← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 100

Sashe 33

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasir da yake shigowa ya k'arashe mata maganan da cewa "in yaso nayi abin da zanyi ko?
Yana kallon cikin idon Hajja ya zauna a kujeran da yake facing da ita
yaci gaba
"ni Nasir zaki yankewa hukunci Hajja kinsan abin da kike fada kuwa? ni d'an kine ubana kika Haifa bani ba kuma yanzu yana ina bayanan dan haka Allah da ya hadamu yaraba ikon ki da isarki ya tsaya a iya yaran ki da su Aiban da suka ga zasu iya d'aukan amma ni
ni nake yankewa kaina hukunci rayuwata ce idan naso na kwana da mata dubu meye naki baki da Lada baki da zunubi kuma ba kabari daya za abunne mu ba kin zauna sai zafgawa mutane iko kike ai ba mommy zaki aika wajena ba ni ya kamata ki kira kisa idon ki cikin nawa ki gaya min ni bayahude ne kiga aikin yahudawa...
Abu ne yayi k'arfin halin dakatar dashi haba Nasir Hajja fa uwace agaremu idan ba idon uban ka ai mu gamu bamu can canci kazauna kana fadan haka a gaban mu ba...........
da sauri ya katse Abu da cewa
"saurara Abu ina mutuk'ar jin nauyin ku kai da daddy amma bana son ana shiga rayuwata zan iyayin komai me yasa da Hajjar take fadan magan ganun a kaina bakayi mata magana ba yanzu zata bude baki tacewa d'an ka Agrif bayahude ne agaban ka ko zata ce masa mazinaci saboda ni ba ubana bata shayin komai Kai tsaye ta furta min duk b'atan cin da yazo bakin ta...
duk kowa yayi shiru yana sauraron sa ko kyakkyawan motsi bameyi sai Nasrim da tunda yafara take zaf ga masa wani irin harara kasa daurewa
tayi cikin b'aci rai tace'' Abun kake gayawa magana haka wllh mutum idan bai daraja iyayen mu ba muma bazamu daraja shiba idan kai ba bayahud....
da katar da ita Agrif yayi da cewa " kece me baki ki bari ya gama wannan alama ne da yake nuni da Koda uban sa Abdulsamad yana raye zai iya c.....
bai k'arasa ba yaji wani irin sauk'an mari a fuskan sa cikin b'acin rai
Abu yace " lalle Agrif a gabana kake K'iran sunan dan uwana wannan yazama na farko kuma na k'arshe...
dafa k'unci Agrif yayi yana kallon Abu shi tunda yake Abu bai taba daura hannu akan sa ba sauk'owa yayi k'asa yazuba guiwowin sa cikin sanyi murya yace"Abu kayi hakuri wllh ban fadi haka dan naci zarafin Abba ba sai dan dakatar da Nasrim dan nafi kowa sanin waye Nasir
amma dan Allah kuyi hakuri".
Hajja tace'' bawani kai yanzu Agrif a gabana kake kama sunan Abdulsamad yoko uban ka Abdulrahaman ya isa ya kama sunan Abdulsamad kai tsaye kowaye yamuku Kai Yana dawa kuke fantamawa k'unci kun batse da gumin sa shi yaje ya kwanta dama bazaku ambace shi da al'kairi ba sai Sherri ni kullum d'ana da al'kairi nake ambaton sa..
nan ko Hajja tafara zagin Agrif duk haushin Nasir ta huce akan sa daga k'arshe Abu yabata hakuri dak'er ta hak'ura
Nasir ya doka tsaki ya fice

********************
Nasir yana zaune abakin gadon mommy tana ta shirya masa kayan tafiyar sa dan yanzu ansamu cigaba a nasiyar da mommy ta masa yadena yawo da mata sai da tagama hada masa kayan tazo ta zauna a kusa dashi tayi shiru tana son tayi masa magana tana tsoron abinda zai biyo baya
gane hakanne yasa ya ajiye wayan hannun sa ya fuskan ceta sosai yace "mommy akwai damuwa ne?
numfasawa tayi ta gyad'a kai".
"kamar na me ba?".
numfasawa tayi tace
"my son dama akan maganan Hajja najiya ne my dear nima gaskiya burina kenan naga kayi aure kaga fa Aiban kanin kane amma yanzu matar sa har takusa haifuwa Agrif sa'an kane yayi aure Kamal sa'anka ne yayi Ayman Ramadan aliyu duk abokan.......
"da kata Mommy wai meye naku na sai nayi aure ne? Ummm duk su Wanda kike lisafamin zuciyar mu daya dasu ko ra'ayin mu daya ne wai meye acikin auren banda bak'in ciki da damuwa gaskiya mommy kiyi hakuri ki dena min wani zance aure kawai ki din gamin adduar idan Allah yayi zanyi zanyi".
"shi kenan my Son".
tayi maganan cikin sanyi murya
Nasir jikin sane yayi sanyi bayason ganin mommyn sa cikin b'acin rai
hannuta yakama yace' mommy ki kwantar da hankalin ki inde aure ki ke so zanyi kuma ko banyi ba kin kusa rike jinina insha Allah".
arazane ta ware idon ta akansa tace'' ban gane ko bakayi aure ba kuma kace na kusa rik'e jinin ka?".
murmushi yayi yasaki hannu ta yana mek'ewa tsaye zaunar dashi tasake yi cikin raunen niyar murya
tace'' baka ban amsa ba Nasir kamin alk'awarin bazaka aikata Zina ba fa".?
"Mommy kenan ai shi halin mutum saka riga yacire yafishi wahalan canzuwa".
" cikin in nina tace'' Nasir kana nufin kazama mazinaci".
"kai mommy bincike fa haramun ne kisa a ranki nayi so daya ko biyu kuma yazama na k'ashe amma mommy dan Allah kimin addua Allah yamin maganin damuwata".

Mommy mek'ewa tayi tsaye tace'' nashiga ukku ni Fanna Nasir nasan Kai ba mak'aryace bane mai fad'an gaskiya duk d'acin sane amma ban sanka da karya
ba me yacanza min kai".?
ganin mommy cikin damuwa yace "Kai mommy idan baki sanni da k'arya ba ai kin san ni dayi miki wasa bazan taba zanzawa ba aure zanyi insha Allah".
ajiyar zuciya mommy ta sauk'e tace " Al'hamdulillah wllh har kabani tsoro".?
"ammm mommy da Baba Nasuru fa zan tafi akwai wani likitan kwakwalwa kwararre ne da namasa bayani yace " in kai shi ko za a dace".
cikin jin dad'in tace''yawwa my Son dan al'barka Allah yasa adace burina kenan naga suwaye iyayen Halima".
"Ameen". Yace
tare da fara tafiya mommy ta dau jakan sa dawasu tar kacen sa ta tafara binsa abaya
sai da suka fito babban parlou Zahira tayi saurin k'arban kayan hannu mommy ganin har ya doshi parking space yasa mommy tace'' my Son ba zakayi sallama da mutanen gida bane bama ku gaisa ba ai tun da baka fito breakfast ba ".
dan yamutsa fuska yayi sai kuma yayi part din Ummu ita kuma mommy ta zauna a compound jiran sa
cikin takun sa na isassun maza ahankali ya murd'a handle din bakin sa d'auke da sallaman na nasa naciki ciki Wanda bakowa ne yakeji ba balle a babban falo irin wannan Agrif yagani da Nasrim suna baje akan kujera there'siter cup ne ahannu sa da cokalin a ciki yana kaiwa bakin ta
kallo daya yayi wa Nasir yajuya yana iban kunun madara me kauyi yana kaiwa bak'in Nasrim juya kanta tayi cikin shagwaba tace'' Allah Yaya nide ciki na zai fashe ".
" Please my Honey daga wannan shikenan".
"to nide sai kamin alk'awarin zaka shafa turaren first night din nan Allah wancen bashi bane".
Agrif dan juyawa yayi yana kallon gefin da Nasir yake a tsaye kamar ma bai san da suba nanko kunne sa yana wajen
ya juyo yace " idan kina tare dani baki da damuwa zan shafa".
dariya tayi Wanda yasa kumatun ta duka lomewa ta wangala baki shi kuma ya zuba mata
murmushi Nasir "yayi afili ya furta zanyi maganin ka yanzu".
yanda bazasu jima
Yakalli me'aikin Ummu da take ta jera masa sannu yace' Ummu fa".?
cikin in nina tace'' tana falon sama".
cikin sauri ya fara hayewa steps din Ummu tana zaune ana saka mata lalle ak'afa tana ganin sa ta washe baki tana cewa " d'an mommy shirin kenan".
zama yayi kusa da ita cikin ladabi yace " Ummu zan tafi".
" to Nasara ko gani kafi mutum sai bayan shekara ko ".
murmushi yayi yace " gamu nan de".
ya k'arashe maganan yana mek'ewa
ita kuma Ummu sai fatan alkairi take masa har zaifita kuma sai yajuyo yace' Ummu dan Allah kiyiwa Agrif magana yafara wasa da aiki har nayi mai magana bai jiba yanzu tare yakamata mukoma amma yace a a".
Ummu tace'' Zainab ba kince Agrif yana falo ba kiramin shi

"baka ban amsa ba meye dalilin ka na wasa sa aiki".?
shiru Agrif yayi a zuciyar sa yace tanan kuma ka bullo
afili kuma yayi saurin cewa "Ummu kiyi hakuri Nasrim ce bata d'an jin dad'in kuma gashi tana buk'an tan temako na".
jin jina kai Ummu tayi azuciyar ta tace gaskiya ne tunda ana auren yatafi yanzu kuma gashi ko sati bayyi ba yakoma zai iya shiga hakki ta gaskiya amma ya suka iya badan makaran ta ba da sai suna tafiya da matan su afili kuma
tace'' hakane sai de kuyi hakuri na dan lokacine idan sun gama makaranta kowa yana iya tafiya da matar sa .
ta kalli Nasir ta cigaba to Nasir kaji uzurin sa amma hakan bazai hanashi tafiya ko da zuwa gobe ne ba tunda yanzu bai Shirya ba goben ya bika".
Nasir bai so hakan ba yaso yatafi k'afar sa k'afar Agrif yanzu idan ya kyale shi tunda yau baya nan Agrif zai iya kasan cewa da Nasrim amma a afili kuma yace"shikenan Ummu amma daga goben kar ya kwana anan akwai aiki acan yayi maganan yanayin gaba ko adawo lafiya masu aiki da Ummu baya amsawa a falo ya tarar da Nasrim tana bacci kallo daya yayiwa wajen ya fice
Azuciyar sa yana cewa yanzu zaki huta na dan lokaci kafin ki haifamin yaro na insan matakin d'auka akan ki
Chapter 33 · 0% Book details