← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 100

Sashe 75

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

numfasawa Baba Nasuru yayi yace kamar yanda na faɗa miki ni ɗan mai duguri ne ina da mata da yara biyu maza kuma ina zuwa lagos neman kuɗi kusa da inda Emaka da mahaifiyar suke ƙosai anan nake wanki da guga da gyaran ta kalmin idan ya samu to ana cikin haka emaka ta kawomin tallan kanta ita de tana sona kinsa alokacin nayi kyau sosai duk baƙine ni ina da hanci da tsowo da dogon fuska kuma shi kuka gado halima kam ma kamar kara aka tsaga dani sai yara na na mai duguri Girema bai biyoni ba mahaifiyarsa ya biyo amma Bana ya biyoni sosai
haka Emaka tayi ta shigemin har nima naji na fara son ta amma dama tana nuna ƙyama ga addini na bata son muslumci sosai soyayya mu har tayi ƙarfin da ta kaimu ga maganan aure Emaka masifafiya ce gani kasheni bata barin iyayenta ma balle yayunta ba wanda take tsoro a familyn su sai ita ake tsoro tana juya kowa a gidan yanda takeso dan haka ba wanda ya musa mata da tace ni zata aure wani limami ne ya tara musullamai aka daura mana aure ita tayi al adan su sukasha biki ita da ƴan uwanta muka tare ita tana fita sana arta nima ina fita nawa naso naja ra'ayin ta muyi planning amma ina gaskiya Emaka tafi ƙarfina ban son haifuwa da ita saboda muddin muka haifu to zata saka min yara cikin kafurci nikuma ba abinda na tsana irin addinin christian shi yasa banso mu haifu ba amma da tagane sai tafara fadan musulmai muna fukaine ina moran jikinta amma bana son haifuwa da ita sai nafito na gaya mata ga abin da nake gudu sai tace idan hakane ba damuwa zata bani dama idan muka haifu nima na nunawa yaran addini na ita ma tanuna nada duk wanda yayi rinjaye shikenan na amince da haka tunda nasan hujjan musulmi yafi na kafiri ƙarfi nasan nine da nasara mukayi wannan alƙawari shakara daya Allah yabamu ɗa namiji na saka masa Muhammed ina ƙiransa Mala ita kuma tana ƙiransa Friday Mala yana da shekara hudu aka haifeku to gaskiya Emaka ta samu nasaran akaina akan mala saboda tanayiwa yaron wani irin so da jansa ajiki sosai ko waƙa irin na coci yakeyi duk abinda nake koya masa baya dauka ni kuma ganin bazan iya barin ɗana ya shiga hanyar ɓata ba yasa nasa aka tsacemin shi zuwa maiduguri dama ƴan uwana sun san da maganan auren kafura da nayi tunda ina yawan zuwa ganin gida
sosai na tada fitunan Emaka ta ɓatar min ɗa nida ita har wajen yan sanda akan ita ta ɓatar min ɗa tane bo sosai na tada bori hankalin Emaka ya tashi sosai da tana mugun son MALA sonda ko keda Halima banayiwa haka de mukayi ta nema har ta haƙura gani na kawar da matsalan Mala yana inda zai tashi da Addini na yasa duk hankalina kuma yakoma kan ku sosai nake janku ajiki mude bakin kuma da BISMILLAH kuka fara saboda komai zanyi sai nace bismilla idan zan ajiyeku da bismilla idan zan ɗauƙe ku idan zamuci abinci kai har ni kaina ya zame min jiki alokacin ko magana zanyi sai nace bismilla komai yara suna bude baki suma suka fara shiga banɗaki addua fitowa addua ga na siri sallolin nafila agida tunda farali a masalaci nakeyi kullum nafila sosai nayi iya kokari na lokacin shekaran ku uku Matata Fanna wanda sunan ta nasaka miki wai ta gaji ta tako tazo lagos da yaran Girema da Bana dakuma MALA ɗan wajen Emaka to fa aranan ne babban tashin hankalin ya faru ban taba tsammannin masifan Emaka yaka haka ba ashe tana ragamin saboda son da take min aranan yan aguwar ma basu samu bacci ba ta tafi ƙiran yan sanda na dauƙi matata da yaran ta da Mala nakai tasha Allah ya temaka nasamu mota saura mutum daya ina sasu nace taje dasu ni ma idan na samu na dauki Fanna da Halima zan gudo

ina zuwa gida naga ta kawo yan sanda suka tafi dani nasha azaba sosai ahannun su amma duk tambayar suka min sai nake cewa ba ɗan ta bane ɗan gidan matata ce nace kuma kama suke dani shima mala dani yake kama gani ba yanda basuyi ban faɗa ba yasa dole suka rabu dani sosai nake lalaba Emaka akan tayi kaƙuri muci gaba da zaman mu kamar da fir taƙi wai naci amanan ta ban sanar da ita ina da mata ba ni kuma lallaɓa tan da nake dama nasamu na dauke kune na gudu amma tayi mugun sa ido akan ku saboda sace mata ɗa da akayi wata rana ke ta daukeki ta tafi coci na dauki Halima muka gudu kinji iya abin da ya hadamu da ita kenan

mukuma mukayi hatsari a hanya yanzu babban abinda nake damuna yanda zan fuskanci yara na maza uku da Matata Fanna sarkin haƙuri ƴar aljanna Allah yasa ma tana raye na nemi yafiyar ta ".
Na sauke ajiyar zuciya tace " , Insha Allah zata yafe maka Baba".

washe garin ranan birthday din Abdul Nasrim ta kalli Humairan da take ta shirin fita tace " amma de ba fita zakiyi bako Humairah tana gyara rolling din mayafin ta tace "fita kuwa akwai wani case da muke dashi gobe za ayi zama wllh wani tsohon banzane yayi wata yarinyan yar shakara 9 rapping shine nake son nasamu zama da iyayen yarinyar kafin goben".
ta ƙarashe maganan tana shirin daukan jakan

Nasrim tace " amma inaga kin manta da yau ne birthday din Abdul naga bakiyi kowane shiri ba ana su Muwadda iyanzu har an fara shirin party kuma ke kika shirya a ina za ayi cake din ne nasu Muwadda yayi kyau sosai ayi a inda akayi nasu dan Allah kinsan lokacin da akayi nasu Muwadda nawa cikin sukunin dina ai".

cikin rashin damuwa Humaira tace "ba wani birthday din da za a masa yaron da uban sa yake kulle meye nashi na birthday wllh ina mugun ta kaicin haɗa jini da Kamal".

hararan ta Nasrim tayi tace " ok yanzu kenan saboda Ya Kamal ba ƙe son Abdul kenan to nifa nayi yaya da Khaflan da yake ba ɗan sunna bane".?

Humairah tace '" ai wannan ƙaddara ce."

Nasrim tace shima Ya Kamal ƙaddara ce laifin da yayi kuma da makirci irin na uwar sa idan ki ka bari lefin ya kamal ya shafi Abdul baki masa adalci ba".

da yamma sosai Nasrim ta shiryawa Abdul birthday da ya ƙayata kowa saide sunyi kukan rashi Kamal sosai rashin Kamal yake damun mutanen gidan kodan dama can shine a gida sauran ba zama suke ba
ba shaƙuwa kamar na Kamal

washe gari akayi shirin mai duguri

Nasir ne ya shigo da sallama dan ya gaida Ta soro tana waya ya sameta

"yo ai Nasurim da kin gaya min da na miki rakiya dama ina son naje naga garin ƙamshi sai jin labarin sa nake".
saurarawa tayi can tace "Allah sarki to akawo mana kayan ƙamshi sosai anjima zan ƙiraki ga balarabe yazo zamu gaisa ai rannan kina fita ba jimawa ya shigo ashe wajen Jafaru ya leƙa kinsan dama Jafarun ne yayi hanyar haɗuwar mu Jafaru mai gadin kidan Alhaji yahaya".

sai da tabari ta saurara
ta sake cewa wllh kuwa ya miki baƙin cikin ganin wannan kyan nasa koda yake ai shima yayi a saran ganin naki kyan kin san ance abincin ido ganin abu me kyau shiyasa ni ko sanda na ke FADA wllh dan dole nake ɗaga ido na kalli gimbiya Murja nafi son na kalli gimbiya Balaraba ai wata zan kai ki fadan nan ki ga gimbiya Balaraba
to to a sauƙa lafiya".
Nasir yace
"HAJIYA waki ka samu ne"?.

" da mutumiya ta mana kaji wai tana hanyan mai dugurin garin kakan nin ta amma dayake in bata ga dama ba miskilan kanta ce zuwanta shekaran jiya bata gaya min zata tafi ba ko tana min baƙin cikin naje na kwashi ƙamshine waya sani ita mata ta ibi ƙugu kamar balam balam wllh duk mai rabon da ya kwashi wannan ƴa ummm zai kwashi kayan aiki ai shiyasa Ma'aruf ya rikice wai shi sai ita shegiyar uwar wai ya zai auri bazawara a auren fari yabari ya auri FIRDAUSIN in yazo ya ƙara da ita Nasrim ita kuma da yake da ruwan hanji aka wanketa zata tsaya jiran sa tana son ta mana a saran hada jini da gidan arziki yo idan jikana ya aure ƴar gidan jiri buroda ai fasa kaina ƙaruwa zayyi zan ƙara daraja a idon mutanen fada yo yanzu ma fa sun fara cewa dama mu dan gin sune idan jikana ya auri masu kudin duniya ai ƴan uwan su zamu zama ba dangi ba yo yanzu mafa idan na shiga fada kilishina daman ita nazama sirikar tiri buroda ai jerawa zanyi da mai babban ɗaki muzauna uwar sarkin gaba ɗaya baride Alhajin Allah yazo ya samu sarki da manyan mutane suje mana tambaya kaga ni baruwana da wani baza wara ce ai ANNABIN ALLAH ma da bazawar rar data girmeshi shekaru ma yafara yo ba sunna bane ai masu farawa da zawarawa sune a gaba gaba a wajen annabi ni nayi wasa da mutanen sai de muji labarin su agari yanzu gashi munsan jina".

Nasir de murmushi yayi yana tuno kalman ta na duk wanda ya ibi Nasrim ya ibi kayan aiki
gyada kansa yayi afili kuma yace
to Hajiya kuma ita ta amince zata auri Ma'aruf din?".

"kajini da wani zance yo kai kaga Ma'aruf dinne hai ko mace bata soshi da komai ba ta soshi dan ƙyansa uwar fa bafulatana ce kasan ni yara duk bana bari su auri mummunar mace shiyasa koda Isiya da Baban gida ba suyi kuɗi ba to yaran su ƙadaran mune balle ma gashi nan sunyi ƙudin zata soshi tunda tana kulashi yanzu ma".

Nasir de ya gaji dajin surutun hajja ya tashi ya fice tana ƙorafin miskilan cin sa yayi yawa baya tsayawa suna fira wllh sai ta rake masa albashi inde ba zaina zama tana bawa idon ta abincin saba
Chapter 75 · 0% Book details