← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 100

Sashe 44

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummu dafa kafadan Nasrim tayi tace'' Nasrim ki dauka amatsayin k'addara ba cin Amana ba zakiga riba Insha Allah kiyi misali da zaman hjy Aisha da Dr Fanna mana Wllh muna zaune agidan nan duk kan mu muna zaune tsakanin Dr Fanna da Aisha sunfi kusanci har Ina ganin kamar ni sun wareni ko da Abdulsamad ya rasu Hajja tace'' daya daga cikin mazajen mune zai auri Dr Fanna wllh nazaci nawa mijin za a bawa saboda yanda Dr da Aisha suke k'awance amma sai Allah yasa Abdulmajid ne mijin kuma alak'an Dr da Aisha k'aruwa yayi bai ragu ba wani abun ma sai suyi su binne ban sani ba kinga ba fa basu da kishi bane sun danne abun a rai ne kawai dan shi kishi ta yanda ka daukeshi haka zai zo maka kiyi hakuri ba abinda Izza zata rage ki dashi kuma nasan Insha Allah nima zan sa Ido akan zaman ku Baban gida zai kwantan ta adalci a tsakanin k.........

cikin b'acin rai Nasrim tace'' shikenan Ummu nagode".

Ummu bata gamsu da yanda Nasrim ta amsa abin ba gashi kuma gaban ta dare ne komai zai iya faruwa dan haka sai
tace'' ko za muje ki kwana a part dina gobe sai kizo".

murmushi Nasrim tayi tace'' lah Ummu ba komai ba abinda zai faru insha Allah".
"Ummu tace'' Yawwa Nasirisiya ta Allah yamiki al'barka."
bayan fitan Ummu Nasrim kicin ta shiga kwalin wuk'a ta dauko sai da ta zabi adda wanda yafi kaifin da tsini ta dauka ta zaga baya ta fara gogawa ajikin wani dutse ahankali take gogawa Khafulan da yake sama yana cire uniform din islamiya ya hango mamyn tasu a baya yace "kai bro gata can tana wasa adda ko Abbamu zata kashe muguwa ce".
Fayyat ya lek'a yana kallon ta yajuyo ya kalli Khafulan yace " mamy kake cewa muguwa Allah idan nagirma sai nasa an daure ka kullum kanayi wa mamy rashin mutumci".
"Eh nayi din karama mata mana ai itama batason Papa na bayahude take ce masa".
Fayyat yace "to tafada din".
shima Khafulan yace
"To nima na fada din daga nan suka kama kokuwa Allah yatemaki Fayyat shima yana da k'arfi dan haka dai dai suke karawa Khaldum ne dama bawan Allah ba ruwan sa

A office ko Agrif sallahn azahar ne kawai ya tashe sa bayan ya dawo daga sallan ya d'auki wayan sa ainda ya ajiye tun zuwan sa bai ma tsaya duba yawan Miss call da message din ba yasan Nasrim baza ta kirashi ba sai wannan na cacceciyar Izza tsaki yayi yana kashe wayar gaba daya batare da duba cikin saba ya maida ya ajiye sai asannan yafara aikin sa shine har sha biyun dare tukun ya tattara tarkacen sa yarufe office din ya fito yasamu drive komai akasalance yakeyi Allah Allah yake idan yaje gida yasamu Nasrim tayi bacci

Nasrim ko tasake hawa dam duk atunanin ta Agrif yana wajen Izza dan Izzan ta sake daura wani sabon status da yake nuni da suna tare har tana ikirarin tare zasu kana a hospital din

Yana bude kofar falo yace
"Inna'lillahi Halima bakiyi bacci ba".?
"banyi ba sai na aiwatar da abinda nake son na aikata".
"Halima kin gane nima a cikin damuwar nake wllh bansan wani mafita ba da nasani da nayi nima inda akwai hanyar da za ayi nagujewa auren da nayi amma kemeye naki shawaran".
Murmushi tayi tace''
Ummmm huuuu maza kenan har Kai kana da bak'in magana ka taba kaiwa bayan magaruba a waje amma yau saboda masoyiyar ka tana asbiti shine kaje kasata agaba kuna daura status na cin zarafina wllh bani kuka tozar taba kanku".
"Status kuma wani irin status".
kallon sama da k'asa ta masa tayi dariya ta shige ciki shi kuma ya jefa kan sa kujera there'siter lumshe ido yayi yana "Lahaulawalakkuwata'lillah'billah" .
bayyi auni ba kawai yaji an yankeshi a hannu a firgice ya mek'e kafin ya Ankara ta sake yankan sa ahannu
"Halima Halima Halima."!!!!!!
ganin zata masa illa yasa ya yi kanta gadan gadan
Tana nunashi da wuk'an tana ja dabaya tace'' inde dole sai kayi auren nan to zan kasheka inyaso a fanshi ranka da nawa".
"Halima ki saurara ni wllh bani da niyar auren nan zan miki bayani".
ni wllh bawani bayanin da zaka min ba kace ko Rana da wata zasu dena haske sai ita ba".?

"yaushe na fad'a mezanyi da wata Izza da har zan furta wannan akanta".
"a bayyane kafada yanda duk duniya zasuji shine dan kazo gabana......
gani da gaske take yada Agrif yin waje da gudu itama biyo sa tayi amma Allah ya temake sa yafice yarufo kofan ta waje yasa annu a al'jihun sa yana zaro wayan ya kira Kamal a take Kamal yafito a nasa part din yana tambayar sa lafiya
Agrif nuna masa annun sa dayake jini yayi yace " kaga hannu na Nasrim ce tamin haka tana ciki wai sai ta kasheni".
Nasrim ta ciki sai dukan kofar take
Kamal ya numfasa yace " Agrif duk lefin kane ai ba ka kyauta ba ko zaka fara d'okin Izza kabari tazama matar ka mana amma wllh nima banji dad'i abinda ka aikata ba".

"me na aikata Kamal wani d'oki na nunawa Izza yarinyar da ko kirana ta bana dauka".
Kamal yace "status din da kayi da ita ba doki bane".
cikin mamaki da rashin sani Agrif yace " ban gane status ba" ?.
yace yana duba wayan sa yace karo da status din da bashi ya d'aura ba kuma a wayan sa "what!? meye haka Kamal wllh bansan dashi ba ni bani na daura ba wllh ni bani da wani hoton Izza a wayata meyake faduwa".
Kamal yace"ban gane ba ta yaya wani zai d'auki wayan ka ya d'aura maka status".
cikin gigicewa Agrif yace
"Wallashi Kamal ka yarda dani ba tare muke da kai ba yau kaga ma nayi amfani da waya
" a silent fa na sata".
Kamal yace" ai shine nima abin yaban mamaki ina zuwa nasamu Humairah tana kuka ita take gayamin ga abinda yafaru wllh ban yarda ba Saida ta nuna min na yarda".
"Kamal me nayiwa mutane suke son ganin bayana da matata".

ganin yanda jini yake fita Sosai a hannu Agrif Kamal yace muje hospital

bayan su dawo daga asbitin
nasrim ta gama buge bugen ta wullar da wuk'an gefi tana maida numfashi dak'er Kamal ya shawo kan Nasrim tayarda ta shiga bedroom din ta Kamal yaraka yana kwantar mata da hankali tashiga wanka Yana zauna tafito sanye da rigan baccin har sai da yaga ta kwanta yaja blanket ya rufeta yafita
shima Agrif din Kamal dinne ya rakashi bedroom din sa
Kamal yace"shikenan Haruna ta hakura har ta kwata ma kaima kayi kwanciyar ka amma dan Allah idan da matsalan kayi saurin kirana dan FURUCI Nasrim Yana bani tsoro

************************

" da a suba Nasrim tana farkawa taji gaban ta Yana wani irin faduwa sai kuma ta kejin buga kofa kamar ana kuka kuma kamar kukan yaran ta da ta gudu tayi d'akin nasu tana bude kofar taci karo da Fayyat da Khaldum a kwance cikin jini an musu yankan rabo sai bige bigen kofar batdroom din d'aki a ke jitayi komai ya tsaya mata ahankali tayi kofar ban dakin tace'' waye aciki !"?

"mamy Dan Allah kar
ki kasheni na dena miki rashin kunyar wllh dan Allah kin kashe Fayyat da Khaldum !!!
"Khafulan bani na k'ashe suba dan Allah ka bude kaga yamin da kaske fa sun musu waye ya kashe su".

"Mamy kece kece da wuk'an da kika wasa d'azu kika kashe su bazan bude nima ki kashe niba".

Nasrim da gudu taju ya ta fita dakin Agrif nan ma me zata gani shima gaba daya an gama cakeshi da wuk'a juyawa tayi da gudu ikon Allah ne kawai ya kai ta part din su Kamal tana cewa ya Kamal sun mutu da gaske ne!!! dan Allah ya Kamal me yake faruwa Kamal da yake zaune a parlou da carbi hannu agaban sa tazube summemiya
a gigice yace " suwaye suka mutu jin k'aran Kamal yasa Humairah fitowa da sauri Kamal yace " yau me zamu gani Nasrim kashe San kikayi da kugu Humairah da Kamal suka fita direct bedroom din Agrif Kamal yayi kanin halin da yake yasa ya fasa wani gigitaccen k'ara yayi waje da gudu haka Humairah ma
Mai ai'kin Humairah ne suka sanar wa mutanen gidan
dan Humairah wuk'a ta dauko tana ta faman sumbatun itama sai ta kashe Nasrim tunda takashe mata Dan uwa itako Nasrim asume ma take bata masan me take ba duk masu ai'kin Humairah suke rike Humairah

gaba daya gida ya rikice
tun ba asan mutuwar su Fayyat ba mommy ce ta gano basu awajen tashi tayi ta shiga dakin fitowa tayi tana nuna d'akin da yatsa tana cewa
"ku shiga nan kuga".

Khafulan sai da yaji muryar su Abbaty ya bude kofar yana cewa" wllh mamy ce mamyn muce ta kashe su
kafin kace me har yan sanda sunzo Nasrim da take cikin wani hali suka dauka zasu saka amota mommy ta rik'e ta gem tana kuka "wllh ba Nasrim bace wannan wani mak'ircin ne aka kulla mana wllh Nasrim baza a iya kashe mijin ta da yaran ta ba" .

Hajja tace'' idan ba ita ba waye ba gashi Khafulan ya fada ba kuma jiya agaban kowa tace sai ta kashe daya acikin ukku tace rigiman duniya dame rai akeyi ".
cikin kuka me tsanani mommy tace "abin ya hau kan *FURRUCI TA NE*
Khafulan yace "wllh mommy itace da wannan kayan na jikin ta ta shigo ni ina batdroom zanfito na ganta tana kashe su har na mata video kashi nan ma dama papa yace duk abin da zatayi na mata video ".
yan sanda ne suka karbi wayan hannun Khafulan suka hada Nasrim suka fita da ita mommy tana kuka tace'' na sani duk mak'irci ne wallahi wallahi inde Ina raye kuma kudi suna magani a duniya Nasrim ko furzin ba zatayi ba ........

*Tofa masoya sai kunyi hakuri fa dama sunan litafin rikicin babban gida nasan pg yau zai ba k'anta ranku kamar yanda nima yau dag'er nake typing amma ya muka iya wannan shine jigon labarin*
Chapter 44 · 0% Book details