← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 100

Sashe 98

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nasir ya kalli Agrif yace "bro kafa bar ƴar mutane ya kamata kaje,
kaga ni Nana wai tana jego komeye wani jego Hajja ta haɗani da Mommy ta hanani shiga ɗakin da take ma".

numfashi Agrif ya sauke yace " bros nayi missing dinkane sosai nasan my dear zatamin uzzuri ai tasan muna tare".
Nasir yayi murmushi yace " kai kana yabon wannan matar taka kuma da alaman tana mugun kulamin da kai bro gashi kayi kyau kayi ƙiba fresh dakai".

numfashi Agrif ya sauƙe yace "sosai Izza ƴar aljana ce yanzu na san nayi aure duk namijin da yake son ya morewa rayuwa to ya aure matar da sonta yafi nasa anan ne zaiga tattali nifa yanzu ko sarki saide yanuna min nauyin rawani babu ta inda ta gaza Allah yamin baiwa da mafificin baiwa da ya hadani da Izza Izza she's good komai nata nice nasan bazan taba nadaman samunta amatsayin mata ba".

Nasir yace "kaga nikam duk ta yanda taga dama takeyi dani juyani ake sosai nikuma idan na fito na rama akan ma'aikata".

dariya Agrif yayi yana dukan kafaɗan Nasir yace" ah nasan ka fa ai bazaka juyu ba duk da nasan soyayya ce take tafiyar da rayuwarka ɗan loop"

Agrif yace yawwa bro ni kana kula da harkan companyn Kamal kuwa Abbaty de yace a'iki yamasa yawa baisan halinda ake ciki game da company ledan saba amma wasu plaza din sa yace komai normal ko".
"Eh ina bincikene akan company gaskiya manager din ba mutumin kirki babe yana son kashe masa company amma gobe de zan gama dukkan binciken a canza manager din".

sunsha fira yanda yakamata duk da tattauna war tasu akan business ne
sai kusan 2 na dare yafito daga Part din Nasir din

Izza har ta gaji da jira tayi bacci Suhal ne ya tashi ya fara kuka daukan sa tayi tana shirin sashi a nono ya shigo cikin sallamar sa da ya tsaya a iya leben sa direct bathroom ya wuce ba tare da yakalli inda take ma bajimawa ya fito daure da towel ɗaya a ƙugun sa ɗaya yana goge jiki dashi ya wuce inda mirror sama sama ya murza lotion a jikin sa tare da fesa turare ya ware ido yana kallon yanda ɗakin yasha gyara kamar ba shiba gaba daya part din ma yabashi mamakin yanda aka canza masa fasali murmushi yayi yace "ni Haruna ɗan gatan Mommy ne nasan wannan aikin sai ke Allah yabar manake yace tareda meƙewa yasaka kayan baccin sa
ahankali ya sunkuya ya sakarwa lil Aiban da yake cikin gadon sa agefin nasu kiss yashafa kan Suhal da yake cinyar Izza ya hau gadon tare da gyara pillown sa ya shafa addua ya kwanta tareda jan bargo

ahankali ta kwantar da yaron akan gadon sa ta sauƙo daga gadon ta zaga gefin sa ta gurƙusa tare da jan barkon cikin rawar murya
tace "mijina yau ni kajuyawa baya kasanar dani lefina kamin hukunci daidai da lefina kar ka zabi azaf tar dani ta wannan ɓan gare bazan iya jurewa ba".

kallon ta yayi ido cikin ido yace
"Izza kina son kifara taurin kai ko".

hawaye ne ya zubowa Izza yarrr bazato tace "subbahalallashi ni ni taurin kai Abban Zeenat menayi".

cikin daure fuska yace " tun yaushe nake miki maganan gyara mu'amullar ki da Halima amma kikace sai munzu gida gashi munzu ina gani ko kallon inda take bakiyi ba Nasrim bata daga cikin jerin matan da zakiyi kishi dasu ita din ƴar kuwa tace jini na kuma bazan gaji da gaya miki arziƙin ta kike c............

da sauri ta rufe masa baki da tafin gannunta tana girgiza masa kai ga hawaye na surto mata
"my habibi baka fassara ni dai-dai ba ni na isa nayi kishi da Nasrim albarkacin ta fana keci wllh wllh Ya Agrif ko kai bazaka gayamin son Nasrin ba Nasrim itace ta inganta rayuwa ta adaliln ta muka shigo cikin gidan nan ita tazamar ni mutum wllh kunyar ta ne ya hana na mata magana ina mutuƙar jin kunyarta ne kuma tana min ƙwarjini sosai kuma kai ma kasha cewa Nasrim tana da ƙwarjini so dayawa Hajja da kanta tana cewa anya Nasrim da Nasir ba sha shatau suke shaba suna da ƙwarjini sosai ni bansan ta inda zanyi controlling kaina a gaban ta ba amma tunda umarnin mijina ne ko zan mutu sai naje na gana da ita awannan tsohon dare ba sai gobe ba.....

ta ƙarashe maganan tare da meƙewa a zabure

wani irin fisgota yayi ta faɗa jikin sa ya birkito da ita tayi ƙasa shi kuma a sama ya sakar mata nauyin sa gaba daya yakai bakin sa daf da nata numfashin su yana fita atare murya can cikin maƙoshi
yace " MAR'ATUSSALIHA kinsan meye sirrin ƙwarjinin N'N".?

girgiza kai tayi tareda rolling da idon ta

yace" sirrin shine falalar salatin Annabi Nasir a kullum yana salati sau dubu arana kin gade duk yawan aikin sa ayanda yake dinnan to bayan ko wacce sallah sai yayi salati so dari biyu istigfari dari kinga idan aka hada na sallah biyar zai bada salatin dubu istigfari dari biyar wannnan ƙa idar Nasir ne sai dana zauna da Nasrim naga itama tanayi kinga nima awajen su na zara wannan shine sirrin su kema ki gwada zakiga abin mamaki".

Izza tace "kwarai kuwa haka Nasrim take duk busy din da zata shifa sai tayi su koda zata bar sauran zazkar din ta kuma wllh sakacine amma tare Mommy ta koya mana wannan tarbiyar Mommy ne Allah yasaka mata da mafificin Alkairi".
ta ƙarashi maganan tare da ƙarasa manna bakin ta kan nasa

*Nasir*

murmushi yayi a lokacin da ya bude dakin ya hango Hajja akan gado sai munshari take zubawa
ahankali ya tako har bakin katifar tsayawa yayi kallon ta yanda take baccin ta cikin kwanciyar hankali ta rungumo Baby Ni'mra ahankali ya jaye Baby tareda daukan ta ya maidata kan gadon Hajja ya dauki pillow ya kara bayan yarinyar ya dawo ya shige jikin Nasrim cikin bacci taji kamshi sa da tattausar jikin sa wani gwuron numfashi ta sauke tareda shigewa jikin sa jin abin yafi karfin kamshi yasa Nasrim ta bude idon ta da sauri bude baki tayi zatayi magana yayi saurin daura yatsan sa akan bakin ta yana juyowa inda hajja take alama yamata da kar ta tada Hajja
ahankali ya kai bakin sa kusa da kunne ta yace" meyasa baki tsaya kin ci abinci ba kika gudu".
ahankali tace "banajin yunwa ne ".
ɗan marin kumatun ta yayi yace "Ah Ah kide fadi gaskiya ganin Agrif yasa kika tsorata kin zata za ace ki rabu da ɗan ɗanon zuman ki ko ".

"kana nufin kai baka tsorata ba Ya Rujjulussalihi na idan akace in rabu dakai ai kamar an tarwatsa rayuwatane toma tayaya impossible ni kai har abada taya zanyiwa wanda yaƙi kula wata saboda ni ya zabi yarayu ba aure duk saboda ni
taya zan maka butul ci akan wani Agrif da bai san meye soyayya ba nasan da kaine baza ka fansar wa wani niba darajata tafi haka awajen ka RUJULUSSALISHI".

girgiza mata kai yayi yace
"Nasrim gaskiya Agrif yana sonki yanada zuciya mai yau wanda ba kowane yake da shiba tabbas bazan iya kwatanta yin abinda yayi ba Nasrim Agrif ɗan Aljanna ne tun muna yara yasha hakura da abinda yakeso akaina kamar irin su abinci zabi na karatu abubuwa dayawa ya sadaukar min kinga muna yara Kamal tak yake jira nayi lefi tazo yafada amma Agrif yafini moye duk abinda ya zamana lefina ne Nasrim ni ban isa nasakawa Agrif abinda yamin arayuwa ba banida abince masa banida abin bashi sai adduar dacewa a wajen uban giji
ni sannan ina sonki ki manta da kin taba soyayyya ko zaman aure dashi ki zauna dashi amatsayin dan uwan ki nima nayarda dashi bazai cuceni ba nadauke duk wani kishina inde akan Agrif ne".

can cikin dare Hajja taji ƙafa da da hannun Baby yanata shurin ta azabure ta tashi tana ihon maciji ya haumata gado ta fara kururuwa tana cewa "dama saida nacewa Abdulrahaman yasa arage itacuwan lambun nan mucizai sun fara yawa agidan nan jiyama saida aka kashe a gidan Haruna gashi yanzu har kan gadona ke Nasrim kunnan wuta inaga muciji yasareni ma Halima ba magana nake ba kin min.............

bata ƙarasa ba Baby ta sandara kukan tsorata da ihon Hajja wani wawan numfashi Hajja ta saike
tace au ashema mai sunata ce Allah sarki takwara kece wannan sakaran uwar taki takawo ki bata sanar dani ba da nadanne ki fa".

ta ƙarashe maganan tana laluman ƴar har ta dauketa ahankali ta sauƙa tana laluman makunni wuta
Chapter 98 · 0% Book details