← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 100

Sashe 14

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakatar da shi mommy ta yi da cewa "ka gaji da irin wannan halin nawa kace ko ? Na ji ka gaji za ka iya daukar matakin da ka ga za ka iya amma inde akan Nasir ne Wllh baka isa ka ce min ba ni da iko a kansa ba ko ka fi ni iko da shi ba".
har zayyi magana yaga yanda yatsan Nasrim ya kunbura sai yanzu yakula da ashe daya yasan ma rawa yake alaman ya karye cikin wani irin razana yace "Dr Fanna ya karyata fa".
"E, na gani ya karyata naka ka sani ai, yanzu ka san halin da shi Nasir yake ciki".
Cikin sanyin murya daddy ya ce "Dr ki zo mu je a kai ta asbiti ba lokacin wannan maganan ki duba halin da y'ar nan take ciki."
Ya k'arashe maganan yana karban Nasrim a hannun Harira
"kai me zai hana ka kaita".
tana gama fadan haka tayi part din Hajja
wani irin hawaye ne ya surtowa daddy yana na kallon Nasrim da sai yanzu ya gane a sume take ga yatsa yana rawa. Ya rasa ma ya zai yi Habu drive ya ce "Alhaji mu je asbitin" Shiga yayi motar kafin driver ya ja yana cewa Baba Yakubu dan Allah
"Yakubu ka cewa Aisha ta same ni a asbiti yanzu".

********

Mommy tana cikin lallashi ta ce'' my Son ka ji mata ciwo fa sosai amma na san Abu ma sai ya yi maka fad'an dan haka idan ya tambaye ka ka ce kai ba ka sani ba ka taka kar kace wa Abunku da gan-gan ka karya ta ka ji".
cikin dafe kansa da yake jin yana masa ciwon ya ce
"No Mom ba zanyi k'arya ba ina sane na taka ta ai dama na ce kar na sake ganin ta kuma dan raini har fa kamani tayi wllh na zaci watace har daukan ta fa na yi Allah ba zanyi k'arya ba da gangan na taka ta shi ma Abun haka zan ce masa".
Mommy tace'' wannan ba k'arya bane kare kai ne nasan Abu zai maka fada ko ya dake ka kamar yanda daddy ya yi".
Cikin kawar da maganan yace mommy kaina ciwo yake min Agrif ya buga min glass Dad ya mare ni''.
"Ok sorry my son mu je hospital ko".
ya ce "Na mommy ba sai mun je ba ki ban magani kawai".
Mommy tace''ok ka sha sai ka kwanta ni kuma zanje na dubo Nasrim an tafi da ita asbiti"?
turo baki yayi yace " wllh mommy ba za ki ba ai a kanta aka dake ni".
" OK my Son ba za ni ba".
Hajja da take sauk'owa daga steps ta tabe baki tace'' au dan ita yar gata ce har asbiti aka kaita daga dan takawar ummmm gata ni Lami yar Habubakar amana yayi k'aranci har agabana Abdulmajid zai nuna bambanci ga d'an Abdulsamad dan Adam kenan mai manta alkairi".
Ummu da take kallon karfin halin su ta kasa jurewa ta ce
"Haba Hajja! ina Nasir ina Nasrim ai ba sa'annin juna ba ne kuma abinda ya yi ai....
Hajja ta ce
"Dakata Amina ni bana ciki da rashin gaskiya ai shi maraya ne ko ma me yayi ai a masa kara ko dan darajan ubansa" .
daga nan Hajja ta kama fada har da gayawa Ummu magana son ranta.

********

Agrif da Mama da Kamal ne suka tafi asbitin lokacin har an shiga da ita za a mata aiki daddy suka samu a zaune yayi tagumi Mama ce tace'' Alhaji kayi hakuri insha Allah zata..
bata k'arasa ba Dr yafito da saurin sa yace '' ranka yadade kayi sauri ka saka mana hannu za ayanke mata daya yatsar duk biyun kayara ne amma daya zai gyaru daya ba zai gyaru ba dole sai dai mu cire mata dan k'ashin ya riga yayi daga-daga".
wani irin kuka Agrif da kamal suka sa haka Mama ma shima daddy cikin hawaye yace "A'a ina da d'an uwa da mahaifiya bari na gaya musu kafin nasa hannu na ji ta bakinsu. Hajja ya fara kira yana gaya mata ta sa kuka ta ce
" Abdulmajid abin har ya kai haka wllh ban yarda a ciremin yatsar jika ba gani nan zuwa".
shide katse K'iran yayi yana kiran
Alhaji Abdulraham shima Abu ya ce"subbahanalla gani nan zuwa ina cikin makaranta".
yana kashe wayan ya dafa kai ahankali yake fitar da numfashi
Dr ya ce "sir please aikin yana buk'ara gaggawa bawani abu bane ake cire hannu ma gaba daya balle dan
Fingers".?
Takardar daddy ya karba yasa hannu
Mama tace'' Doctor please bawani hanya da za a bi dan Allah ko da waje ne a fitar da ita ba mason a yanke mata yatsa".
Dr yace "Madam nasan kunfi karfin hakan to wannan k'addara ce bayan da za a yi yatsar ya koma jikinta ya riga ya bar jikinta fatar kawai za mu cire shi yatsar ya riga ya fita ma".
Kuka sosai Agrif da kamal suke yi

Abu ne ya fara zuwa amma lokacin ma har an fito da ita har ankaita d'aki Mama tana zaune a bakin godon daddy kuma akan kujeya ya sa dan yatsar da aka mek'a masa acikin wani kwali gaba Kamal da Agrif har yanzu kuka suke Abu yace "wai me ya faru ne?"
Daddy bai yi magana ba Kamal ne ya bashi labarin komai ajiyar zuciya ya sauk'e ya ce
"Kayi hakuri alk'ali Allah ya k'addara hakan zai faru da ita shikuma Nasir insha Allah suna gama jarrabawar ba za su jona na secondary a nan ba nan da wata 3 za su tafi America kafin su gama ya yi hankali dan a nan Dr Fanna da Hajja su suke biye shi.

********

Sai da Nasrim tayi kwana biyu a asbiti aka sallame su Hajja da Mama sune a kanta ta amma mommy bata ko lek'o ba dan ita a ganinta ita aka yiwa babban lefi an yake mata yatsan y'a bata reda neman izinin ta ba tafake da wannan amma azashiri Nasir ne ya hanata zuwa
dak'er Hajja ta tarasu ta basu hakuri duka. Amma tun daga wannan lokacin Nasrim ba ta sake komawa wajen mommyn ba shi ne dalilin yaye ta
bayan wata 5 tafiyar su Agrif saura sati
yau ne aka gama tattare duk wani dukiyar na Alhaji Abdulsamad akasan yawansa yasa yayiwa daddy yawa dole aka yayyato wasu alk'alai kuma duk wannan shekarun anyisane cikin tattare dukiyar alk'alan su zaga dukkan k'asashen da marigayin yake da company ko dukiyar bayan cire tumilain mommy da hakki mahaifiya Hajja aka rabawa yaran sa guda ahudu wato Nasir da jariran mommy wanda daga baya aka hadewa mommy na yaranta.

Tabdijam ! mommy ta tashi da kaso 80 cikin dari na dukiyar daga baya tace" ita a haɗe nata da na Nasir ba abin da za tayi da wannan dukiyar itama Hajja a take ta raba nata gida biyar ta bawa danginta da na mijinta kaso daya su raba daya kuma ta baya Abdulraham daya Abdulmajid daya daya tace' a bawa Nasir ta bar masa halak malak marayane daya tace za amata aikin Allah sadakatun jari'a yan uwan ta dana mijinta dama suna wajen atake sukace saide mommy ta fansa tunda company ne dama kuma ba ma a Nigeria suke ba mommy sai da ta nemi shawaran Nasir ya yarda tace'' to ta bansa atake tatura musu kudin su ma daddy da Abu cewa sukayi ta fansa dan suke gani kamar hakan zaifi musu sauki dan company nin da Abdulsamad ya mallaka musu na ashana ma bawani iya rikeshi sukayi ba daga k'ashe shima mommy suka saidawa
Yanzu de dukiyar gaba daya yazama na mommy da d'an ta

*bayan shekara biyar*

A wannan lokacin su Nasir suna level 2 a university a k'asar Americans, Aiban kuma bana za su gama secondary shida Abbaty d'an shekara shida a duniya za su shiga primary 3.
Misalin k'afe biyar na yammacin Lahadi hadirin ne sosai yake shirin tasowa daddy kwance a bayan motarsa, ya kalli gefen islamiyar su Nasrim ya ga yara sai fitowa suke wasu an zo daukar su wasu kuma da k'afa suke gudu ya cewa drive Kabiru mu shiga mu mudu ba ko ba azo daukar su Nasrim ba ga hadiri na shirin tashi ko''.
"Kabiru yace ok sir". yayi reverse ya shige ciki.

Nasrim ta lek'o ta window tace "wai Humairah baki gama rubutun ba wllh nide zanbi motar gidan su Ameera ga hadiri kuma yaufa bro Agrif da ya Kamal zasu zo nasan ma yanzu sun zo bama nan kum....
shiru tayi jin Amira tana cewa
"La Nasrim ga motar daddy ku a dai-dai lokacin kuma Humairah ta fito da sauri suka k'arasa gun mota Kabiru ya fito ya bude musu baya suka shiga Humaira ta ce'' Daddy "Ina wuni".
"Lafiya my dear ya karatun".
Ta ce muna yi daddy yace madallah".
ya juya yana kallon Nasrim da take ta faman turo baki yace
"Ya de my sweetheart".?
cikin shagwatar ta tace'' Daddy ba suya Ya Agrif bane zasuzo amma Mama tace wai sai munzo makaranta ina ga ma sunzo yanzu".
"Come down my dota kin manta yau birthday dinki ki daina ɓata rai Agrif ya kawo miki tsaraba da yawa kuma ya ce ba zai kunce ba sai kin zo"
Ihun dadi ta fara dai-dai kwanar da zai kaisu gidan su ne suka samu wani mutum da wata yarinya dakuma wata mata a kwance an rufeta da wani yadi da buzaye suke nad'awa mutumin sai kuka yake yana sake k'enk'eme yarinyar da bazata wuce sa'ar su Nasrim ba Nasrim tace daddy ka ga wasu mutane a waje ruwa yana musu duka mu tsaya mu dauke su daddy".
Sai a san'nan daddy ya juya ya kalli gefen da take nunawa ya sa Kabiru ya tsaya daddy ya leko kai yace" lafiya malam kuke zaune anan ana ruwa wacece wannan a kwance cikin matsanancin kuka mutumin ya d'ago ya ce matata ce ta mutu..
Chapter 14 · 0% Book details