← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 100

Sashe 71

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yashiga ɗakin sa yafito
da kudi ahannun sa zaikai kimanin dubu ashirin da biyar
yace " gawannan kayi guzuri dashi nasan bakason ruwa haka kar ka galabaita kafin kasamu wani sana'ar natara wannan kudinne saboda na biya Alhaji kuɗin hayan sa dubu tabanin ne ba yawa bai haduma kuma gashi gida yazama nawa ka karɓa".

Nasir hawayeni ya taru a idon sa wai yau shine akeyiwa yauta da dubu 25 da sauri ya maida hawayen yasa hannu biyu ya jarɓa yayi godiya

Mama da take ta kuka itama tayi saurin shiga ɗaki tafito da kudi ahannun da batama san yawan suba zasu kai ƙimanin dubu arbain tace nima ga wannan Ahamed kanemi sana"a haka Umma duk yaran gidan saida suka dinga fasa asusun su na cewa Yaya gashi yaya gashi zuciyar Nasir yagama karaya kanin yanda yaran da iyayen suke kuka suna meƙa masa kuɗi bai san sanda yazu ɓe gwuwowin sa a ƙasa ya rungune autan Malam ɗan da bafi shekara 7 ba sa'an Khafulan da yake ta faman meƙa masa kuɗin yan biyar biyar shima ya fasa asusun sa rungume yaron yayi sosai yana kuka inama familyn sa ma suna sonsa kamar haka meyasa su sanda yace zai tafi bazasu sake ganin saba ko ajikin su har farin ciki ma yagani a fuskokin wasu daga cikin ƴan uwansa,
amma su wadan nan yace musu zai zoma suka shiga wannan tashin hankalin kamar anmusu mutuwa wani irin so suke masa inama zai iya zama dasu amma hakan bazai yuwu ba dole ya tsaya da ƙafafuwan sa kada lokaci yamasa nisa a hankali yaraba jikin sa dana auta Amir yayi kiss din yaro yana meƙewa ya karfi kuɗin duk wanda suke meƙa masa ya zuba acikin jakan sa ya bi duk yaran maza yana haɗa hannu su,
matan yadinga musu murmushi yana kama sunan su

yace "ku cigaba da yimin addua zan zo insha Allah".

har yasa ƙafa zai fita Hamza yace Yaya ga waya dan mudinga jin lafiyar ka dan Allah".
ganin idan bai karɓa ba zasu shiga damuwa yasa hannu yaƙarbi wayan Hamza Cecno k9
yace "thank my brother".

yajuya yafita kuka sosai suka fashe dashi duk su bawanda yayi yunƙurin rakashi sai zubewa da sukayi a wajen

*to sis bay gidan malam ladan zamuyi missing gaskiya ni de har araina naji ina son gida ina ma akan su na kafa jigon labarin ba 3A ba*

********************

*Three brother*

dafe ƙirjinta tayi sosai tana sake mannuwa ajikin motan Usman wani ma aikacin sune yazo da sauri yace " subbahanallahi ranki shidade lafiya".
ya ƙarashe maganan yana tattara mata wayan ta da sauran tarkacen ta daya zube awajen
cikin ladabi yasake cewa "ranki ya dade mushiga ciki k...........
cikin wani irin tsawa ta katseshi da cewa
"bazan daɗe ba nace maka bazan daɗe ba mutuwa zanyi shi Agrif da yamutu baya shuta ba nima mutuwa zanyi menayiwa mutane ake tamin bita da ƙulli haka duk wannan shirin film din yanzu akaina aka shiryashi akan a tozar tani
bazan iya ba yara na ake shegan tawa".

a zabure ta meƙe shima Usman a zabure ya jada baya yana bata haƙuri dan a tunanin sa kansa zatayi da duka
direct part din Mommy wanda yanzu ita da Humaira nan suka koma ta nufa Mommy ma dawowar ta kenan a wajen aiki ta zube a parlur tana maida numfashi da Sauri Barira tayi kanta tana cewa " innalillashi rai ahidade meye haka"?.

cikin in ina Nasrim tace "Mommy Mommy ina Mommy Barira me nayi komai yake sauka akaina wai yanzu zargina ake da lefin aikata zina ni wllh ƙazafin zinan bai dameni kamar shegan tamin yara ba
ba mutum daya ba biyu ba kowa gori abin yafara isata duk wanda yazo yace yana sona idan ban amince ba sai yace kwartona nake jira waye kwarton nawa ......

Mommy da take sauƙowa a steps wani irin faduwan gaba taji kamar ta juya
"tofa ranan da ake gudu yazo" tace afuli

Nasrim meƙewa tayi idon ta yakoma ja sosai ta tako gaban Mommy ta kwashe komai ta gaya mata duk wanda suka mata wannan gorin ya d
taura da
cewa "amma nasan zargine gawai da sharri video haɗa wa akayi ai yanzu ba abinda mutum bazayyi dan yaga ya tozarta dan uwan saba wllh Mommy ƙaran Habib Usman Argugun zanyi inyaso duk abinda zai faru yafaru".

dafa kafaɗan ta Mommy tayi tace "pls my daughter ki nutsu bawa baya kaucewa ƙaddaransa kinji dan Allah kidena ɗaga hankalinki akan wannan yanzu anjima Abun ku yace zayyi meeting zakiji komai meye awajen kiyi hakuri".

"Mommy nayi hakuri fa kike maimaitawa kamar baki fashimci meyake faruwa ba ahegan tamin yara fa akeyi kawai saboda sunyi kama da Nasir harda hada video na ƙarya".

kama hanun ta Mommy tayi suka haura sama
Barira ce taje ɗakin Humaira ta gaya mata alokacin suna tare da Izza

girgiza kai Humaira tayi tace yanzu ya zamuyi sister".

nisawa Izza tayi
tace "gaskiya sis ni shiryawa zanyi na tafi gidan Zahra idan abin yalafa nadawo wllh bazan iya cigaba da ganin Nasrim ahalin da zata shiga idan wannan abu yafito ba kuma dama ko hakan bai faru ba Abu yace yau zai gayawa Nacy komai so bazan iya zama ba".

Humaira ta sauke ajiyar zuciya tace "banso taji awani gun ba dama ɗazu take cemin sunyi da Habib yau zanzo ita kuma gaskiya ta gaji dayi masa ƙarya tunda yanace sai yaturo zata gudu gidan Ameera to bayan yazo ance batanan sai yafita kamar wanda yatafi gaba daya shine fa nace tazo yatafi ashe bai tafi gaba ɗaya ba sai gashi yazo kafin na ƙirata na sanar da ita sai gata na hangosu ta window amma banzaci Habib zayyi haka ba kinsan mutum ne me zuciya kuma tun Nasrim tana budurwa yagama naci bai samu ba sai da nacewa Nasrim idan tasan ba auran sa zatayi ba ta lallaba su rabu lafiya nasan halin Habib sosai ko kamal hakuri yake dashi".

Izza tabe baki tayi tace " me ma zatayi dashi ai bai cika masoyi ba da yacika mosoyi ɓoye mata sirrin ta zayyi ba tona mata asiri agaban ƴan aikin gidan su ba
ai AGRIF shine cikekken masoyi abin so mai ɓoye sirrin masoyi."

murmushi Humee tayi tace " to ta Agrif zaki fara ko".

Izza tace "ba batun zan fara bane kema kinsan halinsa yayi arayuwa nifa ban taba ganin mutum mai hali irin nasa ba nifa ko acikin aljanna na bude idona na ganni da Agrif to nasan aduniya nayi abin kirki ni ko haka ma abani shi ba sai an masa wankan da akace anayi ba".

Humaira tayi murmushi tace" balle ma zaki samu wanda yafishi shegiya kuma ya Aiban ɗin gauro zaki barshi a la'hiran ".
shiru Izza tayi tana sauƙe ajiyar zuciya

Abu yabude taro da addua yace " Halima wannan zaman nakine danke muka taru anan Halima dan Allah ina son duk abin da zakiji ki daukeshi amatsayin ƙaddara wanda bawa bai isa guje masa ba Nasrim duk yanda zakiji abin inason kisa hamdala domin nawani ko wata abin yafi haka ƙazanta ke lawye ce duk da baki daɗe da fara aiki ba nasan kinci karo da cese sosai
dan haka
abin zai zo mana cikin sauƙi idan akayi la'akari da ke ɗin malamar addine ce inason kiyi amfani da illinmin ki da nusuwar ki kisani wani baya haihuwar ɗan wani watama uban da ya haifetane zai mata ciki kuma a haifi abin
wata yayan ta muharramin ta wata ƙanin Baban ta muharramin ta wani ƙani ko wan uwar da ta haifeta wannan abin tun munajin sa a nesa yanzu yazo ƙasar mu munji kuma mungani namu mai sauƙine Nasir ba muharramin ki bane ƙidaure kicigaba da karanta innalillashi abin kam da ciwo wanda ni kaina saida nashiga halin da kwana ne kawai ya tashi ni ciwon abin da zafin sa shiya hana mugaya miki tuntuni amma cigaba da ɓoye miki ba abin da zai haifar sai da nasani mumga misali aɗazu Halima ina me baki hakuri ki daure ba kanki farau ba kiyi hakuri ki daure ba Allah yana ƙinki bane ya dauramiki ina son ...........
shiru yayi yana tsunkuyar da kai
Humairah sarkin kuka har tafara Izza kam dama tagudu

cikin rawan murya Nasrim
tace "Abu meyake faruwa koma meye nasan yana da girma tunda har kayimin wannan jawabin nifa musulmace zan dauki dukkan ƙaddara kamar yanda kace RABBI BAYA DAURAWA BAWANSA ABINDA BAZAI IYA BA dan Allah kugayamin".

Daddy share hawayen sa yayi haka Abbaty ma Hajja ma harda jan majina ita Ummu ko tashi tayi cikin sauri ta fita

Abu yafara tundaga yaran da Nasir yayi mata rapping har zuwa haifuwar yaran ya daura dacewa

amma duk ba lefin NASURU bane AIsha ce tayi bokan tane wai yabata wannan sa'an sukasawa Nasir maganin sha'awa tunda sunyi bincike son gano Nasir ba wanda yakeso arayuwar sa *saike* ta gaya mana wannan ne aranan da tace musameta a prison kuma agaban ki tafara faɗa amma da akazo daidai nan Fanna tace Abbaty yafita dake
Chapter 71 · 0% Book details