← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 100

Sashe 11

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin sati biyu aka daura auren Dr Fanna da Abdulmajid namiji ba kunya aranan a part dinta ya kwana
da safe tana zaune gaban mirror tana gyara durin d'an kwalinta ya fito daga wanka towel daure a k'ugunsa yana jifan ta da murmushi tacikin mudubin gaban tane taji ya fadi da ake cewa Abdulmajid da Abdulsamad suna kama ba tagani ba sai yau ta sake tabbatarwa komai nasu irin daya hatta yanayin yanda yake tafiyar da mace kamar a makaranta daya suka koyo ban banci kawai Abdulsamad yafi Abdulmajid haske k'adan
tana cikin wannan tunanin taji ya dafa kafadunta da hannayen sa ya daura kansa awuyar ta ruwan jikin sa yana diga jikinta yana cigaba da yimata murmushi
yace " dan me akayi mudubi?."
bata bashi amsa ba saboda wani irin mamaki da tambayar ya bata idan marigayi ne amsa take bashi da dan ya hasaka sirri fukka shikuma sai yace amma yafi kyau ga masu hasken fata irin ku saboda kinga kekika haska mudubi bashi ya haska kiba,,

jinya ciji gefin kunne ta ne ya dawo da ita daga cikin dogon tunanin ta yace Doctor mubudi ma yafi son masu hasken fata irinku kiga kekika haska mirrorn bashi ya haska kiba ".
ya k'arashe maganan yana kashe mata ido
murmushi tayi tace'' ummmm abin yana bani mamaki ne yawancin kalaman ku irin daya".
mek'er da ita yayi tsaye yakai hancinsa dai-dai nata ahankali yake tifo da kalaman acikin mak'ok'oron sa yace my heart ai ba kalamai ba hatta zuciyar mu iri daya dan munyi tarayya da juna dashi azuciya akan abu daya aranan da nafara ganin ki aranan nakamu da soyyyar ki ina shirin gaya miki naci karo da wasiyar Halima naki auri dan uwa na aranan ba k'aramin tashin hankali na shiga ba dak'er da temakon Allah na jure na daukeki amatsayin matar dan uwa na Fatima ban dauki son ki dawasa ba dan Allah ki bani matsugun ni ko ya yake na miki alk'awarin zan shafe Abdulsamad acikin zuciyar ki nin kinga kin tunoshi to wajen addua ne amma bawani abu na rayuwa ba, Fatima I love you all my heart very very gashi kin bani farin cikin a dare daya kin kaini duniyar da ban san ana zuwa ba Fatima Ina miki sonda ban san iyakan saba".

zaunar dashi tayi tana masa murmushi tace'' nagode sosai".
ta dauko Mai tafara shafa masa aranan de ba dasu akayi breakfast ba har angama watsewa a falon Hajja suka shiga ba itaba shima yaji kunya musamman na uwar gidan sa Aisha

Nasir kam sai akwana na biyu yasan gidan nasu ya sauya tsaye yake abakin kofar mommy knocking yake sosai dan amma shiru Agrif yashawo saman yace Nasara zamuyi letty fa Nasir da gaba daya ransa yagama baci yace "dalla jeka ni sai na gaida mommy jiya mafa ban gaidata ba...
bude kofar akayi mommy ce daga ita sai rigan bacci zai shiga ciki ta fito ta kama hannusa suka fito ta rufe kofar kallon tuhuma yamata yace "mommy bazamu shiga d'akin ba gaidaki fa zanyi".
murmushi tayi tace'' son mu gaisa anan karkuyi letty'.
Yasake cewa "mommy da asuba naga daddy yashiga d'akin ki kuma jiya ma da naje gaida daddy kamal yacemin daddy a part dinmu ya kwana me daddy yakeyi a d'akin ki?".
tambayar ya daure mata kai dama shi take gujewa rasa mezata ce masa tayi ta sauk'e ajiyar zuciya
tace'' kasan tunda muka dena kwana tare nake jin tsoron d'aki na kaga kaima Agrif ya dowo d'akin ka shine nima daddy ya dawo d'ak ina kuma ma ba kullum zaina kwana anan ba wataran part din su wataran nan". kallon ban gamsu ba yake mata yawani hade fuska
amma baice komai ba yajuya zaibi bayan Agri
Mommy tace'' my dear ko ba kason kwanan daddy din anan ne".
juyawa yayi yana kallonta kai tsaye cikin maganan sa na isa tace " eh mommy ai shi namiji ne me yasa zai zo d'aki ki ai malamin islamiyar mu yace ba kyau namiji da mace suna kwana a dadi daya inba mijin gidan bane".
wani irin faduwa gaban mommy yayi tana mamakin malaman yanzu yanda suke fayya cewa yara komai tun basu kai matakin hakan ba yanzu d'an shekara tara har ya isa sanin komai amma afili kuma

tace'' kai my Son daddy ma ai mijin gidan nan neko".
shima cikin mamaki ya kalleta yace" a a shi daddy mijin Mama ne kemuma Abba na ne mijin ki nide gaskiya Daddy ya dena shigowa d'akin ki".
dafa kan sa mommy tayi tace'' oooo Nasir zaka ku makara idan kadawo sai muyi zancen kaji".
cikin fushi yafice ko gaisuwar bai mata ba
to haka mommy tayi ta shan tambaya a wajen Nasir cikin ikon Allah auren daddy da mommy bai cike wata 3 ba ciki ya bayyana ajikin ta alokacin Ummu ma tana daciki zaikai watani 4 tare sukayi goyon ciki har Allah ya sauk'i Ummu lafiya awannan karon macce ta haifa ayanzu yaran Ummu sun cike 4 Agrif Aiban Abbati sai wannan jaririyar me sunan Mama akasa wato kishiyar mommy Aisha anaki kiranta Humairah Hajja da kowa na gidan yanzu sai Humairah awajen takwaran ta Mama take wuni sai idan zata sha nono akawota wajen Ummu

bayan wata 2 itama mommy Allah yasauk'e ta lafiya kyakkyawar yarinya mekama dasu daddy su Agrif bak'a bata biyo mommy da Nasir ba
Nasir yana dawowa a makaranta zai wuce sama sai Dr Hafsa
tace'' Nasara kogani kafi mutum Nasara me wuyar badan ci baka ga jaririya ba kayi k'anwa "Mami nagani".
atunanin sa Humairah ce dan haka ya yamutsa fuska yace "nagan ta mezan mata".?
Dr Hafsat tayi dariya tace'' shikenan zan tafi da ita gida zan bawa Ayman dama matar sace namasa kamu".?
bai sake magana ba ya hakura sama sai Agrif ne yagane mommy ce ta haifu dan haka jefar da school bag din sa yayi yatafi da gudu
ai yana arba da yarinyar yasa wani irin ihu yana cewa "woow mommy haifa mata ita kikayi mommy kiga tafi Humairah kyau sosai kyakkyawa ce mamin Ayman bani ita".
ya k'arashe maganan yana zama akan kujeran yana washe baki Nasara da bai k'arasa hayewa ba yaji yakasa tafiya yajuyo yana kallon inda suke ahankali ya sauko yasa hannu yaja tawel din da aka nade yarinya sai da yamata kallon kamar na second 9 ya yamutsa fuska ya koma baya yana kallon mommy da take kurban tea itama shi take kallo yace mommy meyasa baki haifi fara kamar mu ba kika hafi wannan bak'ar ai wannan k'azama ce nide wllh bana son ta kuma kar a haura da ita saman mu".
ya k'arashe maganan yana yarfa hannun sa daya taba tawel din alanman yana tsantsanin hannu sa
Hajja ta meka masa zagi da hannu
tace'' kai ungo naka".
kallon raini ya mata yace " a a rik'e abin ki."

cikin matsifa Hajja

tace'' kai har ka isa kace kana k'amar bak'i uwar ka Halima bak'a uban ka Abdulsamad baki kaimu kaf dan ginmu ma bak'ak'e ne waye kaga fari kaima wayasani ko a hasbitin aka canjo ka da kanin b'akin halin ka baka gado mu ba idan an haura da ita saman ka kasheta".

shima cikin matsifar da dama sun saba shida Hajja yanuna mommy da yatsa yace kinga uwata farace tas niban san wata Halima ba... mommy ta ajiye cup din hannu ta
tace'' my Son jeka ka cire uniform din ka''.
wani dogon tsaki Nasir yaja yafara hayewa
Hajja tace'' Fanna kinga irinta ko ke kika b'ata yaronnan gashi yanzu y'ar da kika Haifa ma yace ba yaso kuma kinsan tunda ya furta baya so baya sonne nifa halin yaron nan tsoron yake bani bak'in halinsa fa k'aruwa yake" .
Mommy tace Hajja Nasir yarone zai dena".
Hajja tace''d'an shekara goman ne yaro"?.
shiru mommy tayi
Dr Hafsat tace'' gaskiya Dr Fanna ki duba al amarin yaron nan ki ajiye son da kike masa ki fara fashim tar dashi abu mekyau da barar kyau dai-dai da ba dai'dai ba ya kamata da rashinsa ba wata uwa wanda bata son d'anta saide hakan take dannewa da nusar dashi hanya......
Nasir da har yakusa hayewa yaji kalaman mamin Ayman sun gama bak'anta masa rai afusace ya juyo cikin rashin kunya yace "ke kije kinunawa Ayman dai-dai mana aishima jakin ajine kuma kullma sai yayi Letty kiji da kanki malama."
ya k'are maganan tareda jan uban tsak'i ya haye cikin sauri
Hajja tace'' kunji ko yaron nan wata rana dukan mu zayyi harke me daure masa gindin tunda gashi yafara da zagin aminiyar ki".
mommy tace'' Hajja zagi kuma ai amagana Nasir ba kalman zagi martani kawai ya mayarwa Mamin Ayman''

Mommy ta kalli Dr Hafsa tace'' amma dan Allah Dr Hafsat kiyi hakuri haka Nasir yake bayason a shiga harkan sa kuma inda Nasir zai shekara da mutum wllh baya shiga har kansa sai yashiga nasa".
cikin mamaki Dr hafsa take kallon mommy tarasa wacce iri yace ita itade tasan wannan ba tarbiyya bace mekyu amma afili tace
'' to Allah ya shiryeshi Amin mommy tace'' tana mek'ewa tayi sama
Hajja tana nunata da baki tace'' ta tafi lallashi

Mommy kai tsaye d'aki Nasir ta wuce a tsaye a tsakiyar d'aki ya dafa kai ahankali ta k'arasa inda yake ta zaga tasa hannu tacire hannusa akan ta girgiza ai tace'' am sorry kan ka ko ciwo amma meyasa kake da daukar zafi da wuri ka din ga hakuri kuma zakabawa Mami ku hakuri".
"me nayi mata zan bata hakuri ai ita ta zageni har tana cewa a dai'dai tani".
"kayi mana cewa fa kayi bakason k'anwar ka saboda bak'ace kuma mummuna".
"mommy nide ba k'anwata bace kuma wllh bazan taba sonta ba na tsaneta".
cikin damuwa tace''
''Meyasa katsaneta naga kai kake ta cewa kafison na Haifa maka y'amace kasa mata suna *NASRIM*".
cikin fusata yace
"Eh amma yanzu bana sonta Mommy kinsan fa duk yanda nake son abu idan wani ya rigani ina hakura meyasa Agrif zai rigani daukan ta har yana cewa tana da kyau ni yakamata na riga kowa ganin ta".?
Chapter 11 · 0% Book details