← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 100

Sashe 65

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummm Kamal na jima Ina bibiyar ka duk kanayi cikin *WAYO* da kace kana zaune kana jira nayi wani FURUCI akan Izza ka gama da ida kana zaman jiran na Khafulan to kawai dan Khafulan ya daki Abdul sai nace sai na kashe sa
sai kuma reshe ta juye ko to duk aikin *NASARA NE NASARA KO GONI KAFI MUTU NASARA ME WUYAR FADANCI NASARA GOSHIN GIRGI ME WUYAR KARAU*
murmushi tayi tace''
ummmm karna cika ka da surutu ana jiran ka saki na nake buk'ata dan na samu Wanda yake waje ba na gidan prison ba ai ni naso da bakaga ratayar NASRIM ba naga naka amma badamu zamuga na jatuma kace da ita ta gaida habila da hamana da fir'auna".

cikin muryar tausayi yace'' Humairah Ina son ki bazan taba sakin kiba dan haka dole ki jira na fito i love you with all my heart ya k'arashe maganan yana murmushi".
kamashi yan sanda sukayi aka fice dashi haka Mama ma tana ta kuka tana cewa abar ta zatayi magana da mijin da Mommy da Nasrim amma Ina basu bata dama ba

dak'er aka cusa Nasrim cikin mota sai ihun a bar ta taje gun Mama da Kamal take wllh basu bane sun daukawa kansu ne dan su kub'utar dani'.

haka de aka jata akasaka ta cikin mota

*Three brother house*

Big problem kenan

Daddy daga kotu bai zo gida ba sai tes daya turawa Hajja na yawuce jidda kawai wajen Abu
Mommy zaune ta rakka uban tagumi duk wanda suke zuwa murna ko nace jeje ba abari suna shiga ciki inba najiki sosai irin su Dr Hafsa ba kuka take sosai tayi tayi ta shawon kan Nasrim amma ta kasa to yanzu duk ranan da taji ta samu labarin abinda Nasir ya mata zata ce gwara na Kamal kenan gashi dole Nasrim tasan hakan tunda magana ya bazu ko ina kuma dama Kamal ne yabaza afili ta sake cewa Allah ya isa Nasir Nasrim da dan shegen ".

Ayman ne ya shigo shida Aliyu
bayan sun gaisa da Mommy

Mommy tace''Ayman Aliyu Allah ubangiji ya muku albarka yasa kufi haka kune kuka zame min komai ku kuka tsaya min da nemam lawyer alokacin da kowa ya guje mu".

Aliyu yace'' Ah Ah Mommy ai duk wannan aikin Nasir da Hajja ne shi ya tsaye muku Mommy Nasir yasha wahala Sosai Nasir ne ya saka aka temakawa Nasrim asan da take gidan prison Hajja ita ta fara gano waye kamal Hajja ita t..........

katse sa Mommy tayi da cewa '' Ayman idan kana son farin ciki na kar ka sake min maganan Nasir yanzu ni neman da zan masa na shiga kotu ne zan makasa kotu duk abin da yamin wllh bazan yafe masa ba......

Hajja da take shigowa ne
tace'' nima zamuyi zaman kotu dake ki nemonin jikana idan yazo gida sai ki makasa kotu Allah yabawa ne sa'a sa'a yo mu agaya mana kotu kotun sukutum na haifa eshe

*To masoya mu hadu a 23 dan jin dame Hajja ta temaka ya Shari'ar Izza da babanta zai kasan ce Mama da Kamal zasu yarda da hukuncin*

*Ina Nasir*
*Kamal zai saki Humairah ko sai dole tajirashi kamar yanda yace*

*Allah sarki Zahra na miki kuka*

*Bj*
*FURUCINA NE*
(rikicin babban gida)

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
( _rikicin babban gida_ )

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

*23*

dariya Ayman yayi yace "Kai Hajjar mu Allah yabar mana ke wato ke ba alk'alin bama kotun sukutum kika haifa".

"yo ai gaskiya ne Aymanu ya zata koremin jika kuma tazo tana wani cewa ita zata kaishi kotu ai ga hanyar kotun".
ta k'arashe maganan tana zama a k'asa sunkuyar da kai Mommy tayi
Dr Hafsa tace'' Hajja muna godiya sosai da kokarin ki Allah ya K'ara lafiya da nisan kwana".

Ayman ya kalli mommy yacigaba " Mommy kiyarda Nasir shi yayi komai kinga da farko Hajja ce tagano gomai".
Hajja tace'' ai ita bata masan me take ba yo ai dana biyewa fañna da duk zuri'a ta ba shafe tareshin su Aisha zatayi ba y'ar matan nan gata de mutum a furka me rai yana kallo ni mairo".

Dr Hafsa tace'' Hajja to ya akayi kika gano ta".?

"Ummm ai tun ran da nace sai na hada auren Izza da Haruna naga murna a tattare da ita kuma abin da yafi dauremin kai yanda Nasrim tacigaba da haukan bataso amma Aisha shiru kakeji bata ce komai ba bayan Nasrim maganan ta kad'ai takeji da kaina na Kira Aisha nace tabawa Nasrim hakuri ayi abinnan yariyar nan Izza tana da biyayya kuma wllh tana mutuwar son Haruna tun tana takaba na gano hakan har mafarkin sa take duk Ina sane to kawai dan jikata ce agidan sai nazama meson kai bayan ALLAH yace kayi temako a inda kakeda ikonyi musamman sunnan manzon Allah ba Lada zan samu ba amma Aisha da alaman ma zuge Nasrim take daga nan nagano sai abin da yasa zargina yasake k'aruwa kuma ranan da Haruna ya mutu Nasir yazo yake gayamin shifa yana tunanin ba Nasrim bace tayi kisan shiyasan duk Wanda yayi kisan akai abinda yake son
kuma ganin bayan Nasrim yake son yayi shine yayi kisan a kan gab'an FURUCIN ta
nace masa to wakake zargi kai tsaye yace Kamal tare dabani hujjojin da misalai sai yace inde da gaske Kamal ne
to Hajja ba makawa akan dukiya zayyi hakan dan Kamal b'arawo ne sosai bashida Amana bama ganin dai-dai a
ai'kin sa kawai muna kyaleshi ne sabo da ai yafi wani abin duniya awajen mu sannan idan Kamal ya tara dukiya mezayyi dasu ba three brother zai kawo ba zuba basa idon da mukayi yasa yana yanda yake so gsky Hajja ina mugun zargin sa da boyeyen hali yanzu de nasaka an saka CC TV na boye da farko dole sai mun sako daddy a binciken ke kuma abin da nakeso dake kinuna bakya goyon bayan Nasrim da Mommy ki dage akai abin kotu sannan ki tunzura Mommy ta fadi wani abun sai kawai daddy ya saki Mommy kinga idan shi yakeyi idan aka saki mommy jikin sa zanyi sanyi idan dan dukiyar Mommy yakeyi zamu gane

Tode haka akayi kuma yana kunna bin CC TV din Ina ganin duk munafurcin da Aisha da dan ta suke kullawa
sati 3 da rasuwan su Agrif Humairah tazo min da kuka tana cemin wai Kamal ne yayi kisan kayan ta yasaka yayi kisan gasunan yanzu Faiza mai'aikinta tafito dasu anan muka sake tambatarwa Nasir yace takoma tayi zaman ta kamar bata gani ba komai yazo k'arshe amma sheda mukeso dumu-dumu
anan Nasir yace to muma Hajja murikita musu tunani ta hanya amfani da FURUCIN Mommy muce tabaki guba a gefe daya akasaka guban aka bani naci gefin da ba guban sannan na gauraya na fara birgima
ai kunga yanda hankali Kamal da uwar ya tashi suka fara tunanin basu kad'ai bane masu kulla kullan kuma kunga ita Fanna ta tsira da bamuyi saurin amfani da FURUCIN nata ba su zasuyi dashi kuma ni zasu kashe alokacin tunda nice Fanna tayiwa FURUCI a kaina
NASIR da iyawan sa da Basiran sa saida yabi diddigi ya kawo wani babban malami mai suna malam K'aura ashe bokane shi yake koya musu komai ashe tun Aisha tana budurwa take aiki akan gidan nan tayi ta asa sosai amma mun rufawa malamin a Siri tunda yamana alk'awarin ya tuba yana da yaran shine Nasir yace mu rufa masa asiri".

Mommy tace'' kenan ku kuka sa Barira aiki kenan".?

"Eh mune muka sata amma daga baya ta zama abin farautar su dan su samu wanda yasakata aikin Saida Nasuru yasa aka d'auke ta agidan ko Dr Hafsa ma dagan gan ya saka aka kulleta duk dan yabata kariya dan sunyi niyar hallakata sabo tasan komai na Fanna shima Baba Nasuru ai ni nasa aka fita dashi dama Nasir ya gaya min Baban Fanna ne amma idan suka gano zasu iya illatashi saboda magajin Mommy ne ita kuma Fanna ta kwashe ta gayawa Kamal shine baban ta shikuma dan hauka aranan yazo kashe Baba Nasuru Wanda adaukan sa mahaukaci ne bayan ya warke ras kuma idan baki man taba ai nashigo aranan nida yaron alk'ali har nace na canza k'aran ai bayan nan nashigo nacewa Baba Nasuru karyayi bacci zai iyayin b'oko cikin dare kuma yanda na zarga din ne Kamal yazo kashe sa
Amma aikin mu daga k'arshe yaso ya b'aci saboda rashin Nasir karfin addua ne kawai yasa aka samu nasara Fanna kina da saurin yarda yanzu gashi mun rasa Nasir anyi neman duniya ba a gan Shiba burina yanzu naga Nasir sai mu daukeshi muje wajen kakar sa Emaka muje maiduguri musan asalin Nasuru shima".
Dr Hafsa tace'' Hajja Allah ya temaka yanzu ba inda aka samu labarin Nasir ".

Hajja ta nuna Aliyu da Ayman tace''kinga agun Wanda nake jin labarin nima
Ayman yace'' wllh mamy babu labarin sa amma muna nan muna bincigawa insha Allah za a ganshe".

Kotu ta yankewa Baban Izza hukuncin kisa ta hanyan rataya bisa kwararun hujja da Izza ta gabatar shikam bayyi mutuwar salihai ba dan Asher yake ta kutsawa Izza har yacika

*Allah kasa k'arshen kalman mu aduniya yazama kalmatus shahada ne Allah kacitan ta aikin mu na alkairi ya rinjayi sherrinmu duniya duniya cike take taf da rud'adi*

washe gari dan aike yazo daga prison wai Mama tana son magana da duk yan gidan kafin arataye ta dak'er Abbaty ya lalaba Daddy ya y'arda zai zo haka Ummu da Hajja da Mommy ma dak'er ya shawon kan su

Prison
Chapter 65 · 0% Book details