← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 149

Sashe 144

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi can bangaren deeni tun daren jiya jikinshi yabashi gidanshi bbu lafiya sbd mafarkin barkatai daya kwanayi km duk akan nablah ne Dan Haka tun da asuba yashiga neman layin zeenat dana ummi Amman shr bbu wanda ya dauka acikinsu ,Bai hakura ba Yacigaba da neman layin Daga karshe ma daya Kira yaji wayar akashe .
nan fa hankalin shi yayi mugun dagawa yakasa yin komai sannan Kuma rasa jin dadin zuciyarsa kawai yaga gara ya dawo gida .batare da bata lokaci ba yabada Umarni siyan Tiket kawai yana shirya jikinshi yana neman layin ummi dana zeenat Amman har lokaci shr swchoff ake ce masa . Wani tashin hankali ma sai jirginsu ya sauka a Lagos gabansa ya tsananta faduwa zuciyarsa Na tsinkewa Allah Allah yake yaganshi agida kawai ..

Yana shigowa 'cikin gidan da zeenat yasoma cin karo ya sauke ajiyar zuciya da karfi yana dubanta tana sauri tana hada kayan bby Na haihuwa Dan jiya daddare basu tafi da kayan haihuwa ba sbd a rude suke.
tana ganinsa duk ta dabirce tasoma kuka muryasa Na rawa yace Ina nablah da ummi 'cikin sharar hawaye tace suna hospital prioucion s .
Tun jiya batada lfy amman doctor yace nakuda ce ....inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana tafiya yana furta hakan acikin zuciyarsa atare suka shiga mota gabadayansu a rude suke .

sanda ya iso asibiti nablah ta jigata iya jigatuwa bbu kowa agurinta sai nurse nurse ne tare daita.
deeni ko gaisawa bai tsaya yi da ummi ba.

Hankalinsa a matukar tashe yace Ina nablah take ?
Suka nuna mishi dakin haihuwa Kai tsaye yashige 'cikin labour' room din wata doctor ce tace please sir kayi hakuri ka Dan jiramu awaje hankalinsa a matukar tashe yace madam Dan girma Allah kiyi hakuri nima Ina son naga matata .
Ai yana dora idanunshi akanta Bai san sanda hawaye suka shiga siyayo masa .
ya mannata ajikinshi ya rungumeta yana kuka da aikin jero mata sannu bbu kaukautawa addu'a kawai yake mata yana zubda hawayen tausayinta ya dinga jin daana kar bar wa mutun nakuda daya karbarma ta huta tun daren jiya ake abu daya har yanzu . tamkar shi nakudar take jira ta tashi zanga zanga Amman haihuwa shr bbu labari .

Hankali likitoci Suma yayi matukar tashi sosai tun daren jiya suke tsaye akanta , zeenat kuwa a ranta tace tun dai shekaranjiya Dan dai bamu gaya muku gsky bane .
.. likitoci suka tabbatarwa deeni zata haihu zuwa karfe goma shabiyu ranar Amman gashi har yanzu shr Ga dai 'cikin Na motsa alamun bby 'cikin Na raye.
Sosai hankalin deeni yakai karshe gurin tashi tsigar jikinshi har tashi suke tsabar tausayin yarinyar .
ganin har biyu tayi ta wuce bbu sauki sai wahala datake Sha Yasa Shi cewa doctors din suyi mata aiki su cire mata abinda yake 'cikin ta huta .
tunda sauran karfinta yazamo yanzu ko nishin bata iyawa sai shanyayyun idanunta datake jujjuyawa wal wal dasu .

Hudu daidai aka yi mata shirin aiki sai addu'a ummi keyi ita ko zeenat kuka take sosai har da shesheka .

A dakin tiyata sabon ciwo yatashi 'cikin zafi zafi ta dinga jin bayanta tamkar ana Sara mata da ada jikinta wani irin rawa har gadon datake kwance akai shima sheking yake .iya wahala nablah tasha sai dai Allah sauketa lafiya ..

Deeni rike da hanuta yana kuka yana mata addu'ar .Shi yanzu bata 'cikin jikinta yake ba ,ita din yafi bukata .domin duk yadda yakai da son haihuwa sai daya ji ta fita aranshi tausayinta da kaunarta ke zariya a gangar jikinshi.
wani irin uban nishi tayi da karfi sai Ga kan yaro ya fito fit .
Jim kadan wani kadan wani yaron ya sake fitowa sororo deeni yayi yana kuka yana kallon ikon Allah Wani sabon kukan farinciki ya kufce masa ya rike hannuta gam yaki saki sai sumar kanta yake shafa ahankali yana mata sannu can km sai Ga wani sabon ciwo nakuda take doctors din suka gane Yan uku ne suka taimaka mata aka fiddota agalabaice duk tafisu shan wahala Dan ko kuka batayi.
nan suka fita da yaran duka uku Dan gyarasu ummi tayi matukar farinciki da saukarta lfy an shirya yara ummi nata murna .

Shi kam deeni bbu wanda yake son Gani kmr nablah doctors sukace masa kada ya damu ana kimtsa ta ne suka mata allurar bacci sannan suka kaita dakin hutu bacci take sosai Dan batasan irin hidimar da'akeyi daita ba .koda zeenat taga bbys sai kirjinta ya buga sbd tsabar kamanin da suke da deeni sak sak komai Nasu Na deeni har ma gara ta mace ta dauko kamanin uwarta sai sai farin Na deeni ta debo .'aiko take tasoma yiwa ummi mitar kamanin yaran .Kai zeenat wlh Kin fiyye matsala Wani kama yaran nan sukayi da deeni kawai idanunki ke ganin hk Amman ni Banga hk ba ..

Tun asibitin ummi ta dinga kiran dangi tana sheda musu zeenat ta haihu sauka lafiya tasamu yan uku .

Sannan ta tilasawa doctor kan sai ya sallamesu a ranar doctor yace a'a sbd uwar tana bukatar hutu .ummi tace bbu damuwa abar uwar anan zasu wace da yaran doctor yacika da mamaki Amman dayaga ai sune suka kawota yace shikennan .

Suna komawa gida nan dangi sukayi matuka murna da farinciki saukarta lfy kowa sai albarkaci bakinsa yake fada Kai Kai zeenat gsky kin iya haihuwa tamkar bake ce kika haifi yaran nan ba.
Kai Masha Allah Yara sak ubansu takoina deeni yaran nan suka dauko ita dai sai dai tayi murmushi kawai tana duban yaran dake kwance masu tsantsar kamanin da mijinta tun asibitin gabanta ke faduwa sbd tsabar kamanin da yaran ke yi da deeni ..

ita kam nablah tana can hospital batasan hidimar da'ake da bbys dinta a gida ba.
Dan batama San yan uku ta haifa ba .

Tana farkawa idanunta suka sauka akan deeni ya taso da sauri sannu nablah kin tashi ?
Kallonsa kurum tayi .
Ta kauda fuskarta gefe ya wanke mata baki 'cikin wani dan karamin kwanan siliva tare da tayarda ita zaune yaje ya ajiye kwano ya hado mata tea me kwari yazo yana bata da kanshi ..idanunta kawai ta tsura masa tana kallonsa tana tea din .
ahankali ,shi kanshi yagane mgn take son yi .. 'cikin sanyi jiki ta kauda bakinta Daga cup din . alamun takoshi .
Ya ajiye cup ya dawo gefenta ya zauna ya kamo tafin hannunta 'cikin nashi yana mammatsa mata magana take son yi Amman bakinta Yayi mata nauyi ..

Ya kafe da rikitattun idanunshi gabadaya tayi wata irin muguwar rama acikin kwana biyn din datayi tana nakuda muryarsa a sanyaye yace kina son wani abu ne akawo miki ?
Ta girgiza masa kanta. ahankali .

Ok kimin mgn mana naji muryarki ko wani guri Na miki ciwo ne,?
Nan ma ta girgiza masa kanta ..can km muryarta a raunane tace Ina abinda Na haifa ?

Gabansa yayi Wani irin tsalle Dan baiyi tunanin zata tambayi abinda ta haifa ba .take
Zuciyarsa tashiga harbawa da sauri da sauri muryarsa can kasa kasa yace Suna gida gurinsu ummi .
ta runtse shanyayyun idanunta da suka sake shanyewa tsabar wahala dataci .
yabita da wani irin kallo tunhuma Haka kawai yaji gabansa Nacigaba da dukan uku uku sautin muryarta ya sake ji nima Ina son zuwa gida .yace Ok bari nasamu doctor . Ya Mike tsaye ya sumbaci goshinta kana ya fice da sauri yana waigenta .

Byn deen yasamu doctor yayi masa bayanin ko za'a iya sallamarsu bbu wata matsala doctor yace bbu komai ai zasu iya wucewa ..

Sai yamma liss suka shiga estate din ta kofar baya deeni yashiga daita sbd taron mutane dake 'cike da gidan.
Yan taya murna bai samu damar kaita dakinta ba .
ya nufi dakinsa na kasa daita zuwa lokacin da jama zasu tafi ..

misalin karfe tara Na daren deeni yaje gadon kwanciyar yaran ya dauko mace da namiji ya rungume yaran yana jin matukar son yaran nabin jiki da jinin jikinshi yana mamaye ruhinsa da zuciyarsa .. ummi ta dauko daya suka nufi dakin da nablah take .
Da sallama suka shigo dakin nablah .
suka zauna tare da saka nablah a tsakiyarsu muryar deeni cike da farinciki yace nablah kinga arzikin da Allah Ya ...wani irin kallo ummi tayi masa yakasa karasa abin zaice take km yagane ashe yaso ya kwabsa ne..kwantar da yaran sukayi akan bed .wayanda suka Sha wasu haddun kaya sanyi masu shegen kyau da tsada da daukar hankalin farare tas tas dasu tamkar ya'yan turawa ,sosai ta tsurawa bbys din ido tana masu Wani irin.kallo kamanin yaran take kallo 'cikin tashin hankali taki dauke idanunta akansu yanzu itace ta haifi wayan nan kyawawan bbys din masu kyawun kyau hk ganin yadda yake kallon baby's din Yasa ummi tashi ta fice shima can deeni ya Mike tsaye yana amsa wayar Yan taya Shi murna ya bar dakin .

Dakin ya saura Daga nablah sai bbys dinta da suke kwance reras akan gado abin sha'awa. kallon yaran tacigaba tana jin Wani irin sanyi Na bin jikinta take km taji Wani irin mugun son yaran yashiga ranta tare da ratsa kowane shashi Na gangar jikinta tundaga tafin kafafunta har 'cikin kwalkwaluwarta nan take taji idan dukiya zata taru bazata iya rabuwa da yaranta ba ,daidai da daya Daga cikinsu bazata iya bayarwa ba ballanantana dukansu kawai ta fashe da wani irin matsanancin kuka tare da rungume yaranta tasoma sabatu , wallahi tallahi bazan iya rabuwa daku ba yarana Ina sonku ina kaunarku km zan rayu daku.
koda kuwa duniya zatakini .
ta zageni akanku Ina sonku takarasa fadar hkn tana sakin Wani irin kuka me cin rai ahankali take cigaba da kallon baby's dinta hawayenta Na tsaya ahankali tasa hannuta ta goge tana sakin ajiyar zuciya 'ta daura mazan duka a saman cinyoyinta mace km ta daurata akafadarta tana jin Wani irin dadi mara misaltuwa aranta tare da jin duk abinda zai faru sai sai ya rafu Amman bazata rabuwa dasu ba ....

Uhmmmm nah wa oooooooooo

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Dedicated to
HAUWA A USMAN
JIDDARH

Page 99
Chapter 144 · 0% Book details