← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 100

Sashe 18

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

karfe Sha biyun rana jirkin su Agrif zai sauk'a amma tun sha daya Nasrim ta azalzali Bala drive ya hada mata kan direbobi da bodyguard su tafi airport kada ya sauk'a yayi jira ta higa ta fesa wanka tabdi aiki awajen make-up aka bata lokaci
kalliyar ta single ba wani hayani ya amma tayi kyau sosai Nasrim wankan tarwad'a ce wato kalan chocolate Allah ya bata baiwar kyan fata gashi ya hadu da hutu ko macce k'arya take tayiwa Nasrim kallo daya bata sake ba ko Izza da take fara sol farin buzayen asali ba takai Nasrim d'aukan hankali ba haka fuskan ta tako ina acike yake ba wani tayani muni ko kumatu shi bayyi fadi ba shi bayyi siriri ba haka hancin ta ba siriri bane can amma amek'e yake san bal haka jajayen leben ta wanda yake a tsuke ya samu kyakkyawan zama kamar ita ta zana
abinda yafi zaukan hankalin mutane fiye da komai atare da Nasrim idon ta duk da basu fiye girma ba amma farare ne sol me d'auke da dogayen gashi a sama da k'asar su gashi ta iya sarrafa ido sosai yanda take k'adasu da juyasu idan tana magana zaka zaci tsabar yan gane da iyayi nan ko halittar tace a haka tun tana yarinya kullum da safe Mama sai ta tofa mata La'ahwaula a idon ta Nasrim tana da zanen nen gashin gira siriri wanda inba wanda ya santa ba zaice concealer take zanawan dan bawani karkata a setti yake sai kwanceccen sajen ta wanda yazo mata har kunne ta tana da cikar gashi da tsawo
bai war Nasrim na jan hankalin mutane bai tsaya anan ba Nasrim macce ce ta sama da k'asa heeps din ta awani irin mulmule yake ga tozo ko ya take tafiya sai sun motsa shiyasa Mama take yawan cewa tasa shijab duk da de tozon sa a cikin shijab ba yana fitowa gata bata fiyye son sa shijab ba ita manya kaya ma takurata suke kullum suna cikin fada da Mama akan sa k'ananun kaya
boops dinta acike suke dayake bata da jiki sosai girman su yake fitowa har takurata yake mutane suna neman k'arin heeps da boops ita tana neman rage sa so dayawa tana cewa Mama ita a nemo mata maganin rage girman heeps da boops musamman idan anyi bak'i maza Mama tana kula da yanda idon su yake kan Nasrim koda yaushe ahankali take tafiya wai Dan kar su motsa amma sai de idan bata motsa jikin taba dan sai sun k'ada komai na Nasrim me kyau ne
Zahra ce ta shigo ihu tayi tana cewa "kai Nasy kingan ki kuwa".
sake kallon kanta tayi a mirror tayi murmushi tace yawwa "Zar dan Allah kizo ki zabani kayan da yadace dani nasa doguwar riga yar Dubai da saudia da sinigal yafi kala goma duk basu min ba gashi Mama ta hana ni saka English wears kawai atakura mutum da manya kaya"..ta k'are maganan tana turo baki
dariya Zahra tayi tace "mu meyasa bata hana mu ai yanayin halittar kine ya janyo miki shi yasa a kullum nake taya Ya Agrif murna wllh yayi mugun tsintar dami akale wai ni da ake cewa mutum tara yake bai ciki goma ba to ni kullum tambayar da nakewa kaina ke meye naki bai cika ba".
kallon ta Nasrim tayi tana cire yatsan roban da yake hannun ta tanuna mata tace "kinga abin da bai cika ba kuma bayan shima akwai da yawa".
Zahra ta kalli hannu tace " wllh bayan shi bawani abun in kuma akwai nuna".
murmushi Nasrim tayi tana maida yatsan kan manu niyar yatsan ta na hagu tace'' yanzu de time ya kusa ki ki bani shawaran".
Zahra tace'' ni wanne ma zaki sane yawwa kisa wannan
Swice lace din nan wanda mommy ta siyo mana a Dubai yellow ki d'aura masa wannan blue after idan bayyi ba sai mu duba wani".
hakan ko ahayi sosai kayan ya mata kyau Humairah ta shigo tana ganin ta tafara mata wak'a ayee riii zobiya naira zo biya naira zalla Yaya na kaji dadin ka".
juyi Nasrim tayi tace '' nayi bazai kushe ba".
Zahra tace'' wane shi ni ina tsoron ma ki masa kwarjinin da zai kasa cewa yana So".
take yanayin moment dinta ya canza
ta juya tana d'aura agogon ta na farin gol
Humairah tace'' ke wasa take miki kisa aranki za abaki wanda ki keso".
"bana son irin wannan wasan ai ni yau kam ko bai furta ba ni zan furta wai ni yawwa Ina Izza ta shiga yau ".?
ta k'arashe maganan da tambaya
Zahra tace'' ai jiya da taje wajen Baban ta bata zo da wuri ba har mukayi bacci ina ga ramuwar baccin take".?
tabe baki Humairah tayi tace'' can ta matse mata ba wani bacci da take shegen zurfin cikin na ta ne ya motsa tana nan akwance sai juyi take ko breakfast bata fito ba".
dama Nasrim tun asuba tabar d'akin data gama kuma direct dressing room ta shigo
basu Ankara ba suka ji tsayuwar motocin
da sauri Nasrim ta k'arasa jikin window tana ganin drive ya fito ya zaga ya bude back seat din wani irin dafa k'irjinta tayi tana jin yanda yake bugawa kamar tayi fuka fuki ta dira ta finciko sa take ji shiko kamar yasan tana jiran sa sai da yadan b'ata lokaci ya ziro k'afar sa daya wanda yake cikin b'akin socks me shak'i sake ziro dayan ma yayi daga nan kuma ya mek'e gaba daya yafito da gan-gan jikin sa wow ba Nasrim ba ko wacce macce dole ta so wannan guy din dan bashi da makusa sa ta ko ina dogone b'aki amma ba bak'i can ba kalan fatar sa irin na Nasrim ne har kusan kaman suma suna yanayi sosai kusan duk gidan sunfi kama dashi da ganin yanda fatar sa take shek'i kasan ba k'ananun kudi ake kashe masa ba bakin kilas ne a idon sa saide yanayin sa ba kamar na da ba yau ba far'a'an nan da haba haba da mutane kana ganin sa kaga me damuwa Baba Yakubu ne yafara masa kirarin da yasaba yace "barka da zuwa Alhaji Haruna sarkin tsafta Haruna kan d'aki bane hannu daya ya dauka ba a kaida d'a nabiyu a gidan 3.A. full nd'ororo an baka kabawa yaran baya Haruna kafi k'asan randa yawan wanka kai jarumi kake meson mutum kake".
hannun kawai ya jinjina masa ya fara takawa wanda da dane yadin ka wahe baki kenan yana nagode Baba Yakubu dan ko Nasara idan baba Yakubu ya fara masa kirari sai yasa shi murmushi balle Agrif sarkin fara'a ahankali yake takawa
Nasrim tayi saurin damk'e hannun
Zahra da hannun ta daya dayan kuma ta dafe k'irjin ta tace'' Zar gaba na faduwa yake"!
Zahra tace''
"Kinji kifa meye abin faduwar gaba bayan gashi gaki yazo lafiya zo musauk'a ya shigo".
Nasrim tace''kema kinsan part din Hajja zai wuce kibari sai ya shiga sai muje".
Agrif direct part din Hajja ya wuce kamar yanda al'adan gidan yake duk wanda yazo daga tafiya a nan yake sauk'a tun kafin ya k'arasa shiga parlourn ya fara rage suit din sa yarik'e a hannu sai farin riga da yabari
Hajja tana zaune akan wani lallausar kilishin ta idon ta cikin farin glass ta sunkuyar da kai tana karatun wani littafin da yagama tafiya da hankalin ta k'afar ta akan tum-tum Barira tana shafa mata man zafi ya shigo ciki-ciki yayi sallaman dan haka ba wanda yaji balle Hajja da tayi nisa a karatun ta har ya k'araso ya cilla kansa kan kujera there'siter bata jiba sai da Barira tace" barka dazuwa yallabai Agrif".
hannun kawai ya d'aga mata
sai asannan Hajja ta d'ago ta kalleshi ta tabe baki tace'' zama da mad'aukin kanwa dama ance shiyake kawo farin kai karasa halin d'auka sai na wannan bayahuden sallama ya gagare ka Haruna".
ta k'arashe maganan tana cire glass din idon ta tare da ajiye littafin
tsaki yayi yace". ko nayi sallaman amfani me zai miki dan Allah Hajja me kike nema a duniyar nan ne yanzu littattafan addini yaka mata agani a hannu ki ba wai novel ba ko mu jikokin ki bama karantawa".
"Haruna ka kiyayeni kar kaga ina raga maka saboda girman sunan ka awajena haka nace maka bana karanta littafin addini kalli can duk sune yoni ban dama Hajiya sabuwa tacemin littafin yayi dadi da ma'ana Wllh rabona da nayi karatu har na manta idan bana addini ba".
sake jan tsaki yayi yace kinji fa Hajiya sabuwa fa baza ta wuce sa ar Ummu ba amma da ita kike k'awancen karatun litafin soyayya".?
Chapter 18 · 0% Book details