← Book details Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 100

Sashe 23

Furucina Ne Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

******************
a hankali take takawa daga part din mommy zuwa nasu daga sama taji sauk'ar ruwa me sanyi a kanta cikin sauri ta d'aga ido ta ga wane isheshen ne zaune ta gansa kafa daya akan taya yana aikin zuk'ar taba tsigari gefe da gefen sa yan mata ne fararen fata a tsaye cikin bad dress
kafin ta gama tan_tan ce waye taji an jeho guntun sigar cikin bakin ta da sauri ta tofushi tana murza leben ta inda ya k'one cikin fusata taja baya dan tagan shi da kyau to waye shi kaman taso ganiwa amma bata ganin fuskan sa sosai gashi yana sama kuma idon sa acikin bak'in glass Wannan din waye shi? tace afili kawai sai tajuya takoma part din mommyn banko kofar tayi mommy tagani a dining room batayi mata magana ba ta fara taka steps mommy tace'' ke Nasrim ina zaki hakan?".
"Mommy wani d'an iska ne a sama ya zubo min ruwa ya jefa min guntu sigari shine zanje na duba d'an uban waye shi".?
cikin tsoro mommy tace'' Nasrim Yayan ki nefa".
"Mommy Yayana kuma? ni kaf cikin yayuna ba mahayin taba ba mane min mata wasu turawa nagani da bad dress a sama....
sauran maganan ne ya mak'ale mata saboda wani irin shak'a da taji a mak'ok'oron ta
"mommy cikin in in na tace'' dan Allah my Son kayi hakuri bata san kai bane afuwan".
"cikin dakiyar murya irin tasa yace "ai shine yanzu nake son ta sani tasan ni d'an uban waye na kuma tabbatar dani D'an iska ne"..
Mommy tace dan Allah kayi hakuri nace".?
"Wllh mommy yau sai tasha giya tasha taba sannan na hadata da alade ta kwana dashi kinga ta zama cikekkiyar y'ar iska ko".
da k'er har Saida mommy tasa kuka ya hakura ya barta amma yace zasu sake haduwa ta guji haduwa na biyu dan baya yafiya".
Mommy tace'' insha Allah baza ku haduba yanzu mafa data shigo sai da nacewa Barira tace bana nan kar ta bari ta shigo ai idan kana gida bana bari ta shigo kayi hakuri kaji my Son".
sakin ta yayi ya juya ya haye upstairs cikin b'acin rai
Nasrim ma cikin b'acin rain tace "mommy dama kina gida kika ce ace bakya nan saboda wani banza mommy na bar masa ke nikuma har abadan bazan k'ara ahigowa part din ku ba".
dagudu ta juya ta fice

**************
Aiban da Agrif

"Aiban dan Allah kaine kadai zaka iya temakona kamin wannan alfarman".
shiru Aiban yayi can ya sauk'e numfashi yace'' haba Agrif meyasa da kasan Nasrim kake so kace Izza yanzu Koda nace inason Izza ai iyayen mu bazasu yarda ba kuma yazama kamar wasa da hankalin sune ai".
Agrif yace"ni amin cewar ka kawai nake buk'ata nasu me sauki ne zuwa zakayi gaban Hajja kazube kana kuka kace ai Izza kake so nasan tana sonka zata amince kuma amincewar ta shine amincewar kowa nikuma idan aka tambayeni zance na sadaukar maka da ita zan tafi karatu course na watanni tara kafin nazo kunyi aure kuma kafin nazo nasan yanda zanyi na shawo kan Nasrim".
Aiban ya girgiza kai
yace "zanyi hakan saboda farin ciki ka amma ba dan Izza tamin ba".
**************
Hakan ko akayi Aiban yazube gwaiwoyin sa a gaban Hajja yana kukan shi idan bai aure Izza ba zai mutum Hajja uwar son jikoji kodan basu da yawa nan danan ta gigice ta tara mutanen gida ta tambayi Agrif zai iya hakura ya barwa k'anin sa da gudu ya amsa eh
Hajja tayi ta sawa Agrif albarka akan sadaukar

Izza zaune a d'akin Baban ta tace'' Baba kaji shawaran da suka yanke ko".?
Mustapha yayi shiru
can yace " eh Izza amma abin da yafi bani mamaki akwai maganan aure tsakanin ki da Agrif ga kuma shima Aiban za ayi auren abin yana rudani har yanzu na kasa tan tance wa gashi de ina gani har da rabon haifuwa a tsakanin ki da Aiban to na kasa gane yanda Agrif ma yake ta k'iftawa ta tsakani".
Izza tace " Baba kawai Ina ga maganan da d'in kake gani".

gir giza kai baban Izza yayi yace' ah ah bana baya bane akwai rud'adi sosai amma kar ki damu zanji da komai".

Izza tace" nifa Baba hakan yafiye min ma Aiban yanzu na gama gane Aiban yafi kowa aiki dukkan account din dukiyar gaba daya yana hannun sa dan shine aban garen kudi sai yagani yake turawa Nasara ma ni shakan ma yafi dan kana ganin Aiban gaka Naira".

dariya Baban yayi yace' ai ni nayi aiki akan Wanda yafi kudi yazama shine mijin ki yanzu de abin da yafi damuna wannan maganan Agrif din".
Izza tace'' kai Baba rabu dashi ayi abin da zai fita a rayuwata in ma sona take".

***************
a ranan aka sa ranan daurin auren Aiban da Izza Humairah da Kamal zahra da Aliyu sati biyu kacal dan Aiban yace bazai bar k'asan ba har sai an daura auren
Nasir yakoma Agrif ma haka fadan shagalin da akayi a bikin b'ata lokacine Agrif yazo bikin amma Nasir bai zoba Agrif tun a na shagarin yake ta faman tura kansa wajen Nasrim amma ba fuska acikin gidan aka ajiye Izza da Humaira dayake Hajja tace duk ka jikokin ta 5 anan zasu zauna da matan su dan haka gidan Izza da Humairah ajere suke Aiban bayan gama cin amarci yakoma India yabar Izza saboda makaranta Izza kam ta taka matakin da take so aburin ta dan Aiban me bushasha ne motocin da ya saya mata ma abin kallon ne tana fasa kai yanda take so cikin k'awaye fiye da yanda Nasrim takeyi
******************
*bayan wata 2*
Izza ta kalli Nasrim tace'' haba my sister amma idan kikace haka bakiyiwa ya Agrif adalci ba kuma akaran kan ki maki duba mun tashi mu hudu duk kan mu ukku munyi aure ban da ke."
Nasrim tace'' lokacin kune yayi nikuma ahalin yanzu bani da wani space da zan ajiye namiji kingane musamman Agrif bana buk'ar sake jin wannan ke da mijin ki kune masu yimin wannan dan ya Kamal tun so daya da yakawo min yaga ba fuska bai kara ba amma ya Aiban da ya Abbaty sun nace min har nadena mude message din su".
Izza tace
"to naji dan Allah tunda yace alfarma ya nema kimasa alfarma Koda na iya gaisuwar ne gashi ma a falo dan Allah ki fito".
da k'er Izza ta shawo kan Nasrim ta samu Agrif a falo Agrif kam awanan Karan da k'arfin sa da kalamai masu zafi yazo bai sha wani wahalan shawo kan Nasrim ba duk taurin kai irin nata

Numfasawa tayi tace'' shikenan amma kasani ina da dokoki".
'ki fadi ko wacce iri yace inde zaki yarda ni Agrif ina son ki".
tace
"na farko deni ina da kishi duk mijin da ya auri Nasrim to yasa a ransa tamkar ya auri mata hudu ne dan daga ni ba k'ari ina da kishin azaba wanda ni kaina ban san iyakar sa ba".
Murmushi yayi ya sauka daga kujeran yazuba guiwowin sa k'asa yace" inde wannan ne mai sauki ne ba mata hudu ba na sawa Raina ke a masayin mata dubu kike a rai na ke daya ce azuciya ki rik'e ki aje ".

murmushi tayi tace'' Allah ya Ag wllh ba dan ina mutuwar son kaba wllh ba zan sake yarda da kai ba dan ina da kishi sosai a gabana kece kai Izza k.....
rufe mata baki yayi da tafukan hannu sa yana dariya
*************
Hajja tace'' ikon Allah ai ni dama nasan iskanci ne irin na yaran zamani amma Agrif ai na Nasrim ne kunji irin iskancin da yadinga min ne wai wllh shi de cikin satin nan ya keson adaura masa aure daddy yace "gaskiya Hajja ba wani abin da yarage banda a daura auren me za a saya jira a take aka sa ranan auren wata 1
Nasir bai ji ba sai a status din Kamal ya gani alokacin ma ko suna tare da Agrif din a Dubai cikin riki cewar yanani yake kallon Agrif yace
"Agrif bakaji gargadin dana maka akan yarinyar nan ba ko Wllh auren yariyar nan shine mummunar k'addaran ka na gaya maka ba matar ka bace ka nace".
Agrif cikin b'acin rai yace'' ni kuma na gaya maka baka isa ba Ina son Nasrim kuma baka isa hanani auren taba".
Nasir
mek'ewa yayi tsaye cikin b'acin rai yayi taku ukku ya k'arasa Inda Agrif yake cikin sanyi murya yace Wannan shine Warning na k'arshe da zan maka Haruna kar ka auri Halima rayuwar ta ba shida kyu idan kasa taurin kai abin ba zai muku yau ba".
"Ai kai ba ubana bane da zaka sani gaba kana gayamin wannan Nasrim ce nan da sati biyu tazama matata".
gyad'a kai Nasir yayi yana
murmushi yafara takawa na barin gun
tun daga wannan rana Nasir bai k'ara nuna cewa baya son aure ba har taya Agrif shidimar biki yake saura kwanaki biyun adaura suka sauk'a a k'asar da dinbin abokan su
Dr Fanna kam awanan Karan tafito tanuna eh Nasrim y'arta ce kuma tayi rawan gani
Safiyar jumma'a dinbin al'uma suka sheda auren
Haruna Agrif Abdulrahaman da Halima Abdulmajid Nasrim
Justice Abdulmajid yatara mutane sosai
Chapter 23 · 0% Book details