← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 100

Sashe 62

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh Baba bazan iya kisan kai ba Baba Al'hamdulillah meyeAllah bai min ba zanyi butulci Baba narayu cikin ni'imar cikin wadacecen illimi Allah yamun baiwa da mafi kirman baiwar ya bani Al Qu'ranin sa mai girma wan bakowa yakeyiwa baiwar hakan ba amma na butulce na kashe rai Allah yafi kowa son ran bawan sa taya zanyiwa Allah butulci wajen dauke wannan ran Baba abinda yasa na biye maka nun farko saboda son Agrif ne Allah bayyi auren na dashi ba na auri k'anin sa badan Allah yaciremin son Agrif ba "Ah Ah dashi nake yayuwa sai gashi dare daya Allah ya dauk'e mijina atunani na dan burina yacika na auri Agrif ne yasa Aiban ya mutu na biyeka kake duk wannan kulla kullan amma bawai zuciyata tayi bushewar da zan iya kashe rai ba
mek'ewa tsaye tayi tana kallon Baban ta tace'' Baba kasan abinda yasa na biye muku bayan rasuwar Agrif dan na gano waye ya kwashe Agrif ne nasan Nasrim bazata taba iya kashe shiba kuma Al'hamdulillah na gano ayanzu aikina zai fara sai na bayyana wa duk duniya waya kashe Agrif sai na d'auka masa fansa ko shine karshe abin da zanyi a duniya ne sai na cika burina Agrif salishin bawane jinin sa bazai tafi a banza ba".
ta k'arashe maganan tana juyawa zata fita

cafkota yayi ya wurgar da ita yace'' kikace kin gano waye kina nufin bazaki mai da hankali ki auri Kamal ba kenan?".
cikin tsoron yanda idon Baban nata yakoma Wanda zai iyayin komai ma tace'' ah ah Baba zan aureshi".

"to waye ya kashe Agrif".?
cikin in Ina tace'' ban gama binciken ba zan gaya ma idan nagama".

komawa yayi ya zauna yace'' Izzatu nasan kinsan Kamal ne yayi duk wannan kisan to Wllh karkiyi gigin tona masa asiri ki bari ayankewa Nasrim hukuncin a kashe ta bayan an kashe ta sai ki fito da duk hujjojin da zai nuna Kamal ne yayi kisan shida uwar sa kinga shima Kamal za akashe shi dukiyar zai koma wajen Abbaty kanin mijin ki anan zanyi aikin da dole sai Abbaty ya aure ki kinga komai zai dawo hannun mu ankusa ki daure akwai nasara rayuwar ki fari ne tas Ina hangowa haske acikin rayuwar ki".

Izza wani kallon baka da ilimi tayiwa Baban tace''to Baba amma yanzu bazan iya kashe Mommy ba abari sai bayan Shari'a zanyi duk yanda ka keso".
da haka Izza ta lallaba Baban ta ta fota

*Kamal da Mama*

"Mama na gama kwashe duk kudin nan na cikin account din mommy amma na Nasir ne ban gano ba kinsan shege ne Mommy kuma nayi duk da bara tace ba yanzu ba na bari asamu nutsuwa sata gayamin password din daya account din shima akwai manyan ajiya aciki ".
Mama tace'' duk ba wannan ba ko kasan munyi waya da K'aura yace kar mu tafi idan mun sake mun tafi kwai matsala amma yanzu yace muyi zaman mu zai haukatar da Humairah kuma bata gayawa kowa ba kayan yana hannu ta yanzu abin da nake so dakai kaje wajen uwar ta kasata agaba kace kund'an samu tsabani da Humairah ta dugu dan Allah tagaya maka inda take kaje ka sameta sokuwar fada maka Inda take zatayi sai musan abinyi".

*************
Kamal da Ummu
Ummu tace
"ikon Allah wai dama tsabani kuma samu kai da ita ai ban sani ba nide ta cemin zata je Kaduna gidan Balaraba dama nayi mamaki da tace min zata kaduna dan ita ma Balaraban yau zata bar k'asan zuwa saudia duba Abun ku
Humairah kenan shiyasa ta barmin wayoyin ta anan dan karma kane meta to tana gidan Balaraba". ta k'arashe maganan tana murmushi
jumm Kamal yayi yace'' amm Ummu ina wayoyin nata to?".

zuciya daya Ummu tace'' yana d'aki ta mek'e ta dauko masa
Murmushi Kamal yayi yace'' thanks Ummu amma dan Allah kar ki gaya mata gani nan zuwa dan zata iya canza waje yanzu zan wuce Kaduna gidan Aunty BB".

Kamal direct wajen Mama yasake komawa yace'' Mama komai yazo mana da sauk'i tana gidan wannan ma tsiyaciyar k'anwar uwar ta ta Balaraba kuma wai Balaraban sun tafi dubo Abu ita da mijin ta kin sa ba masu gadine da su ba agidan ba ma tsiyata
zansa yanzu amin kidnappers dinta kafin naje idan naje nakira uwar ta nace banga Humairah ba kinga zamu b'atar da ita cikin sauk'i ga kuma wayan acikin na dauki wasu tsirrika dayawa har".

"Shikenan Kamal Allah yasa bata gayawa kowa ba".
murmushi yayi yace "ai Mama aikin K'aura yana tafiya yanda yakamata amma.....
jin sallaman mommy ne ya katse masa maganan

Mommy cikin tashin hankali tace'' Kamal ya akayi kudin general account din
na duka babu kuma meyake faruwa?".

da sauri Kamal ya mek'e tsaye a zabure ya zaro ido yace'
"babu kuma mommy kamar yaya da sa hannu wa aka cire kuma?"
Mommy Zama tayi a kujera twositer tace'' da sing dina wai amma transfer akayi zuwa account na company nan Nigeria".
hannun Kamal ya d'aura akai yace "ai Mommy d'a zunnan naga an kwashe kudin company gaba daya dan haka kudin ko rabin ma'ai katan da suke iya cikin gidan nan ba bazai biya ba balle na company kuma ba Wanda zayyi wannan aikin idan ba Nasir ba".

Mommy tace'' Nasir! Nasir ! Nasir!".

"Mommy please kiyi hakuri mu bar shi da Allah mufuskanci yanda Shari'ar Nasrim zata kasance dan shine a gaban mu akwai kwararun lawyer da nasamu insha Allah za adace".
Mommy tace'' kai Kamal Allah de yabar zumunci ko bayan Raina Nasrim ta b'ata maka ban yafe mata ba".

"Ameen mommy zanje Kaduna dauko Humairah wai rigima take min Sosai akan sai na goyi bayan su a Shari'a nace ah ah shine ta nace sai na saketa wllh badan Abu da daddy ba da zanyi yanda takeso nagaji zan iya rabuwa da ita akan Nasrim kwata kwata kwanakin nan ta hanani kwanciyar hankalin".

girgiza kai mommy tayi tace
"Ah Ah Kamal kayi hakuri duk rashin fashinta ne itama tana da gaskiya rashin dan uwa tayi abin akwai ciwo fatan mu de gaskiya ta bayyana kowa ya gane Nasir ne ya aikata wannan aikin a kamoshi aduk inda yake a hukunta shi akan kudi ban zaci Nasir zanyi haba yayi surprise dina inda tun farko kudi yake so dana bashi mun tsira da lafiyar mu da mutumcin mu ni duk nafi tunanin makomar Zainab da Khafulan ko d'azu saida Hajiya Amina ta korosu wai su tafi dangin shegu wllh nafi jin su
su kam su Fayyat da suka tafi ai sun huta".
ta k'arashe maganan tana sakin kuka kamar kullum

hakuri Kamal da Mama suka shiga bata

**************
Dr Hafsa da Mommy

Dr Hafsa tace'' Dr Fanna kinyi gan gancin me yasa zaki dauki duniya ki dan kawa Kamal shi Kamal ba dan Adam bane wanda zai iya can zawa asanda yaga dama nifa zargina bancire kowaba a cikin gidan nan ina guje maki nadama yanzu har idan Nasir zai kwashe miki kudi zai barmiki nashi yatafi nifa nake gani kamar wannan abinda yafaru ya taba kwakwanki".

cikin b'acin rai Mommy tace
"Dr Hafsa idan ba temakona zakiyi ba kidena rabanin hankali Sam banga wani abin da kikayi Wanda zai temaka min ba sai Aisha da Kamal su
suke fafutukar akan Nasrim tunda wannan Abu yafaru dan haka ki bari naji da abinda yake damuna ni na gamsu da son da Kamal yakeyiwa Nasrim kinga fa yanzu har sun tsamu matsala da matar sa akan cese din".

girgiza kai Dr Hafsa tayi tace'' banga lefin kiba dan ayanzu dake da wanda ruwa yacisa daya kuke ko huta akace ki kama kamawa zaki amma.....
dakatar da ita mommy tayi tace'' stop Dr".

Kamal

cikin karayan murya Kamal yace'' please Ummu dan Allah ki tambayi min Aunty BB mana kode tare suka tafi da Humairah bata gidan nasu bokowa ba agidan".

Ummu tace'' Ah ah yanzun nan muka gama waya da Balaraba sun sauk'a basa tare amma Kamal ka kwantar da hankalin ka tasan zan gaya maka ne yasa ta canza waje amma de a gidan suka bar ta duk inda take bazata wuce kwanaki 5 ba zata zo kodan wannan Shari'ar da ta kwallafawa rai zata zo dan shi yahana taje duba Baban ku ma kayi hakuri kwanakin nan tana cikin damuwa kayi hakuri kafin nan ma zata dan samu sauk'i insha Allah Allah de ubangiji ya kawo mana sauk'i wannan Abu".
ajiyar zuciya ya sauk'e kamar gaske abin yana damun cikin
sanyin murya yace" Amin Ummu".
Yana kashe wayan yace Madam keda y'arki sai a *darussalam*
Al'hamdulillah komai yana zuwa min cikin sauk'i alokacin da nake so yanzu ba batun guduwa
yayi magana yana daddana wayan sa
ana dauka yace "Gagare cika'aiki tafadad'i Wanda tagayawa ne".
"Allah ya temaki oga tace ita kadai take aikin ta kuma kaya ta k'onasu baya wajen ta''.

murmushi yayi yace"k'arya take ku bata azaba ku sata a bencin sama har sai ta fadi gaskiya".

ya kashe wayan yana kiran lawyer din Nasrim yana dauka yace'' barrister Fu'at Jiji nine Habubakar Abdulmajid wanda da cese din k'anwa ta yake hannun ka ina son zan dan ganka kafin lokacin".

Barrister haryayi shiru de yace'' ok Ina zamu hadu".
Kamal yace yanzu ina kd amma zuwa dare kafadi inda zan sameka".

*Kotu zama na farko*

tacika makil

bayan maga takadda yayi bayani kotu ta buk'aci lawyer su gabatar da kansu da shedun su
aka mukaci lawyer mai k'ara yafito idan yana da tabaya
Lawyer ya kalli Nasrim
yace'' muna son ki fad'a mana sunanki".
"sunana Halima Abdulmajid Haruna".
"Ok Halima adaren ranan 8 ga watan 3 da misalin 12 pm kina ina".
"Ina gida".
"Mijin ki fa?.
"shima haka".
"Ok da yaushe yazo gida tunda ranan yakama ranan Monday ne ranan aiki".
"da misalin karfe 12 ya shigo".

"Halima ayanda CCTV ya nuna mana Yana shigowa kiyayi inkurin kashe sa hakane".?
Chapter 62 · 0% Book details