← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 100

Sashe 40

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

**********************
IZZA da Baban ta
"Baba baza ka gane bane wllh kowa yafi son yaran Nasrim da nazaci dan anga maza ne sai yanzu data haifi macce nagane ba komai bane nuna ban banci ne shi kansa Aiban fa yafi son yaran Nasrim akan namu komai yace 3 brother idan kaduba Media duk inda ake daura picture to hoton su zakaga ya d'aura yanzu haka ko password din wayan sa dana computer din sa sunan Khafulan ne ga Nasara bai taba ko kallon inda yara na sukeba amma yaran Nasrim tamkar shine uban su nagaji".
cikin daure fuska Baban nata yace
"Izza saurareni duk wata na sara yana tare da hakuri nace kiyi hakuri akwai wani guba da zai fashe acikin gidan nan wanda Ina sa ran mu zayyiwa dad'i kece da riba amma sai kinyi hakuri matakin na sara hakuri ne".
"amma baba ka duba ida yanda za ayi dan Allah".
"nace miki akwai abinda yake shirin faruwa wanda yafi guguwar tsafina ma k'arfi kede kiyi fadan Allah yasa yafaru mune da nasara tasu ma ya ishe su basai nayi wani abu akan su ba".

"shikenan Baba bari na koma ciki dan na san ko Musanat zata fashe da kuka sai de suce ma ai'katan gidan su goyasu amma bade Ummu ko Mama ko mommy su d'auke ta ba".
tayi maganan tana tashi

murmushi Baban Izza yayi yana shafa gemunsa afili yace yacika taf rikicin babban gida zayyi fashewa da kowa sai ya hadiyi zuciya yamutu daga ni sai izza da yaran ta zamu rage".

Nasrim tun tana sa ran ganin Agrif har dare shiru ga wanya sa bata shiga
haka washe gari ma da dare yayi ta kasa jurewa sai da ta dai-dai ci kowa ya tafi part din Hajja ta saka dogon shijab ta fito ahankali take takawa har zuwa bangaren nasu shiru har tafara tunanin ko bayanan sai kuma ta tuno Zakar ya tabbatar mata da yana ciki sama ta haura bata koyi knocking ba ta murda handle din tashiga ganban ta ne yafadi asan da tagan sa a kugunnune cikin barko da sauri ta k'arasa tana cewa "Abban Fayyat kana lafiya kuwa".
ta k'arashe maganan tana Jan blanket din hannu ta daura goshin sa zuwa wuyan sa zafi taji rau cikin gigicewa tace'' kai Agrif me yake damun ka kaji jikin ka kuwa".?
a hankali ya sauk'e hannun ta ajikin sa yace Halima bana son haramtaccen hannun ki ya K'ara tab'a min jiki abu daya nake buk'ata awajen ki meyasa jaririn nan tayi kama da muhammad".?
Nasrim tace"muhammad waye"? ku..............
*Rikicin babban gida*

*jiya kunji ni shiru wani uzuri yahana nayi typing ina neman afuwan jira da b'atamuku lokacin da nayi Wanda suka kirani dan jin lafiya nagode da kulawar ku nima inayin ku over*

*sannu ku da kogari karatu masoya Ina jin dadin comments naku ina kuma jin dad'i sosai shi yake k'aramin k'arfin gwaiwa muje zuwa rikicin babban gida zanzu za afara*

*B JATTKO*
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
-rikicin babban gida-

NA

*BATUL ADAM JATTKO*

*13*

" waye MUHAMMAD?
Haramtattce kuma hannun nawa ?.

shiru Agrif yayi yana tunanin anya idan ya zargi Nasrim yamata adalci gaskiya zargi haramun ne kuma ayan da Nasrim ta tsani Nasir bawani abu da zai faru tsakani su wannan wani Shirin Nasir ne dan yasake dulmiya rayuwan su cikin matsala yanzu idan yabari suka samu matsala da Nasrim to Nasir yayi Nasara kenan ko
kawai sai yafara wani irin karkarwa alaman zazzabin ne yake damun sa daganan yafara sururu
" ammmm ke wacece dan Allah ki kiramin matata Halima ah ah ana kiranta nasssrirm wayyo kaina ne kwarkwata ne a kaina zata ciremin kwarkwata ki kiramin matata kar ki tabani da hannun ki Haramtacce........
kuka Nasrim ta fara Sosai tana jijjigashi "ya Agrif me yake damunka jikin ka kamar wuta nashiga ukku.."
tayi maganan tana sakin sa tare da fita da sauri abakin get din part din taci garo da Zakar bodyguard din Agrif din
"lafiya Madam".?
cikin in nina tace'' Agrif Agrif "
tana nuna masa cikin gidan
atsorace Zakar yace Sir!.?
Yayi saurin shiga cikin ita kuma da gudu tayi part din Hajja cikin kidima take musu bayani a kidime kowa yatashi akayi part din Agrif bai dena sururun ba har Saida mommy ta masa allurai har dana bacci
Hajja tace'' ooo ni Lami ina jan ina murnan zamun Zainabu ashe Haruna Yana cikin wani hali haba nifa tunjiya ban ganshi ba Allah sarki me gida Allah ya baka lafiya".
Mommy tace'' abarshi yadan huta Abbaty Kai zaka kwana dashi idan dawani matsala sai ka sanar dani".
Hajja tace'' to Adamu ka kula da shi Sosai nima badan ban iya bacci sai a gadona na Abdulsamad ba da anan zan kwana yo idan na kwana nan ai sai na manta a shima nida duk juyi sai na masa addua Allah sarki Abdulsamad dan al'jannan
Nasrim ba a son ranta ba ta tafi ko cikin dare takira Abbaty yafi so 3

Sai bayan sallan asuba Nasir yabi su daddy gaida Agrif bayan fitan su daddy Nasir yacewa Abbaty
"bro kaje kadan samu bacci ina nan".
Abbaty Yana fita Nasir ya rufo k'ofan har da murd'a key yazo ya zauma kan bedside
yace "wllh A'A ina tausaya maka bansan yaushe kazama me taurin kai ba".
tashi Agrif yayi zaune ya kamo hannun Nasir yace " ai nadena na barmaka komai ahannun ka kayi yanda ka keso na baka nan da ahikara dubu 1000 ko zaka gaji amma abu dayane bazan saki matata Halima ba yara kuma da kake tara mana wllh ba ragata kayi da komai ba sai ma k'aruwa dana ke samu ko yanzu na mutu yaran nan amatsayin nawa suke ni zanfi samun adduar su fiye da kowa ake zuwa gidan marayu ma ake daukan yara arena balle ni yaran Dan uwana makusan cina Wanda suka fito ajikin Nasrim yarinyar da bani da kamar ta wllh godiya ma yakama na maka musamman yaran da suke fitowa da kalan kyu na daukan hankali shiyasa kowa yake son su saboda albarkacin wannan kyan da suka gado".

shiru Nasir yayi da alama yarasa abincewa

wayan Agrif ne yayi ring hannu yamek'a yajawo akan bedside murmushi yayi ganin Nasrim ce yana d'agawa yafara mata waka
" _TILAS GANIN MU TILAS BARIN MU KAUNAR KI TUN DA NAYYI NISAN SO BA BATUN NA FASA KO ZA'A CE MINI IN BADA RAI FANSA_".
wani nannauye numfashi ta sauke cikin sanyi murya tace
"Al'hamdulillah Abban Fayyat wllh na tsorata jiya ya jikin naka yanzu".?

cikin tattausan murya yace" naki din sai kin rama min wak'ar da namiki".
Murmushi tayi tafara
_ME KAKE SO YAZA MA ALAMA DAN AKWAI SABO INKO YARDA KAKE BUK'ATA TO GASAN YA RABO DAN KAI GUDA NE DA BA KAMAR_ shi kenan ".
"Eh ya 3brother ya baby".?
tace
"ga baby ai su brother suna wajen mommyn kasan wai wancen bayahuden yace agun ta zasu zau nima har yazu banga Fayyat ba tunda aka masa k'arin jini".
yace' kar ki damu ai Mama tana da sauran yaran rik'o awajen ta mommyn dama ya dace abawa jikin Fayyat kuma da sauk'i jiya ai ni na dauk'o su bayan munzo ne zazzabin yazu ba min".
"to kai ya naka jinkin.?
"Al'hamdulillah ba abinda nakeji yanzu sai son ganin ki".
hakade suka k'araci firansu Nasir yana kwance agefen sa kamar baya ji
har ya kashe wayan
ya maida kan bedside yayi rigin gine yana kallon sama yafara wak'an
_zama na aure yana da dad'i yana da dad'i ma'arata ashe soyayya da dad'i_

sai kuma ya mek'e tsaye yana taku ahankali zai shiga bathroom har ya murd'a handle ya juyo
yace " na fad'a na k'ara wanda yaso ka kaso shi wanda ya k'ika ka kleshi hassada babban ciwo a zuciyar me k'ullaahi
kuma duk mai halin muciji bakin sa bayi kyan hali ba wani bai yadda JALLA keyi ba
Bai yadda da k'addara ba to naga tuni yayi gaba".
Chapter 40 · 0% Book details