← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 149

Sashe 69

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi tayi murmushi kawai Tare da sake zubawa nablah ido ganin yadda duk ta dawo kalar tausayi ..
ummi ta girgiza kanta sannan tace yanzu akan zakiyi magana da auntynki ne duk kika dawo haka tamkar zakiyi da kuka?
.. gsky nablah akwai shagwaba atare dake tasa ummi takarasa fadar haka Tare da Mika hannu ta janyo wayarta dake gefe tasoma dealing number Salmah ta Miko mata wayar tare da nunawa nablah wani daki da hannuta . Kishi Ga nan kiyi wayarki kinji diyarta .. haushi da takaici ne gabadaya suka gama turnuke zuciyar Zeenat dake zaune gurin tamkar ta tashi ta shake wuyar nablah ta dinga a zuciyarta , tarasa yadda zatayi ne kawai yasa ta dinga ja tsaki tana aiyana yadda zatayi da yarinyar..

wayar manne da kunnenta har tashiga dakin da ummi ta nuna mata ,daidai nan murya aunty Salmah ta doki dodon kunneta tun kafin nablah tayi magana aunty Salmah tace assalamu alaikum hjy anyi lafiya .
murya nablah cike da doki da shagwaba aunty ba hjy ba ce nablah ce .

Aunty Salmah tayi murmushi A'a nablah.. yana ji muryarki haka kmr kina cikin damuwa ?
Sai da nablah ta sauke ajiyar zuciya sannan tace bazaki jini cikin damuwa ba , byn kewarku ta dameni duk sai aunty Salmah gigice.
tace ko dai akwai da matsala ne a gidan?
" nablah tace uhmmmm fa ba matsalar komai.. in ma akwai matsalar nan bai wuce kewarku ba .

Nablah tacigaba aunty baki bawa mama number wayar hjyr bane kmr yadda kika ce gsky zuwa yanzu na matsu da son jin muryarta, km kmr naganni agabanta haka nake ji ,aunty Salmah tace Eh ban bata number ba nafison zuwa nan da sati biyu tukun nasan zuwa wannan lokacin kingama da sanin halin mutane gidan , ni dai abinda nake so dake ki zauna lfy da kowa Amman da kinga akwai matsi da takura just give me a cul" furrrrr zaki ga aunty ki kmr flay.

nablah ta saki sanyayyayiyar murmurshin dayasa dimple dinta lotsawa sosai wanda hakan ke sake fito da ainihin bawar kyawun da Allah yayi mata .

Ahankali " tace Allah aunty bbu matsalar komai fa aunty Salmah tace to.to. shikenan ,ki kama kanki da kyau km ki dinga saka hijab dinki duk inda zaki shiga a gidan .

Nablah tace har baccima dashi nake aunty Salmah Tayi yauwa Yar gari nablah na murmushi tasake bude baki da niyar tambayar auntyta dip ...maganar ta tsaya ...... Tana zaro Idanu waje sakamakon hasken dataga ya gwaraye dakin gabadaya duk daman can akwai wuta a dakin dan koda tashigo fan na aiki ..

kwance yake akan kujera idanunshi a lumshe yana kallonta kmr ranar farko daya soma ganinta a rayuwasa .

murya aunty Salmah taji tana cigaba da cewa lfy na jiki shr kin dauke wuta kmr NEPA.

A daburce tasoma in in na , A'a.......uhmmmm ba komai to yanaga duk kin rikece kigayamin in wani abu nablah tace Allah bbu komai aunty to kigaida hjy zan Kuma bawa mama number hjy zuwa jibi inshallahu ki kwantar da hankaliki zata kiraki, itama ta matsu taji muryar autata ,da kyar nablah dake kokuwa da numfashinta ta iya bude baki tace to aunty sannan ta kashe wayar Tare da sauke wayar daga kunnena.
har lokacin bai dauke idanunshi akanta ba wanda shi kansa basan ma Yana kallon nata ba .

Itama shanyayun idanunta ta zuba masa kawai tana kallon kwakkywar fuskarsa dam ...taji kirjinta da zuciyarta sun amsa a lokaci daya take ta soma jin tsoron yanayin irin kallon dayake mata.

,jikinta kuwa Banda kirma bbu abinda yake ,takoina gumi ya dinga tsatsafo mata ajikinta Jira kawai take taji yace arrrrrrr ta arce da gudun maseefa Amman Sai kawai taga sabanin haka, domin ko motsa bakinsa bai da alamun yi ballanantana akai gasamun fitowar kalma daya daga bakinsa Sai ma taga tabe bakinsa tare da dauke idanunshi akanta .

aransa kuwa cewa yayi munafuka kawai Tayi wani shr kmr ba yanzu tagama wage baki tana waya ba..😍😍😍
Ni dai nace uhmmmm deeni Banda kin fad ar gaskiya...nooooo

komawa yayi sosai yayi kwanciyarsa normal ganin datayi ya kina ya kwanta ne yasa tayi saurin juyawa da jikinta na rawa ta bar dakin har hijab dinta na neman hardeta kafafuwanta .

" afrigece ta dawo parlour inda ta bar su ummi .
Ummi kadai tagani zaune Banda mdm muzeenat ko Ina tashiga oho ita dai tunda tasamu ta mikawa ummi wayarta ta bawa karfa iska .

tayi shr sannan komai ta tuna ta dagamin kai ...

Koda tashiga dakin ma bayi tashiga dan jin yadda cikinta ke murdawa ,tun sanda take tsaye gaban horo dan sunnan data bashi kennan take jin yadda cikinta ya cure guri daya .

toilet tayi sosai byn tagama tashiga cikin bathtub ta kunnawa kainta" shawa ta dade kwance tana jin dadin yadda ruwan ke rasa kowani part na jikinta .

sai data soma jin kiran sallar ne a masallaci dake cikin gidan sannan tayi alwala ta fito jikinta daure da towel zigidir tayi gaban mirrow tana goge sauran wuraren dake da ruwa ajikinta yayansa take bin koina ajikinta da kallon, yadda yanayinta ya canza gabadaya 'ahankali tayi murmushi tana sake kallon kanta doguwar rigar mai dagon hannu ta zirawa jikinta tare da zira hijab dinta ta tada ikama...

MMN SUDAIS CE
[7/12, 7:08 AM] 0mmer Farouk: 💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA .A .BAGUDO

Page 63

Byn ta idar da sallah ne ta Mike 'ahankali jikinta a tsanyaye takarasa jikin window dakinta .
" ta makale hade da dan zuge labule window kadan ,ta yadda zata ji dadin hango abinda ke wakana a compound din estate din.

Tana nan tsaye tana kallon yadda motocin ke shige da fice a cikin estate din , ta zurawa waje Ido sosai kmr mai shirin hango wani abu na daban aciki estate din, yayinda take shakar wata iska ta musamman mai dadi da ratsa jiki.
wanda rabonta da jin irin haka ta dade , tun kafin shigowarta cikin gidan.

,har wani lumshe shanyayun idanunta take sakamakon farinciki data tsinci kainta ciki.

,Ta dauki tsawon lokacin makalle agurin tana shan iska "karar bude kofar dakin data ji anyi ne.
Yasa ta dan juyo da sauri hade da sakin labulen window.

ahankali nablah ta sauke idanunta fess. akan Zeenat dake tsaye kikam.. tana mazurai . take gaban nablah Yashiga faduwa da sauri a yatsine Zeenat ke watsawa nablah wani irin mugun kallon wanda ke hautsina kayan cikinta , ganin irin kallon rashin arzikin da Zeenat ke binta dashi ne . yasa nablah shan jinin jikinta.

tabe baki Zeenat tayi sannan tace Yar iskar baiwa... kawai abinda yakawo kennan , kin wani zo kin nemi waje a daki kin zauna kina tamkar boka dan tsabar munafurci , to kike so yayi miki sauran aiki da yayi saura uhm ?

Nablah tayi saurin girgiza kanta tare da cewa dan Allah aunty kiyi hakuri wlh na dauka ko mungama aikin ne.

Zeenat , ta sake watsamata wata uwar hararar hade da kallon banza.. wanda hakan ya suka sake frigita zuciyar nabla dake tsaye Amman ta dake batare da tabari Zeenat din ta gane yanayin data ciki ba .

Mtsssssss Zeenat taja tsaki tare da cewa dan Allah malam ni fito ki kije ki karasawa mutane aiki sannan km ki daura min abinci ,Yar isakar baiwa... nablah tayi shr tare da dago shanyayun idanunta tana kallon Zeenat dasu ,yayinda take jin zuciyarta tamkar zata kama da wuta tsabar takaicin sunan da Zeenat din kirata dashi .

Zeenat tace
Kin wani tsareni da idanunwa narai narai kina kallona ko baza kiyi bane ?
a tsanake batare da wata alamun tsoro ko fargaba ba nablah tace zanyi ..
Ok minti biyu kacal nabaki "naganki a kitchen "idan kika kuskura kika bata min lokaci zakiga yadda zan ci ubanki a gidan nan " tana gama fadar haka
ta juya fuuuuuu tasoma tafiya tana kunfar baki.

"Nablah tayi zuru kawai tare da bin bayan Zeenat da wani irin kallon mamaki da alajabi abinda tayi mata.

dan ko kusa batayi tsammani zata fuskanci irin wannan babbar wulakancin ba mai cike da al,mara .

Yau itace aka aiki tajawo aka zagin mahaifinta..abanza uban ta fa aka zaga ,ta furta akan akasan ranta, wato silar ainkinta ne jawo a dinga wulakanta mata uba Haka km ma har da kiranta da sunan baiwa...baiwa fa takirani dashi ta sake maimaita sunan a filli gabadaya abin yazo mata wani iri km abazata" tamkar ba gaske ba.
Anya kuwa rayuwar zata yuwu a Haka tun ba,aje koina ba an fara da zagar mata mahaifnta.
" Anya kuwa zan iya daukar wannan kalar kaskancin da iskanci kuwa ,abinda ta tmbyi kanta da kanta Keenan?

,'ahankali ta furzar da iska ta bakinta tana furta wlh da sake Dan zan iya daukar komai na kunci rayuwa Amman Banda zagar min iyaye .

,

, Mtssss taja tsaki itama tana harara kofar da Zeenat tabi .cikin sanyi jiki ta nufi kitchen .

Ko minti biyu batayi da daura ruwan abincin dare ba Zeenat takaraso ta tsaya a bakin kitchen din tana kiran.. ke....ke.. nablah dake tsaye tana jin Tayi banza daita duk da tasan daita take sannan km taki juyowa ...
Sai ma cigaba da aikinta Tayi.

Sai da Zeenat ta sake maimaita kiranta sannan nablah da ke ..Kusan Sau uku sannan nablah ta juyo a danketa tana kallon cikin idanunta Zeenat .

Zeenat tace ,Yar iska yarinya kawai kina jin mutane suna kiranki Amman dan dakikanci irin naki kika yi shr..ko

nablah ta hadiye bacin ran dataji yana taso mata tun daga tsintsiyar kafafunta ,sannan tace kiyi hakuri basan dani kike ba" sbd ita kalmar ke.. din da kika ce bata daga cikinta sunan nablah....

. eyyyye Zeenat ta fadi Haka tare da ta ware ido tana kallon nablah da mamaki ni zaki kawa rainin hankali , nablah tace kiyi hakuri aunty barainin sense bane a zafafe Zeenat tace yi min shr stupid girl kawai ni zaki kalla kicewa ba sunanki ke ba.... Dan bakida mutunci , to kisani ni daga yau da sunan ke ... zan dinga kiraki ,Dan Allah idan nakiraki dan ubanki karki amsa kiga yadda zanyi dake a cikin gidan nan .. .
Chapter 69 · 0% Book details