yayi".?

bata masa magana ba sai murmushi da take jifan sa dashi tafara murda murfin kwalban da yake hannun ta
ta jefar da murfin still de tana jin sa da murmushi tace " da kunnen ka da idon ka zaɓi wanda zan rabaka dashi yanzu".
yayi murmushi cikin izzar sa ya tsaya a gabanta ƙyam yace "wannan zaɓin kine wanda baƙya so zaki zubawa".
tsayawa tayi tana kalon gefe da gefen alaman bata son wani ya ganta

idon sa a rufe yace " amma ko duk kina sone ba wanda baƙya so daga idon har kunnen duk kina so

cikin wani irin ƙarfin gwaiwa ta ɗaga kwalban ..................

*sis muhadu a pg 28 dan jin me zai faru da nasir NA GODE SOSAI DA COMMENT DINKU ALLAH YABAR KAUNA*

ƁJ

[4/8, 1:49 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*28*

hannun ta ne ya fara wani irin rawa cikin ƙarfafa zuciyar ta ta sake yunƙurin ɗaga hanun ta a garo na ukku kawai sai taji kamar an ƙame mata hannu akaro na hudu ne kawai ta cilla kwalban gefin su atake interlock din wajen yafara mani irin ta fasa sosai yana mamaya

Nasir da bai rufe idon gaba ɗaya ba yana kallon ta ya saki wani irin murmushi ya mai da idon sa kan kwalban acid din a hankali ya bude idon sa akan ta
yace "ok ko ina kina so bazaki iya illata su ba".

Nasrim cikin kakkau sar muryar tace "lokaci ne bayyi ba nafison ka sake ɗan ɗanan azabar duniya a yanda ka taso da taƙama da mulki
ko mai ma ƴan iskan matan kane suke shafa maka komai yi maka ake yau gashi kai ne a matsayin mai gadin gidan wasu wanda basu wuce ma aikatan ka adaba haka ma ya ishaka amma kar kacire rai da gani na ukku zakaga abin mamaki wannan FURUCINA NE."

ta ƙarashe maganan tana juyawa saida tayi taku ukku yasa hannu ya juyo da ita

yace " haka ne ina son macce tamin komai ni na mata ne kin gane mata sune matakin Nasara a rayu ina son ganin macce ce take bauta min kar ki cire tsammanin watara koke ma zaki iya zama baiwa ta har na hango irin azabar da zan baki kin sani bana daukan nonsense sai kinyi nadaman wannan kallan naki na ƴan iskan mata sai kin zama ƴar iskar Nasir
saboda Nasir baya man tuwa baya daukan abu da sauƙi baya yafiya wllh sai na bauta ki sai kin lashe kashin na sai kin min bautan da ba maccen da tamin a rayuwa"..
ya ƙarashe maganan tare da komawa Nasir din sa na ai nishi
ya saki hannun ta
da karfi yanda za ta iya faduwa ƙasa
ya juya ya shige ciki
Nasrim tayi control din kan ta bata kai ,ƙasa ba tsabar baƙin ciki ji take wani abu ya tokare mata a ƙawon zuciyar ta gudun kar ya tada mata ciwon ta kifa kanta a jikin mota ta saki kuka harda kwallawa da karfi da Allah ya temake ta layin ba kowa taci kukan ta buɗe mota ta shiga anan ma kukan tayi mai ƙara sosai ya
ta dan ji sauƙin zuciyar ta kuwa
cikin shakekƙiyar murya tace ```waye shi waye NASIR mutum ne shi kuwa meyasa duk burina akan sa idan nazo gaban sa nake zama wata wawuya meyasa yake min mugun ƙwarjini wllh wllh sai na dauki mata ki akan sa```

a fusace ta shigo ba tare da ta tsaya gaida Mommy da DR Hafsa da suke zaune ba ta haye sama cikin ɓacin rai

DR Hafsa ta kallin Mommy tace "wai dr har yanzu yarinyar nan bata ware bane anya kina bata ruwan adduar nan na dangana kuwa".
"ina kuwa wannan uwar taurin kance zata sha miki ruwan adduar ko kallon inda yake batayi ba amma kwana biyu ta dan ware wai ta samu wata Ta soro ko watake tsohowar mai shegen surutu ranan da tazo gidan nan ta kafa shegen surutu da ga ƙarshe de danaga naga tafiyar su zai zo daya da Hajja na turata wajen ta sun ko jone sosai da Hajja ita ma Hajja naji tana cewa idan ta ware gajiyar hanya zataje mata ni danace zanje Nasrim hanani tayi kuma da ita take bin bayana naje naje nake ƙi inaga ko zuciya tayi wayasan mata kinsan Nasrim da saurin hawa".
Dr Hafsa tace " ummm to zamu nemi gidan sohuwar muje inde tayi aiki a Fada ai barr Fa'at zai santa tunda gidan sune sai mu bincika muje ai wanda yaso naka ka soshi bari naje naji yanzu meyake damunta".
ta ƙarashe maganan tana meƙewa ta haye step

Nasrim tana shiga tayi cilli da takalmin ta da jakar ta
ta fara rusa uban ihu nata cewa
```YA ZANYI MAI ZAN MAKA NA HUCE KA CUCENI CITA TA HAR ABADA KA ƁATA RAYUWATA KACIMMA BURIN KA NA CEWA DADDARATA BA MAI KYAU BANE YAZANYI YA ZANYI WAYE ZAI SONI AHAKA IDAN BA AGRIF BANE ZAI ZO DUNIYA``` ...

girgiza kai tayi da sauri tace
```BAZAN SAKE AURE BA KO SHI AGRIF INDA ZAI ZO DUNIYA BA ZAN SAKE ZAMA DASHI BA MACI AMANA NE A WAJENA DAN ME YA ƁOYE WANNAN BABBAN TA'ƊIN DA BAƘIN KAFURI YAMIN AZZALUMI WLLH KAI MA DUNIYAR KA BA ZATAYI KYAU BA ZAN NUNA MAKA SHERRIN MACCE YAFI NA MAZA GIRMA SAI NA NUNA MAKA MU MATA SHEƊAN MA SARA MANA YAKE WANNAN FURUCINA NE```
Chapter 76 · 0% Book details