← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 149

Sashe 97

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hassale muryarta Na rawa takatse shi ta hanyar cewa nace karka jirani Kabir..kabir ka nemi matarka a gaba ko dole sai ni zaka aure. ranta abace ta juya fuuuuuu zata wuce da niyar barinsa gurin Yayi sauri janyo hijab dinta da hannushi.
Ta juya a fusace tana masa wani irin mugun kallo may tattare da tsansar takaici takasa ce masa komai sai shanyayun idanunta kawai data zuba masa km still hijab dinta Na rike a hannushi yaki saki daidai wannan lokacin zeenat ta dannowa motarta 'cikin compound din estate din ta nufi parking space.
tayi parking idanunta ya sauka akansu ta bude motarta ,ta fito tana danna key din hannuta ahankali ta riskesu 'cikin wannan halin .
suna kallon junansu yayinda nablah ke mishi kallon tsana may cike da tashin hankali .
shi km Yayi tsaye rike da hijab dinta yana kallon kwayar idanunta wanda in basani kayi ba wlh zaka rantse da Allah kallon love sukewa juna .

da mamaki zeenat ta bar jikin motar tana binsu da matsiyacin kallo har takaraso basu ankara daita ba sai data buga musu tsawa tare da cewa kB wannan wani irin tsagwaron iskanci ne da wulakancin hk ?

A frigice kb ya juyo tsaitin dayaji mgnr Yayi saurin sakin hijab din nabla .. yana soso keya.. Daman iskancin da kuke yiwa mutane a gida kennan idan bamunan ?

.. nablah najin hk jikinta yasoma rawa rawa hawaye suka cicciko a idanunta tashiga furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun abinda take gudu kennan gashi yafaru .
shiyasa take son raba kanta da kB da wata alakar soyayyar dayake son damunta daita .
tun Bai jawo mata tashin hankali da maseefa ba. km tacigaba da rayuwarta har zuwa sanda ummi zataje India ta dawo takama gabanta ..

Shima kB take jikinshi ya dauki rawa jin lafazin mdm zeenat din .

kuna jina inagn kunmin shr awa tsofafin kurame abinda kukeyi kennan ko?
Kai Kabir da kake son bata rayuwar yarinyar mutane idan kawarka akayiwa hk zakaji dadi?
Tsit kake jin mlm kb bbu 'bakin mgn .
Idan sonta kake ai bata Haka zaka biyo ba?
ke km karamar Yar iska may hijabin sharri maimakon ki dauke Dan iska da double slap amman dayake kema isakarce Yar,uwarsa sai kikayi tsaye kina kallonsa.
jin hk Yasa Hawayen dake makale a idanunta samun damar zubowa sharrrrrrr.....muryata cike rudani da in inna tace wa..ll..ahi wlh aunty ba abinda kike tunani bane Na rantse miki da girman Allah bbu komai a tsakaninmu wlh shi.... yimin shr stupid girl kawai "sannan ta juyo tana sake kallon inda kb ke tsaye ya kasa cewa komai .
gabadaya kunyar mgnr zeenat tasa shi jin wani iri ajikinsa ya dinga ji tamkar kasa ta tsage yashige ciki.

daga yau kB banason sake ganinka da yarinyar nan ,ko sbd Kai aka kawota aiki gidan nan ?

Bakinshi Na rawa yace a,a madam to karka sake Na km ganinka daita.
idan ba hk ba wlh you be fired .
Tana kaiwa karshen mgnrta ta juya tashige 'cikin.

nablah dake tsaye tana xubda Hawayen takaicin abinda kb yajanyo mata. 'cikin kuka tace kaga irinta ko kb ?
kaga massefar da kakeson jefani ciki ko?
amman bbu komai Na gode da abinda kayi min da kabarni nayi tafiyata da yanzu hk bata faru dani ba.
kiyi hakuri nablah wlh nima ba hk naso ba .

bbu wani hkr dazaka bani kawai Ni ka cuceni tunda kabari akayi zargini akan abinda bantaba aikatawa ba . Daga karshe Ina hada ka da girman Allah kafita harkata ko gaisuwa Na yanke a tsakaninmu ta juya ahankali tasoma daga kafafunta tana kuka da takaici zargin da zeenat tayi mata .

Bangaren zeenat kuwa tana shiga main parlour din gidan ta tadda ummi tana kallo bata lura da deeni dake kwance a gun ba .
Kallo ma kike ummi ana shirin yimana fasadi acikin gida ?
ummi ta juyo da sauri gabanta Na wani irin faduwa ,da kyar tace meya faru zeenat?
Me kika Gani ?

uhmmmm wlh wancen Dan iskan yaron may wanki ne.
may yake da suna ma , da Ni har Na manta sunanshi ummi tace kB yauwa wlh ummi yanzu nan naganshi rike da hijab din yarinyar nan nablah.
daidai nan DEENI dake kwance ya Dan maida hankalinsa kansu gabashi wani irin dukan uku uku .
Take zuciyarsa tashiga bugawa da sauri da sauri tun Bai ji me zata ce ba . da kyar yacigaba da jan numfashi .

zeenat tacigaba wlh ummi kibaria a sallami yarinyar nan kawai tun kafin ta daukowa mutane magana azo ana kuka damu .
nidai wlh bbu ruwana bbu hannuna ciki.

Dan Allah mlm kiyiwa mutane shr idan bazaki fadi alkhari ba inji cewar ummi Ok hk ma zaki ce ummi ?
to nayi shr bazan sake ganinsu nayi mgn ba. duk abinda yabiyo baya .... ummi ta katseta ta hanyar cewa bbu abinda zai biyo ba sai alkhari hb mamana meyasa kike yin hk ne ?

DEENI da gabadaya hankalinsa yasoma barin gangar jikinsa ya gyara kwannciyarsa kan three sit tare da runtse rikitattun idanunsa gam batare da yace komai ba sai numfashi yake fiddawa .

ummin taja bakinta tayi shr tunowa datayi DEENI na kwance a parlour Dan gabadaya zeenat dince ta rikitata Dan batason DEENI yaji komai . ahankali ummi ta juyo inda yake kwance ganin bbu wata alamun yaji wani abu Yasa ta sauke ajiyar zuciya wa tunaninta Bai ji komai ba tayi zeenat alamun tashiga hankalinta itama zeenat din sai lokacin ta lura dashi amman bata damu dayaji ko kada yaji ba .tunda tasan shi ba may shiga shirgin mutane bane .
amman bata sani bane kwance kawai yake runtse da idanunshi amman gabadaya hankalinsa yana tare dasu tare da jin jikinshi tamkar ana watsa masa garwashi wuta.

...jiki a matukar sanyaye nablah tashigo parlour,n kanta akasa sbd duk taji abinda zeenat din ke fadawa ummi .
Dan hk tasa guri tarakube kanta jikin Bago parlour,n Banda kirrrrrrma bbu abinda ilahirin jikinta keyi .
Ga zufa sai keto mata yake ta koina ajikinta .

Tsayuwar me kikewa mutane a wajen ki wuce kije kiyi min aiki stupid girl kawai inji cewar zeenat wlh mutuncinki kike zubarwa bana wani ba.

Inda kinsa karuwanci ne a ranki ai da baki zo neman..... short up there deeni ya bugawa zeenat wata razananniyar tsawa data nemi frigita dukkansu tsit parlour,n yayi zeenat ta zuba masa ido tana kallonshi da mamaki .

kar dai yadaina tsanar yarinyar kmr yadda ta zata?
to meyasa zaiji Haushi Dan tace idan tasan karuwanci ne a ranta Kai dole akwai wani dalili jikinta yabata hk.
dubi yadda kamaninsa suka sauya kmr itace kb yakamawa hijab .
ya katse mata tunani ta hanyar cewa Bason shiga shara ba shanu kin gane ko?

Bai jira amsarta ba ya juyo inda nabla ke rakube yana jifanta da wani matsiyacin kallon take zuciyarta ta motsa.
tsoro may tsananin yashigeta yayinda hankalinta gabadaya yakara tashi Tasoma fargaban abinda zai mata.
,ganin ya gyara kwanciyarsa ya juya musu baya.
Yasa nablah ta dinga sauke ajiyar zuciya a boye tare da yiwa zeenat din Allah shikara a ranta. kema kiji yadda naji a raina.

Ummi tace kinga abinda nake gudar miki ko mamana amman bakiji mgn idan kika soma nacin mgn bakiji baki Gani .
ummi daga fadar gsky km sai cibi yazama kari . Deeni najinta kmr yatashi ya yaryarfa mata maruka ko zata shiga hankalinta .
amman darajar umminsa yasashi kyaleta .

Ummi tace Hk ake fadar gsky da wulakancin mamana wannan yarinyar ce karama ahankali zaki nutsar daita ta yadda zata fahimci ce ki.
bari Shima kb din zan hada dashi ne zanshiga tsakaninsa daita.
zeenat ta wuce fuuuuuu cike da fushi tayi dakinta .
Shi kuwa deeni cewa Yayi a ranshi dama kin barshir first love Ni.... nasan yadda zanyi dashi

Itama nablah lallabawa tayi tashige kitchen Dan nan yafi mata saukin shiga akan ta wuce dakinta .

Karfe tara Na daren ranar deeni Yasa akayi masa Kiran kb .
wanda tun lokacin da sakon Kiran boss din nasa yasame shi ,yasha jinin jikinsa.
Km hankalisa yayi kololuwar tashi fiyye da tunanin may karatu .

kb durkushe gaban boss dinsa tamkar Wanda zai yi masa sujjada tare da sunkuyar da kanshi kasa sosai yana kallon center rock din dake shimfide a gurin.
yayinda DEENI ke zaune kan kujera may zaman mutun daya system ne a gabanshi yana aikin tura sakwanni ta yanar gizo.. kwata kwata yi yayi tamkar Bai San da zaman wani halitta ba agurin asalima gabadaya hankalinsa baya 'cikin parlour,n Kusan awa daya da wasu Yan mintina sannan ya dago rikitattun idanunsa ya zubawa kb yana kare masa kallo may tattare da tsantsar tausayi..... domin shine dalilin zuwansa 'cikin estate din .
km zamansa yake amman a yau yana jin bazai iya cigaba da zama dashi ba.
deeni ya Dan gyara zamansa tare da dauko wani envelop ya bude bakinsa da kyar Kira sunan kb ......
kb yayi saurin dagowa tare da amsawa yana duban boss dinsa a tsorace ... deeni ya Miko masa envelope din batare da yace masa komai ba .. jikin kb Na rawa yasa hannu biyu yakarba yana sake duban deeni .

Deeni ya numfasa tare dayin gyaran murya sannan yace yau jumma'a km yau ce ranar daza bar aiki tare dani kb .sakamakon son shiga gonata dakake kokarin yi .
amman dana son zan iya hukuntaka da hukunci mafi tsananin .
amman nakiyi sbd kana bani tausayi Dan hk Ga wannna emvelope din.
Chapter 97 · 0% Book details