← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 100

Sashe 54

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gyaran murya daddy yayi yace'' Kamal ka dena irin wanna magan ganun ai idan cutar dasu zayyi bazai fita dasu a idon jama'a ba bana zargin Nasir na komai saboda bai kasance cikin masu boye abu ba komai nashi afili ya keyi ".

haka de Kamal ya tashi shi yarasa inda zai bulowa wannan lamarin k
gaba daya kansa ya gama kullewa

Mommy tayi shiru awani tafkeken parlou da dake ciki ta gasa gane wane garine amma de nasan ba Kano bane tunda anyi tafiya me nisan gaske da ita idon ta arufe juyowa tayi tana shafa kan Zainab da take bacci sai Khafulan daya dameta da jikinsa yana masa ciwo tanemo basa Ball
Jin an murd'a handle yasa da sauri Mommy ta juyo mek'ewa tayi atsaye tace
" Nasir dama Kai kasa aka kawomu nan".
Murmushi yayi Yana k'arasowa yace" mommy Eh wllh ya zauna yana ajiye file din da yake hannun sa a gefin sa yafito da bindiga acikin al'jihun wandon shima ya ajiye yace "mommy ayau nake son komai ya zo k'arshe dan nagaji da wannan b'oye b'oyen zaki saka hannu a wadan nan takaddun da sunan kin barmin dukiyar ki gaba daya sai komai ya zo k'arshe kamar yanda na karboki haka zan karbo y'arki ma nide dukiyar da ubana ya Tara wata ba zata zauna tana ciba kum..........
Bai k'arasa ba mommy ta tashi tana nunashi bakin ta Yana rawa tace'' Nasir wllh k'arya".
shima mek'ewa tsaye yayi yace mommy idan ni zanyi k'arya ai wannan bazayyi ba ya k'arashe maganan yana dauko bindigan tare da seta mata a k'ey".

*To masoya muje zuwa wai waye sta din FURRUCNA NE nikam meje zuwa ranan Monday insha Allah da misalin 9 pm*

*masu yawantambaya na sunayin da suke cikin littafin *FURUCI NA NE*
*ai nake ga duk ka sunayi ne na hakikka sai kawai dan alkunya da akayiwa* *Halima nasrin wata itaciya ce *me k'amshi da fan sha'awa a* *gidan aljannan*
*NASRIN MINALLASHIH*

*Haruna Aarif ana nufin kaman babban mutum ko jaroran*
*Khaldum basarake*
*Aiban kalman godiya*
*Khafulan jajircece*
*Fayyat mai alfarma shima de kalman sarautan*

Bj
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
( _rikicin babban gida_ )

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

*18*

"wllh k'arya shima bindigan da bullet din su keyi k'arya suke su fasa kan mommyn Nasir tace'' tana ture bindigan a k'eyar ta dariya yayi yana jefawa Khafulan bindigan wasan yace'' wai mommy kina nufin ban iya Acting bane baki tsorata ba".?
murmushi tayi tace''
ai ba aikin ka bane shiyasa ko kyau bai yima ba".
Khafulan yace'' Papa nifa Ball nake so jikina ciwo yake min so nake nayi Execise.'
dafa kansa Nasir yayi yace''ooo my God son rigima dare ne kaje sama ka kwanta zamuyi magana da mommy good night ".
yaron zai sake maganan Nasir ya d'aga kai yamasa kallo na gaske Wanda idan Zainab ko su khadum yayi wa har fisari suke amma da yake Khafulan shima Theron kan sane jifa yayi da bindigan hannu sa yana turo baki da gun guni yayi gaba mommy dariya tayi tace'' oho de ai kwara da yazo inda ni da karena ne ai baza kaje ba".
Bai juyo ba amma yanda yake yarfa hannun da gani masifa yake
Nasir ya sauk'e a jiyan zuciya yace'' Mommy yaro nan bashida kunya ko kadan fa".
Mommy tace'' duk waya batashi ai idan ana original copy to Khafulan naka yayi ba ma photon copy ba."

zama yayi Yana dauko Files din da yashigo dashi ya mek'a mata yace'' zaki sa ka hannu anan mommy mommy k'arba tayi takaddun ne na company daya bayan daya tasa hannun shedan ta mallaka masa batare data tambaya meye dalilin sa nayin hakan ba ita de tasan bazai cuce ta ba
jiki a sanyaye yake kallon ta shi yarasa wane irin so da kauna mommy take masa ai ko dan da ka haifa yazo da wannan batun babba za ka iya tsayawa kace meye dalili musamman idan akayi duba da wasan da yamata na yanzu da kuma abin da Dr Hafsa ta kaya mata bai san da afili ya furta" mommy idan ina dake a duniya narasa komai ma zanyi godiya".
d'ago kanta tayi tana cigaba da kallon sa tace'' ina ai bazaka rasani ba banayi maka alk'awarin sai naga jikojin ka ba dan Allah Muhammad ya isa haka kayi aure kai baka ga duniya yana k'erewa bane ga Abbaty nan kanin bayan ku zaiyi aure badan wannan abinda ya faru ba da wata kila matar sa tana da k'aramin ciki amma kai shiru yanzu da mutuwan Agrif da Aiban kaine shikenan watara za amanta ka gaba daya yanzu kaga ko su khadum da Fayyat ba za a manta suba tunda ga Khafulan nan duk Wanda ya gan shi zaice ai su ukku aka Haifa jikoji da tattaba kunne ma sai sunce ai kakan musu ukku aka Haifa amma kai kam b'ata zakayi bat".
a take yanayin sa ya canza cikin b'acin rai yace" towai mommy banji zan iya son yarinyar mutane ba zanyi aure ne bayan nasan bazan iya mata adalci ba ai Annabi yace aure sai kaji zakayi adalci kayi hudu ma amma idan kaji ko dayan ma baza ka iyayewa adalci ba ka hakuri dama sunna ne ba farirla bane".
"haba Nasir buri nane fa kayi kodan ni".
tsaki yaja yakoma Nasuru sa sak yace'' saboda ke zaki zauna da ita ina gaya miki gaskiya kina sake wahalar da kanki."

Cikin b'acin rain itama
tace
"to Nasir ai naga kana da Wanda zaka iya zama da ita mutane sunfara surutun inda ni na haife ka bazan bari ka kai kusan 36yrs ba aure ba kana shiga 40 fa ka fara zama dattijo kuma naga kana da Wanda zaka iya zama da ita Ina Zuhura yar maiduguri nan tana da kirki zata dace dakai daganin hakurin ta zata iya zama da baud'adde irin ka....
katseta yayi dacewa "mommy bakina da naki na cemiki Ina son ta zan iya zaman aure da ita nifa kawai na ganta da irin zanen kine fa kuma yar maiduguri shine nake dan mutumci da ita shine so".?

"To shikenan my son kar ran ka yab'aci ina maka addua wata rana zakayi".
d'aga kafada yayi yana mek'ewa tsaye yace'' shi ke nan
mommy ki kula da kanki da yaran".

Mommy tace'' kai Ina zaka"?.
"Kano".
Yabata amsa a tak'aice
cikin mamaki tace'' nan din ina ne".
cikin wasa yace'' gidan kaso ne".
girgiza kai tayi tace'' my Son".
har yaje tsakiyar parlourn mommy ta mek'e ta kamo hannun sa tabaya tace'' dan Allah Nasir kafitar dani a duhu kagano wani abu ne waye yasawa Hajja guba ina Barira waye yayi belling din ta kana ganin idan aka kama Barira ai asiri zai tonu".
"Mommi komai yazo k'arshe fa kiyi hakuri ko kin koma gidan kar kicewa Barira komai nasan yanda zanyi bana son kisake cewa komai".
"shikenan Nasir nabar komai a hannun ka har cese din k'anwar dan Allah Nasir ka temaki rayuwar k'anwa.......
dakata Mommy wai meye naki na damuwa da wacce y'ar ne ni kadai ma na isheki rayuwa balle ga Zainab ga Khafulan daga yanzu ki lissafata cikin gawar waki dan cikin da yake jikin tane ya hana bamu daukaka k'ara ba dan al amarin yafara bani mamaki har wasu makasan k'awayen ta
ta fitar acikin gidan prison din da take.....
ajiyar zuciya mommy ta sauk'e ta katse shi da cewa shikenan Nasir yanzu yaushe zamu koma gida dan kwara ina daga can yafi".
"akwai gyare gyare da akeyi a part din ki ne saboda k'ara matakan tsaro zuwa tomorrow ma Ina ga saudia zaki wuce idan kin dawo sai ki sauk'a a can nan inda kike Kaduna ne akwai komai a gidan Sai anjima adamu zai kawo miki girls house akwai masu gadi sosai a gidan".
har juya zai fita kuma yajuyo yace'' amm yawwa Mommy zakiga na kulle general account din ki idan kina buk'atan man yan kudi ki tambaye ni".
gyad'a masa kai kawai nayi takoma tana zama gaba daya tunanin ta ajagule yake meyasa Nasir ya tsani Nasrim haka wane zuciya yace duk lefin ki ne tun yana k'arami zuciyar sa ta ginu da kiyayar ta amma baki kwabe saba gashi yanzu anzo inda shi kad'ai ne zai iya mata maganin abin amma ba zayyi ba saboda yana daukan ta amasayin mak'iya yanzu yazanyi Ina Dr Hafsa tabani shawara ko tana zuwa duba Nasrim nide tun ranan farko bata sake zuwa ba
da sauri ta mek'e har an bude masa mota zai shiga back seat
yaga fitowar Mommy tsayawa yayi yana sake hade fuska a tunanin sa maganan Nasrim zata masa
cikin sauri ta k'araso tace'' waya ta fa ?."
a tak'aice yace'' suna gida".

"to Nasir haka zanyi ta zama inason yin magana da Dr Hafsa".
bai sake ko juyowa ba ya shige mota
Mommy dafa kai tayi afili tace'' Allah ya shiryamin kai ya kareka daga dukkan Sharri yabaka sa'a da Nasaran rayuwa".
Komawa tayi ciki

*******************
*Three brother*

Nasir numfashi yasak'e idon sa akan Hajja yace "ammm Hajja Mommy ta mallaka min komai nata hatta company dinta na shikama nikuma na mallakawa Zainab yar gidan Agrif company sarrrafa Madara nawa na Legos sai yaran Aiban mata guda 3
tun gafin ya karasa gaban Izza yayi wani irin bugawa !!!!!
Chapter 54 · 0% Book details