← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 100

Sashe 67

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy na yarda ai kaji abinda yace
Kuma daddy abinda yasa nima na tabbatar da bai mutum ba ranan da ake wankan sa da idona naga dan yatsan sa yamotsa nayi sauri na danne dan kar mutane sugani
Dama kuma Mama tace so biyu tana caka masa wuk'an Yana rikewa wuk'an bai shigeshi Sosai ba
Kuma sannan Daddy damu kaje mak'abarta a gaban idon kowa aka binne Khaldum da Fayyat amma Agrif kai da Abu kukace a watse kuma naga shigowar motan asbiti cikin mak'abarta bayan fitan motan bajimawa kuma kuka fito kaida Abu da Baba suleman da Baba Hamza
washe gani da nakoma mak'abartan zanyi sheda akan kabarin su sai naga Wanda aka tona dan asa Agrif danyen k'asa ne bai bushe kamar na su Fayyat ba na tambayi mai gadin nace ya akayi wannan dan uwan nawa k'asan har yanzu danye yacemin wai ai yanzu aka kawota kuma macce ce".
nide nasa sheda nabar wajen
Duk alokacin ban dauki abin da mushin manci ba duk da naga k'afar sa ta motsa amma tunda an binne sa ai zaimutu acikin rami sai yanzu da ya aikomin da tabbacin bai mutu ba".

Daddy yace'' Habubakar bana son sake jin wannan abakin ka ko Agrif bai mutu ba ai uwar ka ta kashe Khaldum da Fayyat kuma karikewa Agrif Amana kamar yanda yace idan kasake wannan maganan yafito ban yafe maka ba".

"Daddy zan rike Amana dan uwana bazan gayawa kowa ba amma............

*Sorry sis mu hadu a 24*
*Humairah an zama bazawara Izza bazawara Nasrim bazawara dir k'ashi muje zuwa*

*Wane irin wasika AGRIF ya aiko? Muje zuwa rikicin babban gida*

*Bj*

*FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*INA GODIYA SOSAI DA COMMENTS*

*24*

zan reƙe amana Daddy amma dan Allah kasan inda Agrif yake".?
daddy yace " idan nasan inda yake menene".?
"Daddy ƙiramin shi zakayi ina da abinda zan gaya masa dan Allah daddy".
kallon sa daddy yayi sosai ya girgiza kai yace'' bansan inda yake ba sai wani lokacin ka kula da kanka nasa an dauke maka duk wani wahala dan haka kana da lokacin ibada kayi ta istigfari da karatun Qur'an".
hannun daddy ya riƙem yana girgiza kai shima daddy bai san sada hawaye ya suraro masa ba ahankali yaja hannun sa yaraba dana kamal yafara takawa da sauri sauri
cikin ƙara kamal
yace "daddy karka tafi
ka barni daddy inason narayu cikin yan uwana daddy daddy.......

Daddy a cikin mota sai da yasha kuka yaja tissue yagoge hawayen sa sannan yabawa driver umarnin yaja wai kamar shi justice Abdulmajid ne yau yazo ziyaran ɗansa a prison gyaɗa kai yayi afili yafurta Allah humma'ajirni fimusifati".
juyowa driver yayi yace "Alhaji ALLAH de yafito mana da kamal lafiya Allah dan cikar sunayen sa tsarkaka".

"Ameen Lamido". jinji Daddy

*Nasir asbiti*

shigowar wani babban Alhaji wanda da gani yagama taka ƙasa ne ya dakatar sa doctor Ibrashim daga barazanan daga Nasir daga doctor din har nursing din sun kuyar da kai sukayi suka gaidashi cikin ladabi nursing din suka fice suka bar dr da Ahaji a wajen adaidai lokacin wata ƙyakyawar buduwa da bazata wuce shekaru 20 bata shigo cikin taku irin na isassun yan mata wanda gata da kuɗi ya gama ratsasu cikin siririn murya ta tace "dad nafa gaji ko nayi gaba wllh ƙafafuwa na kaman zasu cire nakeji".
Alhajin yajuyo yace "haba Mamana kema wannan dogon takalmin haka ai dole ki gaji bana hanaki saka irin wannan takalmin ba".
"to dad aini a US bana iya tafiya da wani filet sai nadin ga jina ina sauri na saba da wannan".
taƙarashe maganan kamar zata saki kuka
murmushi dad din nata yayi yace ai nan ba US bane".

cikin shakwaɓa tace "dad wayyo ƙafata".
taƙaraahe maganan tana ɗaga doguwar rigan ta har zuwa cinyar ta akan ya tona asirin santala santalan cinyoyin ta farare fat
ta dago ta sake cewa" dad ka gani wllh kunbura yay......

maganan ne ya maƙale mata ganin Nasir kwance akan gado idon sa a lumsha cikin sauri tace dad
"who ts he ?. ta ƙarashe maganan tana matsawa
kusada Nasir din
Dad din nata yace patient ne ma na Mamana".
"Dad balarabe ne?".
doctor Ibrahim ne yace" ranki yadade Hanifa bahaushene sai uban taurin ka wllh ga fadin rai kamar dan wani ni duk ɓaci da shagwaban sa ya ishani gashi wanda suka kawoshi suna gane gaskiya ba shine me lefin ba suka gudu yan sandan ma sun gudu daganan ya kwashe ya fada musu labarin abin da yafaru Nasir
ya daura da cewa

"satin sa biyu anan aka kama wanda yacire idon yasake komawa anguwar da niyar yacirewa wata aka kamashi dayasha budu yace shi yayi wancen ma shine aka dauko
wanda akace yacirewa ido tazo ta sake ganin sa tace ba shi bane aka nuna mata wanda aka kama tace Eh ahine itama yarinyar da akace yayi rapping aka sake kawota tace ba shibane yaran ne kawai suke a gigice alokacin da sukace shine yataka sawon ɓarawo ne kawai".

kuka Hanifa ta fahe dashi sosai tana shafa fuskan Nasir tace "Dad kaga kaga abinda sukayi masa wllh Dad bazan yarda ba sai sai nasaka an kama duk wanda suka masa wannan Dad dan Allah kaga ƙafarsa yana fitar da ruwa Dad kasa akula dashi sosai mutafi dashi us kawai dad ".
ajiyar zuciya Alhaji Mudansir ya sauƙe yace " dr Ibraahim ya akayi akabar ƙafan ta lalace haka".
"sorry sir aikin nashi ne yana bukatar kuɗi sosai kuma yaƙi fada mana family sa".

cikin ɓacin rai alhaji Mudansir yace "Ibrashim danme na bude wannan asbitin badan temakon al'uma bane dole sai ya fadi familyn sa zaka temake shi so nawa zan cemaka ni nine familyn marar gata duk tsadan temako kataɓa jin nace yayimin yawa."
"sorry sir".
Dr yace yana sunkuyar da kai
Hanifa tace "Dad yanzu ba lokacin wannan bane atemaƙe shi".
Dr yace "sir inaga akai shi india zaifi warewa dawuri bawani bata lokaci aka dauki Nasir aka fita dashi yaja fece mask sosai ya rufe fece din yanda baza agane shiba

*******************

*bayan wata shidda*

Alhamdulillah anyi aiki kuma ansamu nasara sosai yana takawa da kafarsa sai ɗan abin da ba arasa ba dan yana ɗan ɗingisawa kaɗan har yanzu

Hanifa haukane kawai batayi akan Nasir wani irin mahaukacin so take masa shiko ko kalman baki bai taba hadasu ba idan tazo ma tana magana jan idon sa yake yarufe ya hade fuska yazama NASARAN sa sak sosai Hanifa take tsoron sa kuma duk wani wukakancin da yake mata baya hana ta kulashi

"Momy ya zan masa nayi duk yanda kikace ko kallona baya yi Momy ko da wasa ban taba kamashi yana kallona ba momy kamar ma yatsane ni wllh Momy bazan iya cigaba da daukan hakan ba Momy ki dafa ƙirjina kiji wllh duk saurin bugawan da yake da sonsa yake bugawa idan yabar Momy nashi ukku".

"please my daughter insha Allah zai soki kamar yanda keki son sa amma kici gaba da respect din sa sosai dan kinga da ganin sa ba baɗan ƙananun mutane bane dagani yana da hadi da jinin sarauta ko wani babban gida kin gane irinsu tsadane dasu sai kin dage sosai
bakiji Daddyn ku yace zoben hannun sa kaɗai zai iya sayan gidan nan da muke cikin ba balle agogon hannun sa wllh ni bazan ma iya lissafin miliyoyin kuɗin agogon nasa ba duk inda yafito dan wani ne a duniya
ni ban yarda ma ba afurike bane ".

cikin shagwaba Hanifa tace "ni Mommy bana mason yazama dan wani nafison ɗan talaka dan ai wannan ƙyan nashi kaɗai ya isa jari momy ƙyansa ya fanshi komai".

girgiza kai Momy tayi tana murmushi tace "kai my daughter Allah yabaki wannan Ahamed din".

"AMEEN Momy na bari na duba ko an gama breakfast na kai masa da kaina".
ta ƙarashe maganan tana yin hanyan kitchen
masu ai'ki har ukku ne suke biye da ita anshirya abinci kala kala kamar ba mutum dayane zai ciba cikin kadabi suka shige da abincin saida HAnifa ta tsaya ta ɗan gyara pert work din jikin ta sannan ta sake kalon fece dinta a jikin glass ɗin ƙofa murmushi yayi tana ɗagawa kanta gira alamam tayi ba ƙarya
tashige ciki tana canza tafiya

masu ai'ki suna fita ita tana shiga ahankali ta zube a gaban sa a ƙasa cikin sanyin murya tace " My bro ina maka fatan farka da zuwa Allah ya yarda zaka taka da ƙafafuwar ka am happy".

bai ko ɗago ya kalle taba sai ma daukan remote da yayi ya ƙara volume tayiwa kan da alƙawarin ayau sai yayi mata magana kamar yanda dad dinta yace yana magana ita de bai taba mata ba ahankali ta meƙe ta zauna a kan kujerar da yake three'sitter matsawa tayi sosai jikin sa duk da gabanta yana faduwa " my diar how are you feelings".
still bai ko kalle taba idon sa akan Tv
ajiyan zuciya ta sauke tace " dan Allah ko magana marar daɗine ka gayamin wllh zanji daɗi nasan kasan dani hakan zai iya sani farin ciki ban taba kula wani ba dan Allah ina son jin maganan ka koya yake dan ALLAH idan kana son MANZON ALLAH da ADDININ MU ina haɗaka da kirman Allah kayi magana ni ko zagina ma kayi ".

ta karashe maganan tana daura hannun ta akan cinyar sa
tacigaba "wllh kome kake so arayuwa zan baka ciki harda kaina ta ƙarashe maganan tana ƙara shige masa sosai har jikin su yana gogan na juna
cikin ɓacin rai da tsare gida yace" AL'HAMDULILLAH kince duk abinda da nake so zaki min ko".

Hanifa ware idon ta tayi tana control din numfashin ta dan jitake kamar numfashin ta bazai dawo ba cikin wani irin murna da sauri tace " yes yes my love wllh zanyi".
Chapter 67 · 0% Book details