← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 100

Sashe 31

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Agrif sake matse hannun sada yake cikin na Nasir yayi cikin k'unan zuciya yace "Nasir kafi karfin komai awajena nasani shine dalilin na na barmaka NASRIM tun farka a zatona da gaske son ta kake duk da nasan bazan jure rashin taba nima amma na bar maka dan kafi karfin komai awajena ashe kai bason Nasrim kake ba nikuma ina sonta bilhakk'i bazan yarda da abin da zai cutar da ita ba dan Allah Nasir Nasrim taci darajan son da kake min kabari mu zauna lafiya".
girgiza kai Nasir yayi yace' ah ah wllh bazan iya ba Agrif bazan iya kwatan ta maka yanda zuciya ta take min barasaza a kowacce second game da Nasrim bane tayi mugun shiga yaruwata yanda bazan iya kwatan tawa ba wllh bazan taba barin ta
ta huta ba".
numfasawa Agrif yayi yace
"Nasir ka bani mamaki duk da nasan halinka duk abin da kace zakayi zakayi da kace bazaka bari nazauna lafiya ba ban zaci ta wannan hanyar zaka bullo ba duk atunani na k'untatawar taka zata tsaya a iya korata a aiki ne tunda Kai ne me campanyn amma ashe abin naka ya zarce nan Nasir ina tausayin ka aranan da zakayi nadaman abinda ka aikata kana musulmi ka aikata zina da matar aure kuma baka sirran tashi ba kanunawa wanda yake auren ta saboda ka isa kasani wllh Allah shine ishehhe Nasir wani irin zuciya Allah yabaka da baka sawa aranka akwai ranan shisabi awai randa ikon ka kudin ka baza su maka amfani ba Nasir ban zaci isar taka har takai ka dauki CC camera kasaka a d'akin aure ba har kana barazana dashi kasani mala'ikun Allah ma idan ma'aurata suka keb'e kansu juya musu baya sukeyi basa ganewa idon su tsiraicin ma'aurata Nasir me namaka ?me Nasrim tamaka? Wllh Nasir ka jefani cikin wani irin k'uci wanda ko fitar rai bana jin yafishi ciwo why".?
ya k'arashe maganan yana dafe goshin sa saboda kansa da yake masa zugin ciwo
Nasir mek'ewa yayi tsaye yana juya baya yana murmushi me dauke da b'acin rai yace
"Agrif duk yanda zaka kwatan ta zuciyar ka bata kai tawa ba wllh nafika shiga cikin k'unci
Dan Allah ka temaka kar kayi yunk'urin bawa Nasrim kowane
irin farin ciki a karo na biyu zan zo maka da buk'ata idan kabi insha Allah zaka tsira da mutumci ka idan kayi gardama irin na baya to saka makon zaifi haka muni".
cikin dauriya Agrif yace" me kake buk'ata"?.
sunkuyawa yayi cikin taushin murya yace
" Ina son ko dan yatsar ta kar ka taba har ta haifamin yaro na sannan ina son mahaifar ta yazama a tsarkake yake shine dalilin saka cc camera idan ka k'arya alk'awarin nasani".
Agrif yace
"wannan sharad'in ai nariga na dauka amma dan Allah kacire CC TV a bedroom din mu bazan kusan ceta ba sannan ba maganan na baka yaro Dan koni nabada ayanda Nasrim ta tsane ka bazata baka d'an taba sannan shara'a musulumci ta halak tamin cikin jikin Nasrim".
wani irin kallo Nasir yabi Agrif dashi ya d'aga kafada yace' ai dama Kai zumane sai da wuta to wllh ni dakai zanga me nasara zan tona asiri komai ma yafaru ba uban kowa zanji kunya ko tsoro ba".
shima Agrif cikin b'acin rai yace "amma ai na yarda da sharad'in kana farko bazan hada shimfida da ita ba dan haka kamin uzurin ta haifun idan ta amince zata maka shikenan amma da sunan ni zan maka kyautan sa dan Allah idan kana kaunar iyayen ka kar ka fallasa zaka zubar da mutumcin gidan mu hakan babban abin kuyane zaka janyowa three brother abin fad'a aduniya kasani gidan mu shaharatren gidane aduniya ".
cikin rashin damuwa yace
"ni duk wannan bai dame ni ba na tsabawa mahaliccina ma balle wani abu da wani bawa me zunubi aka zai fada akai na ba wannan ne damuwa taba damuwa ta ka kula da sharadina kawai".

Agrif yace"shikenan naji zan kiyaye amma dan Allah ina son na d'an kwanta na huta".
murmushi Nasir yayi ya nufi kofa atunanin Agrif fita zayyi sai yaga yasakawa kofar key kuma yazare ya jefa acikin aljihun sa ya tako yana murmushi ya fada bed din yana jan blanket yace "good night".
ba aja dogon lokaci ba bacci ya dauke Nasir
Juyowa Agrif yayi Yana kallon fuskan Nasir afili ya furta "anya ko Nasir kai mutum ne kana nufin kwana zakayi a part din mu wannan wacce iri yar rayuwa ce"?

tashi yayi yafara safada marwa a d'akin ba abinda yake tunawa irin Nasrim tabbas yaga sha'awar kasance wa dashi acikin idon ta mezai ce mata bai gama wannan tunanin ba yaji ana murda handle din kofar da k'arfi gaban sane yaji yafadi sanda yaji muryar ta tana cewa Yaya "Agrif anan kake ne dan Allah kabude min wllh bana iya kwana ni kadai tsoro nakeji".
ta k'arashe maganan tana dafe maranta dan wani irin murdawa yakeyi duk kwana kin nan hakuri takeyi ta rasa wane irin abune yake damunta tabbas cikin jikin ta yana da son a sadu ga magunnuna da aka dura mata yau ma Mama sai da tabata wani shiyasa take jin mugun sha'awa
Ji shiru yasa tace'' dan Allah Yaya kabude"?
tayi maganan tana jij-jiga kofar da k'arfi

bude Ido Nasir yayi yana murmushi yace "kaji jarababbiya ko"?
Nasrim da sauri ta koma d'akin ta
ta dauko wayan ta Saida tazo dai-dai kofar da Agrif yake ciki ta danna k'ira dan azaton ta kobaya d'akin ne aiko taji waya yana Ringing aciki amma har ya katse ba adauka ba
tabbas tasan duk baccin da yake zai ji wannan bugun k'ofar da k'ira da take masa
Afili ta furta "yaya Agrif me hakan kenufi"?.

Nasir yace'' ka bata amsa da cewa kai kana tare da wata yau ba zaka samu daman budewa ba kana da buk'uwa".

cikin razana Agrif yace" ah ah bazan iya ba Nasir cikin sharad'in mu ba wannan'.
mek'ewa yayi tsaye yana cigaba da murmushi sa
yace "ni zan iya yayi bakin k'ofar
Agrif bai ankara ba yaji Nasir ya canza muryar sa ya koma irin na mata sak sai ka rantse macece yace "ke balla gaza da baki san waye mijin naki bane to ki koma da jaraban ki tunda har ya gaiyatoni har gida ba zan hakura ba ban saba da kwana ba namiji ba".
cikin k'araji nasrim tace'' wacece ke......?

sakeyin muryar matan yayi yace' keni bani da wannan lokacin idan nagama aikina na tafi ki tambayi mijin ki".
Agrif zayyi maganan Nasir ya fisgoshi yayi bathroom dashi sai da suka shiga yaturo kofar yace "kasan ni ba tsoro nake jiba idan kayi magana ko kamusa to dai dai yake da tonan asirin komai dama ni shi nake jira........

ji sukayi Nasrim tana wani irin buga k'ofar kamar zata karya tana cewa " ya Agrif kasan wacece Nasrim awajen kishi amma kamin haka kashigo min da k'aruwa har d'akin aure na ka manta nace duk randa kaso wata to za ayi biyu babu wllh kashe ku zanyi".
Agrif yana ji yana gani har muryar Nasrim ya dashe amma ba halin yafita lekawa yayi ta bulin mukuli yaga hannun Nasrim har yakumbura dan bugu jinginuwa yayi jikin kofar yana maida numfashi shi kam Ina ma zai mutu yahuta da wannan rayuwar Ina ma zai iya kisa za zai kashe Nasir kawai ya huta in yaso shima akashe shi sai de shi ko Marin mutum bayason yi balle ya illata mutum ko cinnaka bai taba kashewa ba".

azabure Agrif ya mek'e jin wani irif yana cewa wllh nas...…...

*To masoya mu kasance cikin pages na gaba 10 Ina jin dadin comment din ku ngd sosai da soyayyar ku*

*Taku b JATTKO*
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*

*BATUL ADAM JATTKO*

*Marubuciyar*
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYAR*
*NOW*
*FURUCI NA NE*

*10*
Chapter 31 · 0% Book details