← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 149

Sashe 138

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

" Santa nake kuma auren ta zanyi mutumin ya bawa Deeni amsa kai tsaye, sai da Deeni ya dafe saitin zuciyarsa saboda wata muguwar bugawa da tayi da k'arfi, tana barazanar fasa k'irjinsa, hannunsa ya luma cikin sumar kansa, yana cizon leb'en sa da k'arfi, a harzuk'e yace " waye uban ka?

Ido mutumin ya zaro, shima cikin zafin rai yace " dalla malam waye kai dazaka zo kaina ka tsaya kana min wasu surutai marasa kan gado?

Deeni ya nuna kansa yace " ni......?

sai kuma yayi guntun murmushi yace " dan uwarka uban waye ya baka izinin tsaya min da mata ta,?
ido mutumin ya zaro yace " matar ka fa..?

"Kwarai kuwa matata ce, baka da hankali ne da baka lura da cikin dake jikin ta ba?

" dan girman Allah kayi hak'uri wallahi ban san matar aure bace, kuma Nablah bata gaya min tana da aure ba asalima yau nasoma ganinta har ma narage mata hanya .

Jin mutumin ya kira sunanta yasa Deeni k'ara harzuk'a, nan yabar mutumin ya nufi gida, a parlor ya sami Ummi da Nablah suna hira, dayake ummi tazo gidan maida kayan Nablah ...a fusace ya shigo parlor, hannunsa dafe da zuciyarsa, idonuwansa sunyi mugun yin nauyi , tafiya yake yana tangad'i tsabar jarabar kishi dake cin zuciyarsa..

" Subhanallahi Ummi ta fad'a ta mik'e tsaye ta nufe shi da sauri , dan bata tab'a ganin Deeni cikin mawuyacin hali,i Rin hk ba kuma cikin tashin hankali irin na yau ba, da ganin baya cikin hayyacinsa, gadan-gadan kan Nablah ya nufa, itama tayi masifar tsorata da ganin yanayinsa da sauri ta mik'e tayi bayan Ummi da gudu. Wayyohhhyyy nashiga uku..

Ummi na tambaya lafiya? amma ina ita kawai yake san ya kama, itako ta b'oye a bayan Ummi, kwata-kwata ya manta da wani cikin jikin ta, idonsa ya rufe, cikin zafin rai ya fisgo ta daga bayan Ummi ya zuba mata lafiyayyun kuma kyawawan marika guda guda biyu , then yana shirin rufeta da duka Ummi ta shiga tsakanin su tana rufeshi da maseefa ....

Nablah ta zube kasa tana kuka kamar ranta zai fita, hannunta Ummi ta kama takai ta d'aki, a bakin gado ta zaunar da ita, fridge taje ta d'auko mata ruwan me sanyi ta bata, sai da tasha Ummi ta kalle ta tace " mai kika yi mishi?

Cikin kuka Nablah tace " wallahi Ummi banyi mishi komai ba.,

"To naji yi shiru kinji, sosai Ummi ta lallashi Nablah sannan ta fita, a parlor ta iske shi, a tsaye yadda ta barshi, kallon sa Ummi tayi tace " me tayi maka son?

Shiru yayi, tare da furzar da iska,me zafi yayi ruku'u, ya mik'e a galabaice cikin rawar murya yace " wai yarinyar nan dan iskanci da aure na a kanta take kula samari, harta hau gaban motar sa suna hira tanayi masa murmushi, shi kuma d'an iska na tambaye meye tsakanin su, yace min wai santa yake, auren ta zaiyi, babban abin haushin ma har sunan ta ta fad'a mishi da karbar waya a hannunshi ...

Murmushi Ummi tayi irin na manya ta kama hannunsa ta zaunar dashi ahankali a tsanake take kallonshi tace"..........

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Dedicated to
*HAUWA A usman*
( JIDDARH)

Page 96

Tace idan ance maka kana son yarinyar nan nablah kace Sam baka sonta.
" yanzu gashi nan tsabar kishi ji yadda gabadaya yanayinka yakoma.
tunda Na haifeka deeni har zuwa yanzu ban taba ganin kamanninka sun sauya kazama wani irin mutun abun tsoro kmr irin yau ba .
"kama manta da cikar burinka wato 'cikin dake tare daita sbd tsabar kishi idanunka sun rufe kazo ka kwakwadawa yarinyar mutane mari.
in banda ma Allah Yasa Ina nan nashiga tsakani da sai kamata dukan dakayi asarar bby'n cikinta .
"idan ance kana sonta kace Kai ba Haka ba yanzu meyye wannan kayi ?

Deeni Ga son yarinyar nan karara Ina Gani acikin kwayar idanunka tare da zunzurutun kishinta .
Wanda Yasa har zuciyarka ke bugawa da karfin.
alokacin fa daka shigo dafe da tsaitin kirjinka kake sbd tsabar jarabar kishi da kunar da zuciyarka ke maka akanta ...

Deeni kana son yarinyar nan ko ka yarda ko karka yarda.
kanawa nabla wani irin mahaukacin so ka duba yadda kishi Yasa zakawa yarinyar nan nakaso.
ka duba yadda kake huci kmr zaki , ka duba yadda ka kama Yar mutane zaka mata dukan mutuwa kana kokarin son illata musu 'ya deeni ..
tunda ummi tasoma mgn deeni Yayi shr kawai yana sauraronta batare da Yayi yunkurin cewa mata komai ba.
sai ma rikitattun idanunshi daya tsura mata yana mata wani irin kallo me cike jin tsoron furucinta ...
uhm kayi shr kana dubana kaki cewa dani komai.
sbd kana tunanin zance nah ba hk bane.. muryarsa a sarke km can kasa kasa yace first love ....sai km Yayi shr ..
Deeni kennan karyata mgnta zakayi ko ?
Ba wai karyatawa zanyi ba first love Amman ni bana jin hkn atare dani km har cikin zuciyata da ruhin jikina bana jin wai sonta nake ..Ni dai nasan Ina matukar kishin igiyoyin aurena dake kanta yakarasa fadar Haka zuciyarsa Na tsananta bugawa da sauri da sauri....
Babu komai lokaci shi zai nuna Haka .
can km ummi tayi kasa sosai da muryarta nidai Dan girman Allah ka sausautawa kanka akan lamarin yarinyar nan..
Sannan km karage wannan mugun son dakake mata sbd gaba.. domin idan har yadda nake hango tsagwaron kaunarta 'cikin idanunka,idan suka zarta hk akwai matsala wanda gaba banida abinyi ....
Sannan ka tausayawa zeenat dina kada ta fuskanci wannan son dakake mata.
" ka boye mata kada ruhinta Yayi baki wanda nasan sanadiyar hkn zata iya shiga 'cikin wani hali ......hakika Ina tausayawa diyata ummi takarasa mgnrta tamkar zata zubda hawayen tausayin zeenat.
jikinsa a matukar sanyaye ya kamo hannuwan ummi dukka 'cikin nashi sannan ya Kira sunanta ... first love ki daina ce min hk sannan ki daina cewa Ina son yarinyar nan.
kada bakinki ya kamani ..
"bawai bakina zai kamaka bane deeni oready karigada kayi wannan saken...
Saken daka fada tarkon soyayyarta .
Ni farincikinka shine nawa ka nutsu kadaina takura kanka akanta dayawa ....
a Dan zafafe ya Mike tsaye ta riko hannunshi dake 'cikin nata Ina zuwa km sbd nace ka daina takura kanka akanta ne kayi fushi ..?
runtse rikitattun idanunshi Yayi sannan ya bude fess yana duban fuskar umminsa .. Sam wlh ba hk bane my first love zuwa zanyi nayi wannan yarinyar worning da kyau "
Dan wlh first love zan iya ilatata a duk sanda Na sake ganinta da wani Kato ...
karka sake ka km taba lafiyar jikinta ..
'Cikin jin zafin abinda ummi tace Ya kamo lips dinsa na kasa yana cizawa yana zame hannunshi cikin nata tare da hawa step ...
yayinda duk wannan dramar da'ake madam zeenat Na can dakinta ta manne kunneta da earpiece tana faman aikin chatting..

Yana shigowa dakin ya isketa zaune tana kuka sosai har da shesheka wani irin kallo wulakanci yajefo mata wanda Yasa kirjinta bugawa da sauri ta yunkura ta Mike tsaye da Dan saurinta jikinta Na kirma takoina .. a fusace deeni ya nuna Nablah dake tsaye da Yatsansa daya kana yace Daga Ina wannan mummunar mutumin ya daukoki ?
Chapter 138 · 0% Book details