← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 100

Sashe 34

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

adaren ranan zaune suke a parlour Agrif sai operation din laptop din sa yake Nasrim da tagaji da jiran sa kawai sai tayi mek'a cikin yamutsa fuska tace'' my dear bacci".
d'ago kansa yayi yana kallon ta cikin tausayin kan su
yace'' zaki iya zuwa ki kwanta zan dan k'arasa wani dan aiki ne".
Nasrim kallon sa tayi gaskiya zuwa yanzu kunyar ta da kawaicin da take masa yafara takurata gashi gobe zai tafi yau din ma ba alaman zai kasance da ita bata San sanda yafurta
"na gaji na gaji".
afili ba
ahankali ya janye hannun sa kan laptop din ya d'ago yana kallon ta idon sa cikin nata sunkuyar da kansa yayi ganin bazai jurewa ganin taba amma duk da haka yafi tausayi kansa dan aganin sa yafita shiga takura bak'aramin dauriya yake ba wajen control din kansa awajen ta sosai yake buk'ata kasan cewa da ita yana cikin wannan tunanin bai Ankara ba yajita a jikin sa sosai ta cusa kanta cikin cinyoyin sa tana gyara kwanciyar ta tare da daukan k'afafuwar ta ta d'aura a saman kujera there'siter lumshe ido tayi tana sauk'e numfashi asan da tajita a cikin lafiyeyyen cinyoyin sa
shima a nasa ban gare kasa control din kansa yayi wani irin har bawa gaban sa yayi take jikin sa yafara rawa cikin in nina yace " Nasr Nasrim dan Allah ki sassautawa zuciya ta da gan-gan jikina sha'awar ki zayyi ajalina zai sa nasa b'awa alk'awarin da na dauka miki bazan taba kusan tarki ba har sai kin yarda ba sha awarki nake ba........
sai kuma yayi shiru
bude Ido tayi tana kallon sa can ta numfasa tace'' nifa Yaya Agrif ban San meye naka nayin wannan alk'awarin ba bayan ni da ka daukarwa ban amince dashi ba idan na amince zan shiga hakkin ka" .

"ah ah Nasrim ba wani hakki na da yarage baki ban ba kin min komai kawai de nayiwa kaina alk'awarin hakan ne".
afusace ta tashi zaune cikin b'acin rai tace'' bawani kan ka da kayiwa alk'awarin kayiwa mala'ikan naka ne wancan bayahuden Wanda tun randa kafada nagane ba wai dan Yana sona ya maka fadan ka kusanceni katafi ba
nasan so nane kawai bayayi najima da sanin bayason ka rab'e ni kai nafa san ba kai ba duk wani abu da zai min dad'i arayuwa bayaso mutumin da yarabani da uwar data haifeni zai so wani abunda yasoni ne ya hanaka mu kasance tarene saboda bayason mu samu kwanciyar hankalin idan ba haka ba meye ruwan sa da shiga tsakanin mu wllh bana son sa bana son sa nida shi bazamu taba hada wani halak'a ta y'an uwan taka ba idan kaga munzauna dashi to agaban Allah ne ya mana shisabi".
ta k'arashe maganan tana mek'awa tsaye shima mek'ewar yayi yakamo hannun ta
cikin kalan tausayi yace "come down my dear sister wllh bawai dan shi bane .....
katse sa tayi da cewa
"Kai da bak'in ka kagaya min haka kuma ai naji da kunne na kana cemasa ka dauki duk wani umarnin sa amma ban da saki ba zaka sakeni ba duk da ni ban yarda iya dokan da ya kafa maka bane baza arasa wani ba".
ta k'arashe maganan tana fisge hannun ta tayi gaba
zubewa yayi awajen yana maida numfashi afili yake furta Allah ya isa Nasir wllh kashiga hurumina
ita ma
Nasrim tana shiga d'aki ta kulle kanta ta fad'a gado a yau kam ta kai k'ololuwar buk'ata amma tayiwa kanta alk'awarin ba zata sake nunawa Agrif ba zata zuba ido taka k'arshen sa sai de haka kawai taji tana son sanar da Humairah ko zasu samu wani mafitar dak'er bacci ya dauketa

da sofe bata fito ba sai da lokacin breakfast yayi ta Shirya cikin wani riga da siket na atumfa bak'i me manyan ganye ja d'inkin pitate ne yayi mutu k'ar zama ajikin ta takalmin ta plate ja ta taura Jan mayafi tayi kyau sosai ahankali take taka steps din atunanin ta zata ga Agrif a parlour tunda baya d'akunan sama sai de taga wayam har zata juya ta shiga small parlou sai taga wani takanda akan center tables ahankali ta k'arasa ta dauka
"Kan uba!!!!!. tace a lokacin da takarasa karanta sak'on Agrif kamar haka
_my wife afuwa nayi tafiya akaro na biyu batare da sallama dake ba dan Allah kiyi hakuri nima ba haka na tsara mana rayuwar muba amma zai wuce_

*******************
bayan wata 5
Allah ya sauk'i Izza lafiya ta haifi yan biyu duk ka mata zo kaga murna awajen Hajja da mutanen gidan amma Izza da Baban ta basu so haka ba sunso samun maza
aranan suna yara sukaci sunan Ummu da mommy me sunan mommy itace babba ana kiranta Muwadda sai me sunan ummu Amina ana kiranta umdatu
Aranan sunan su Ummdatu Humairah mata ta haifi d'an ta namiji mesunan Abba Abdulmajid Hajja ta hana acanza dan haka da sunan sa ake kiransa

**********************
*Dubai*
Murmushi Agrif yayi yace
"Nasir tanan kuma ka b'ullo to ma in ba da aljanu kake son nayi aki ba ni daya nayi supervisor a k'asa she har 6 tare da kuma zuwa signing k'atsa 6 acikin wata daya kuma zuwa dakai bayan nawa aikin zaka had'amin aikin mutum shida ni nidaya".
kallon sa Nasir yayi sama da k'asa yace
" Ok ba zakayi ba"?.
mek'a masa file din Agrif yayi yace" Yes wannan aiki ai sai ku gauraye amma bana mu masu iyali bane".
ya ajiye file din ya juya zai fita yaji Nasir yace " lafiya lau Ummu sai dama inason kizama shedane Agrif yace zai ajiye aiki kinga kar aga kamar Koran sa nayi".
shiru yayi yana sauraron can yace " wai dan nadan raga masa nawa aiki dana Aiban kafin Aliyu yazo nikuma gaskiya ban yarda da wani na waje ba shine yace ai wannan aikin sai mu kauraye ok".
yace tare da mek'ewa Agrif wayan "Ummu barka da war haka".
"Agrif me kake son kazama ne kode zaka gaskan tamin maganan Hajja da take cewa idan ka auri Nasrim sai nadage ne tun daga yanzu ka fara wasa da aikin ka akan mace" .

"Ummu ba haka bane ki duba yawan ai.....
"rufemin baki kar nasake jin an kawomin k'aran ka akan aiki inaso ka kasance me aiki tukuru kamar Abban ku marigayi shi kad'ai yana iyayin aikin mutum goma bana son naji kace komai".
"Ok Ummu in sha Allah zanyi yanda kikace".
Daga fa Agrif yashiga very busy
Nasir yasamu abinda yake so dan ayanzu Agrif bashida lokacin kansa ma balle yasamu ya Kira Nasrim ko ta waya ne gaba daya yabircike cikin watannin nan yazama kamar mahaukaci kullum sai ya hau jirji ko shan shani bazai gaya masa yawo ba dama burin Nasir kenan ya kauda hankalin Agrif akan Nasrim

Nasrim ko tasake cika fam dashi yanzu tsayon 3 bako waya dan idan yasamu lokacin Yana dan kwada K'iran ta amma bata picking shima yafi son hakan dan bashida abinda zai gaya mata cikin Nasrim yayi wani irin girma kamar ba haifuwar fari ba watannin cikin 7 amma tana mutuk'ar shan wahala yamata mugun nauyi Hajja da sauran yan gidan Sarai sun gane ba d'a daya bane a cikin ta ganin yanda cikin yarabu kashe biyu kamar na yan ukku mommy Nasrim wanda komai ma yimata ake sallah ma azaune ko akwance fitsari atsaye dan ko gwada tsugunawa bata iyaye tunyana wata 5 ta tare part din Mama komai Mama ce take mata da kanta dan tana sha wahal sosai

*******************

bayan wata 2

duk mutane gidan suna kan dining table amma ita ta baze a tsakiyar parlourn da shirgin tuwon al'kama a gaba Kamal yana firfita mata kunun gyada sai faman lallab'ata yake yana mugun tausayin ta kamar yacire cikin yakeji yamutsa fuska tayi ta ture tuwon a gaban ta Kamal yace " sorry my sister sai me ki keso"?
hawayen data jima tana danne waye ya sirto mata da sauri Kamal ya ajiye cup din hannu yace
" sorry sis me yake damun ki".?
tace'' Yaya Kamal marata da cibiyata'.
ta k'arashe maganan tana kai hannun ta kan maran ta
da sauri Kamal ya juya ya kalli mommy ita ma mommy duk hankalin ta awajen yake dan haka taji abinda Nasrim tace'
Kamal yace " mommy maranta ne yake mata ciwo".? Mommy tace
"Son jikin tane ya janwo mata bana ce tana yawan motsa jiki ba tafa shiga watan haifuwa amma ita kenan kullum ajang'obe awaje daya waya sani mako labor take ta tashi tana d'an zagawa".
Hajja tace'' gaskiya yarinyar nan fa abin tausayi ce mijin ma gani nake baya kulawa da ita wane aiki zai hanani zuwa ganin matar sa ahalin da take ciki nikam wllh Agrif bai iya kula da macce ba sai de d'ir ka ciki daga ganin cikin nan magadan yan ukku ne aciki amma komai saide Aisha da Kamal su mata anya ko a waya yana k'ira kuwa".?
Mama tace'' sosai ma Hajja Yana k'irana" .
Chapter 34 · 0% Book details