← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 100

Sashe 46

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nigeria
Bayan sauk'an su Nasir amamakince yake min mutanen da suke tare tun farkon layin su da kallo wanda dole su suka sauk'a dan mota bazai shoga ba amma dayake bashida kuzarin da zayi wani masifa kawai sai ya sauka tabbas agidan sune amma to meyake faruwa".
yayi maganan afilli hannun sa Aliyu ya sake damkewa yace "sorry MUHAMMAD mushiga ciki ko".
dak'er suke kur tsawa har suka samu nasaran k'arasawa wajen get din masu gadin suna ganin Nasara suka bude kofar ya shiga
da d'ai-d'ai yake kallon mutanen gidan Wanda su Hajja ma har yanzu suna compound duk ana waje a zaune a k'asa Hajja ce kawai take kukan da bama fitowa yake ba muryar ta yagama dashewa Ummu ko tuni ta suma anyi asbiti da ita
yana jefa idon sa kofar part din mommy yagan ta kwance sai faman shafa mata ruwa ake ahankali yake takawa gaban sa yana faduwa
ya k'arasa wajen mommyn zuba gwaiwogin sa yayi a k'asa lips din sa narawa yace "mommy meyake faduwa"""?
Mommy jin murya Nasir yasa tayi saurin mude idon ta kamo hannun Nasir ta damke cikin wahalallen murya tace'' sun tafi da ita Nasuru zasu kashe min y'ata zasu kashe ta Nasuru kaine gatan mu ka karbo min y'ata agaban Alhaji Abdulmajid aka jefa min ya a hilux police suka tafi da ita zasu kashe ta wllh Halima bazata kashe Fayyat da Khaldum da Agrif ba tana son su Dan Allah Nas........
"FAYYYYT KHALDUM
cikin wani irin k'ara da amonsa ya amsa duk gidan yasake cewa "mommy ina Fayyat ina Khaldum kafin mommy tayi magana Khafulan yace " Papa mamy ta shashe su har abbanmu yan sanda sun tafi dasu ni buya yani a toilet Ina ta kiran ka bakayin picking ba papa".
"ahankali Nasara yamek'a tsaye yana girgiza kai yace mutuwa "Ah Ah baza su mutu ba mommy ki min bayani ta yanda zan gane ya za ayi Khaldum da Fayyat su mutu ban nemi yafiyar suba ah ah mommy ki min bayani ya kalli Dr Hafsa yace Ummyn Ayman meya faru? ".
Mommy tace'' Nasuru nima ban san meyake faruwa ba bana gane komai Fayyat ya mutu khadum ya mutu jikokina dana daura dukkan burina akan su an kashe Aiban da guba banyi magana ba naga illan shiru yanzu gashi makiya sunci galaba a kaina an kashe min jikoki an daura al'hakin kisan akan y'ata mutuwa zanyi Nasir".
"Mommy da gaske yarana sun mutu abokina yamutu". Humairah ce tace'' wllh ya Nasir ta kashe su dama tun da rana tace'' sai ta kashe ya Agrif akan ya amince zai auri Izza ta kashe masa yara har biyu".
cikin wani irin amon murya yace
"tana ina tana Ina wllh idan rai goma Allah yaba bata to duk sai sun fita cikin a zaba wllh zatayi mutuwar wulak'ancin sai na daura ta ajikin mota na jata a kwalta sai nayi pieces pieces din naman jikinta tana ina yayi maganan yana cikumo Humairah yana wani irin gurnani kamar mahaukacin zaki".
Humairah kasa magana tayi dan yanda ya cukumota ko numfashi ta kasa ja Kamal da Ayman da Aliyu da sarkin gida dak'er suka ceto Humairah sai alokacin Izza tasamu shigowa dan tana asbiti tun dukan da Nasrim ta mata kwanciya tayi a k'asa tafara wani irin birgima tana rusa ihu haka Mama ma sai yanzu tasa kuka Kamal Abbaty da sauran mutane duk suka fasa kuka daddy da Abu jisuke kamar su kashe kansu duniya ta musu k'unci da gudu daddy yayi part din sana Mama ya haura sama rarufe kansa a d'aki yayi yak'i fitowa kawai shi jira yake ace tashin duniya ne kowa ma yamutu ahuta yakeji Abu ne yabiyo bayan sa yana
buga kofar yace "haba Abdul ka zama namiji mana ka daure kafito mu kwantar wa da matan nan da yaran nan hankali muje
station a karbo Nasrim muyi cuku cukun karban gawar wakin mu musu sutura".
cikin tashin hankali daddy yace "Ah ah Abdulrahaman bazan iya fitowa ba kawai kayi duk abin da yadace ba zan iya cigaba da kallon mutane ba y'ar da na haifa ita takashe d'an ka dan uwanta mijin ta Hajja tayi gaskiya kar kayi kuskuren bellin din Nasrim duk Wanda ya kashe ran mumuni da gan-gan shima a kashe sa".
Abu yace " yanzu kafito ni kadai bazan iya duk wannan ba ga Nasir ma yazo baya cikin hayyacinsa mu yaka mata mu kwantar musu da hankali".
dak'er daddy ya yarda yafito
suka dan kwantarwa da matan hankali suka shiga parlou su kuma suka tafi asbiti dan karbo gawa zasu fita yan sanda suma sukazo binciken gidan aka nuna musu part din da abin yafaru
sai da yan sanda suka gama nasu binciken akan gawar wakin doctors sukayi aka batu gawar wakin dan haka ba asamu daman suturan su a ranan ba Saida suka sake kwana
Nasir sai binciken wane station Nasrim take yakeyi amma yarasa dan bayan magaruba mommy da aminceciyar kawarta Dr Hafsa suka tafi Nasrim tana asbiti hannuwan ta dukka biyi a daure ajikin k'arafunan gadon asbiti a d'aki na musamman yan sanda ciki da wajen d'aki
Mommy girgiza kai tayi tana kallon yanda Nasrim take fitar da numfashin duk da bacci take amma ba na dad'i bane kallon ta tamaida kan Dr Hafsa tace'' Hafsa yanzu Nasrim ce ahaka y'ar dana haifa da cikina ce ahaka a daure ajikin gadon asbiti wllh Hajja ta cuceni Allah ya isa tsakani nadake Hajiya Maryam ke kika hura wannan wutan wllh ko duk abin dana mallaka zai k'are bawanda ya isa yasa a kashemin y'ata ita kadan nake da Nasir yajuya min baya ".
sosai ta fad'a jikin Nasrim take kuka
Hafsa tace'' wannan itace mummunan k'addaran ta amma dan Allah Fanna k'in tada hankalinki dayawa in sha Allah Nasrim zata fita cikin wannan yanayi koda biyan kudin diya zamuyi zamu dauki kwararrun lawyer da suka san aikinfu Nasrim ko ita tayi kisan in Sha Allah sai ta fita".
"Mommy mommy".
su kaji Nasrim tace da sauri mommy ta d'ago
" My daughter gani meye how you feeling now me kike ji yanzu ajikin ki".?
"Mommy ina Agrif ina Fayyat ina Khaldum".
"Nasrim kin kashe su kin kashe Fayyat da Khaldum da Agrif Nasrim meyasa kika mana haka idan kin kashe Agrif saboda kishi su yaran me suka miki me jikokina suka miki gashi kinsa zan rasaki ai da kin barmin su zanji sauk'i ".

"Mommy da gaske sun mutu? Mijina yarana duniya ta kuma ake zargin na k'ashe su meya ke faruwa dani da gaske ni na kashesu mommy".
Mommy tace'' Nasrim kece mana duk bincike ya tabbatar kece Khafulan yaganki kina wasa wuka kuma yace kafin sannan da kuma wukan da yaga kin wasa dashi kikayi kisan duk kuma dama kinyi furucin hakan".
mommy idan ni nakashe su mommy wane hukunci za ayanke min".
"Kisa mana Nasrim ke ba lawyer bace kinfini sani ai".
Murmushi Nasrim tayi tace'' mommy a yau ayanzu yaka mata ayanke min hukunci inason a kasheni yanzu inason naje inda Fayyat d'ana me sona yaje na tambaye shi waye ya kashesu Ina son naje naga mijina na tambaye shi waye ya kashe sa mommy a cikin daren jiyan bayan fitan ya Kamal saida Agrif yaje mukayi magana na fashimtar juna mun sasanta dashi munyi dashi zamu tafi mubar zaman Nigeria mommy meyasa to na k'ashe sa bayan mun sasanta ya yafemin yankan dana masa a hannu ya tabbatar min da mak'irci aha hada bashi ya d'aura hoton ba amma yaga Wanda yadaura hoton dan duk Wanda yayi amfani da wayan sa yana ganewa saboda wayan yana daukan hoton duk wanda ya taba amma nayi nayi ya gaya min yace" hakan bai dace ba amma yasamu munafikin ya tabbatar masa kuma ya nemi yafiyar sa yafe masa dan haka basai yagaya min ba mommy Dan Allah akai ni kotu yanzu zan amsa nina kashe su a kasheni gwara rad'adin mutuwa da kuncin yaruwar da zan fuskanta idan ba Agrif acikin yaruwa ta".

Mommy tace'' Al'hamdulillah kina nufin bake kika kashe suba ".
"Mommy kisa aranki ni banyi ba amma afili ki barshi anice".
Mommy ta girgiza kai tace'' Nasrim bazan bari ba bazan bari akashe minke ba kokina da lefi balle baki dashi sai kin fito sai me lefin yafito da kansa".

murmushi Nasrim tayi tace'' mommy wai meye acikin mutuwa ne duk gudun da zaka yiwa mutuwa zai zo duk tsawon shekarunda mutum zayyi a duniya baya wuce dubu to da mutuwar yanzu dana wata shekaran duk sunan su mutuwa kowane rai sai ya dan danni mutuwa ban damu na mutun ba mommy".

Doctor din da yake kula da Nasrim ne yashigo zubewa yayi har k'asa yace ranki shi dade an wuni lfy ya mukaji da wannan abin da yafaro".
mommy ta juya tana kallon sa tace
"Yawwa Dr suleman kaine akanta ko dan ALLAH akula sosai idan Muhammad Nasir yazo kar abari ya ganta inde ba Daddy ta ko yayanta Kamal ba banason kowa ya shigo".
Chapter 46 · 0% Book details