← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 100

Sashe 9

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abdulraham yana zuwa gun Hajja ya wuce ya bada cinyar ta cikin kuka yace "Hajja ya zamuyi ya zamuyi shima Abdulmajid sai a sannan yaji kuka yazo masa duk suka rungume ta suna kuka Abdulmajid yace "Yarabbi muna son d'an uwan mu amma ka dauke mana shi alokacin da bamu zata ba Allah kasaka mana dauriyar da dangana".
Abdulraham yace "Allah bazai daurawa bawan sa abinda bazai iya ba Allah yana turo dangana tun kafin mutuwar tazo Allah ka yafewa Abdulsamad".
ya mek'e tareda d'an uwan sa
K'iran sallan magari ba akayi bayan anyi sallah aka sake sanar da mutane ayi hakuri a tafi tunda Jana'izar sai gobe sai yan uwa wanda yakama aka bari

Abdulraham da Abdulmajid cikin dauriya suka wanki d'an uwan su da kansu bayan sallar ishai ba wanda yasamu daman rinsawa hatta Abbaty dan shekara 3 shiko Nasir yana asbiti wajen mommyn sa cikin dare mommy ta barka idon ta akan Nasir da ya damk'e mata hannu yana gengedi a hankali tasa hannu ta kwantar da kanshi afirgice ya bude ido yana cewa "mommy kita shi".?
murmushi tayi masa tace" my son meyasa kayi kuka haka?".
tayi maganar tana shafa masa gefen fuskar da jijiyar sukayi rudu'rudu da gani ba k'aramin kuka yasha ba
"Mommy ba Abba ne yamutu ba kema zaki mutum shikenan bani da Baba bani da Mama".
d'ago kansa tayi tana kallon sa tace "Nasir bazan mutu ba Allah bazai kasheni ba ko dan saboda kai zan rayu da kai sai na dauki y'a y'an ka awannan hannu nawa ta k'arashe maganan nata tana nuna masa hannu ta

Dr Hafsa tace "am sorry Dr Fanna kiyi kakuri kisa dan gana acikin zuciyar ki mutuwa de d'aya ce kowa zaman jiran sa yake babba ko yaro duk wanda wa'adin sa yazo kisa dangana ko dan abinda yake cikin ki duk dama yanzu ba bak'aramin barazana ya samu ba dan Allah kiyi hakuri kar ki rasa abinda yake cikin ki shine k'adai son da zaki nunawa Abdulsamad ki Haifa masa abin da yabari".
Mommy shafa cikin ta tayi tace'' Dr hafsa cikina bai zube ba".?

"Eh bai zube ba".
Mommy tace'' Alhamdulillah zan kula in sha Allah nasan Abdulsamad zayyi farin ciki dan rushin sa yatafi da farin cikin wannan abinda yake ciki na Allah ka yafewa mijina isha Allah zan Haifa maka abinda yake cikina".
Amma kuka kam ta kasa yinsa sai wani irin radadi da zuciya ta yake mata
tace'' Dr ki cire min ruwan nan zan tafi naga Abdulsamad".
numfasawa Dr tayi tace'' k'awata bawai ba nason kije bane zan so ki masa addua amma bana son hankalin ki ya tashi ne".
"hankali na zaifi kwanciya agida ba anan ba Dr".

haka Dr hafsa da Dr Farda suka dafa mommy suka shiga da ita zaunar da ita sukayi a kusa da Hajja sabon kuka mutane wajen suka sake sawa ita ko mommy masu kukan sha'awa suke bata dan ita tama kasa kukan sai wani irin ajiyar zuciya take sauk'e wa
Dr Hafsat tace Hajiya dan Allah kudena wannan kukan kwantar mata da hankali yaka mata ayi ahalin da take ciki akwai barazana da abinda yake cikin ta da sauri duk suka kalle ta Hajja tace "ciki kuma!?.
Dr Hafsat tace "eh ai tana da ciki wata 2 dan Allah abata kulawa Hajja amdala tayi har su Abdulmajid
2
Allahu akbar mutuwa me yake jin dadi me raba d'a da mahaifi me sa mata zawarcin dole a hannu mukazo ahannu zamu koma ba a kauce masa duk kudin ka duk da baran ka mutuwa bata barin ku dubi yan da Abdulsamad yayi FURRUCIN yana da matakan kariya a motar sa Wanda bazai tabayin hatsari ba kuma Koda yayi ko gwarzani ba zayyi ba saboda matakan kariya amma sai gashi motar tazama sanadin sa yau da ana sayan rai Abdulsamad yana da kudin da za a tsaya masa rai ko da dubu ne amma sai gashi a hannu an d'agashi za afita dashi

Malama Shamsiya ce take ta nasiyar kada amasa rakiyar kuka haka suna ji suna gani aka fita dashi abokan sa daga k'asashen duniya irin su Albaity Abdallah Amar da shugaban k'asashe da dama har akayi sadan kan bakwai
amma bak'i kamar k'arosu ake wasu suna tafiya wasu na shigowa tsabar amsa gaisuwa yasa mutanen gidan muryar su dashewa sai de maganan kurame Abdulraham da Abdulmajid ko sai de su rubuta idan suna sonyin magana
suko yaran har sun fara mantawa dayake dama Abba ba mazauni bane bawani shak'uwa a tsakanin su dan haka jisu ke kamar yayi tafiya ne

*bayan wata daya*

munane kam sun watse sai jifa-jifa yan gaisuwa ganin yanda mommy take cikin damuwa yasa Hajja tace mata ta taro tazo part dinta su sauna breakfast suke kowa yana cin abinci banda mommy da ruwan tea kawai take hadawa me kauri tana sha
Abdulmajid da yazuba mata ido ne yace "Doctor please tabbas kinyi hakurin juriya amma dan Allah ki sake daurewa ki rungumi k'addaran da Allah ya d'aura mana ayanzu addua kawai brother yake da buk'a awajen mu mukuma abinda yake cikin ki shine buk'a tarmu hakan bazai samu ba sai kin kwantar da hankalin ki damuwa da kuka dazai dawo dashi da ko kwana bazayyi acikin kabari ba"
Abu ma yace "hakane dukkan mu bawanda baya cikin damuwa amma mun sani bazai dawo ba mu fuskanci rayuwa tare dayi masa fatan dacewa...
shiru yayi dan shima kukan ne yake son kufce masa ganin
Mommy ta sun kuyar da kai hawaye yana ta diga akan dining table din suma su Ummu kukan sukeyi
Hajja cikin kuka tace " ai kuka nidashi har tawa tazo Abdulsamad nefa wai babu shi yayi tafiyar da ba wowa yatafin inda Haruna yatafi".
sai tasake k'ara karfin kukan nata haka de wannan ahalin suka kasance cikin damuwa cikin mommy wani irin girma da nauyi yakeyi tun yana da wata hudu tayi scanning anan tasan yara ukku ne kuma duk maza ta dage sosai da kula da cikin duk da takasa cire damuwar da yake cikin ranta wanda ko wane irin abinci kawai cinsa take kamar magani yawanci drip take sawa kanta sai kuka abu medan ruwa-ruwa

*bayan wata 4*
Mommy ta shiga watan haifuwa suna zaune ita da Hajja a compound Hajja ta na bare mata gyada tana bata Mama tana mammatse mata kafar ta dayake a kumbure Hajja ta kalleta cikin tausayawa tace"niko Fanna cikin nan naki me secangin ya nuna dan ba daya bane gaskiya a yanda yarabu gida biyun nan kuma kashi har kin kusa fita awata na goma".
shiru tayi tana tunanin bai kamata ta boye musu ba
tace'' yanuna yara ukku ne."
amma batace maza bane".
salati Hajja tayi cikin hamdala da washe bakin da tunda Abdulsamad ya mutu batayi ba tace "kuma kikayi shiru abinki wannan abin al'kairin haka Allah mun gode maka kai din abin godiya ne ako da yaushe ka kwace Abdulsamad ka musanya mana da har guda ukku Alhamdulillah yaushe ne
EDD naki?".
Mommy tace'' tun jiya yacika kuma tun ajiyan na fara alamun labor amma bawani matsala in sha Allah zuwa shida na yamma zan iya haifuwa".

azabure Hajja tace'' wai ni keko wannan Fannan wace iriyar macece wane irin zurfin ciki Allah yabaki yanzu haka nak'uda kike kike zaune haka"?.

Mommy murmushi tayi tace" ai Hajja bana jin wani ciwo kuma ai ina tashi nadan zaga abinde ina ga da sauki zai zo mun dama yawanci haifuwar yan biyu ko ukku ba ciwo kamar na daya yawanci daya yafi ciwo sabo da mutum yagama ciye ciwon a goyon cikin su bawani damuwa nakira Dr Hafsa ma nace idan ta tashi tabiyo tanan bawani damuwa dan ba sai munje hospital bama In Sha Allah".

" Hajja tace'' kuma fa hakane nima Abdulsamad banyi nak'uda ba ina jan rijiya naji marata tayi nauyi nishi yana zuwa min ina tsugunnawa Abdulsamad yana fadowa amma Abdulraham da Abdulmajid nayi nak'uda har Sai da muka je asbiti Allah de yakawo miki da sauk'i ya raba lafiya".

Mama cikin mamaki take kallon mommy ta ma kasa magana
can tace'' sannu mommy Allah yaraba lafiya ko da wani abinda zan iya temaka miki"?.
Mommy tace''a a hajiya Mama karki damu".
Mama tace'' to bari naje na sanarwa da Ummu wannan abin farin cikin yara har ukku".?
Chapter 9 · 0% Book details