← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 149

Sashe 60

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Ahankali ya fito daga cikin motar cikin takun nan nasa kasaita idan bakasan shi ba zaka dauka ko tsabar iyaye yayi masa yawa nan haka Allah yayi sa da tafiyarsa ta musamman kai tsaye yashigo cikin babban parlour gidan yayinda gabansa ke wani irin faduwa .

inda dai kunnuwanshi ba karya suke masa ba sautin kukan matarsa yake jiyowa da murya aunty, n sa .gabanshi ne yacigaba da dokawa ai da sauri sanyo kansa cikin parlour ,ganin umminsa zaune Yasa shi sauke ajiyar zuciya tare da yin hamdala a zuciyarsa .
Domin tunaninsa ya dauka ko wani abu ne yasamu umminsa .

Zeenat naganinsa ta zabura ta Mike tsaye takaraso gareshi gabadaya ta gigice sai kuka take my hrt dan Allah kazo kagayawa mama bazaka kara aure ba ni kadai na isheka rayuwar duniya dan Allah km zan haihu Wlh nima Ina son na haihuwa dakai .
Dan Allah ka fahimtar daita ,zan iya haihuwa nima kmr kowace macce .ka fada mata Bana son kishiya wlh muddin aka min kishiya wlh zaku rasani gabadaya dan zaniya kashe kaina, , jin haka Yasa DEENI jan mugun tsaki Tare buge mata hannuta data rike shi dashi abin haushi abin dariya 'ahankali ummi ta Mike tsaye tare da kamo hannuta ta zauna daita kusa daita haba zeenat ki natsu man meyasa kike irin haka ince , magana ce kawai akeyi ,ko kinga anyi miki kishiyar ne duk kinbi ki rude kin tadda hankalinki nima kina neman tada nawa .
Wasu Hawaye ne masu zafi suka zubo mata Dan Allah ummi kibar ma ambato min sunan kishiyar ji nake kmr mutuwa zanyi numfashin har neman daukewa take duk hankali ummi yatashi da ganin yadda yarinyata ta dawo cikin kankanin lokaci rarashinta kawai ummi take.,

Mama dake zaune ta ta zuba musu ido kawai 'ahankali ta numfasa sannan tace lallai yau naganewa idanuna abinda ake fada acikin gidan ,ashe dai gaske ne fadeela kece kike daurewa zeenat gidin take yin wulakancin data gama .
,Dan wulakanci ma har wani lallaba yarinya kike kan za'a mata kishiya kanta aka fara yi mutun kishiya ?
Mama ta dubin inda zeenat take zaune tana rizgar kuka ...ince ciki naji ace ki zubar har Sau biyu shine yanzu dan tsabar iskanci,zaki cewa mutane kina son haihuwa.
,da can kinsan kina so meyasa kika zubar da shi ,ummi zatayi magana mama ta dakatar daita abinda nake son kusani shine wlh wlh nasuru ...zai yi aure matsawar baki haihu ba nan da wata tara kinji na rantse sam fadeela Banga alamun kina da tausayi ba ,ubansa ya haife shi kadai ,ya mutu ya bartshi amman shi yakare a bbu ko daya sam hakan bazai yiwu ba ,ummi ta sautata murya tasoma bawa mama hakuri ,yayinda zeenat ita km ke kuruwa tana rizgar kukan har da shesheka.

DEENI rike da wayarsa yana daddannawa bame da niyar cewa komai amman jin abinda mama tayiwa umminsa ya so-so ranshi km ya tsaya masa arai dan haka cike da haushi da takaicin yace haba mama .......meyasa zakice haka naga itama zeenat din diyarki bata ummi kadai bace .
Dan haka bai ka mata kice wai ummi ce ke daure mata gidin yin iskanci ba.
" yakamata kiyiwa ummina uzirin km aure ai nine mayin shi idan naso zanyiwa mamata kishiya Bai sai ansani ba idan bangadama ba kuwa bbu ub....Ai tun Bai kai Ga karasawa ba ummi tayi tsalle ta dire a gabansa Tare da rufe masa baki dan tasan aika aika yake shirin yi.
,mama dake zaune har lokacin ta dinga girgiza kai kawai ..
meyasa meyasa kika rufe masa baki eh ..Ai da kin barshi yakarasa abinda yayi Niya ince irin kalar taki tarbiyar kennan ,amman kusani wata tara kawai na baku tana cika ko haihuwa ko amarya acikin gidan.
ta Mike tsaye tana kokarin barin parlour ummi tabi bayanta tana bata hakuri dan ita bata son tashin hankali km koda tana so bazata iya da family muhd bello khaliyal ba.....😭😭😭

A hassle DEENI yasoma hawa step yana takawa biyu biyu yayinda zeenat ke biyi dashi a baya tana kuka tana bashi hakuri dan Allah my hrt kayi hakuri karka min kishiya wlh bazan iya zama daita ba ... am ready to give any type of bby you wont nima Ina son bby Allah ne Bai km bani ba . Ta ya Allah zai km baki haihuwa zeenat byn bakya so kyautarsa .kin butulcewa ni'ima ubangiji nki.
idanunshi a rufe yakarasa shiga cikin dakinsa ,warwas ya zube akan gado yana fidda numfashi sama sama kuka take har lokacin fuskarta tayi jazir abinka Ga farar macce 'ahankali tasoma cire masa takalminsa taje ta ajiye a inda yake ajiye takalmansa .
ta dawo ganin yana kokarin son balle maballi gaban rigarsa Yasa takarasa da sauri tashiga balle masa ya Mike tsaye tare da zare rigar da wando ya saura daga shi sai dan karamin boxes , kukuan ya isheni haka bana bukatar hayaniya yana gama fadar haka ya shige bathroom har ya fito kuka take tana masa magiya tsausayi ne taba zuciyarsa duk da tsananin haushinta dayake ji aranshi hakan bazaisa yaga ana wulakantata ya kyale ba Dan ko bbu komai ita din wata abace may daraja a gurin umminsa.
dan haka cikin sanyin nan nasa yasa hannuwansa duka ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam tsam .

Uhmmmm uhmmmm 😍😍😍😍😍😍

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 58

Rungume take a faffadan kirjinsa har lokacin " yayinda hawayen tausayin kanta ke cigaba da bin kuncinta" danasani tattare da nadamar abinda ta aikatawa kanta a can baya ne ke damun zuciya .
'hakika rayuwa bata da tabbas gashi komai yana neman tsaya mata " zuciyarta kemata wani irin zafi yau tazo mata tazo mata abu mafi muni ,kishiya ...fa.
yau ita zeenat da kanta ake kokarin son sanya mijin yi karo mata kishiya... Kishirya.. ta sake maimaita hakan akasan ranta abinda tafi mugun tsana a rayuwarta kennan ,wai aba kishiya ..

kirjinta ke mata radadi da nauyi tamkar an dora mata dutse ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta da gangar jikinta... wani irin maseefaffen kishin mijinta ne ke sake tasomata fiyye da yadda take ji a da.
tsanar sauran matan dake duniya zaune bbu aure ne ya dirar mata lokacin.

Kukanta yasoma damun tunani ,kasancewarsa mutun marason damuwa da yawan hayaniya. hakan yasa yasoma sausauta rungumar da yayi mata daga qarshe ya ma rabata da sansar jikinshi gabadaya.

, Tare da zuba mata rikitattun idanushi kawai Dan shi sam kwata kwata bai iya wani abu wai rarrashi ba . ballanantana har ya tsaya wani bata lokacinsa gurin rarrashinta .

,a dake taji sautin muryasa ',malama kiyiwa mutane shr duk kinbi kin cika min kunne da wannan bazan kukan naki mara ma'ana ..

ko uban wani ne ya aikeki wulakanta cikin da Allah yabaki tun farko .

Wlh idan kikasa damuwarki tashafi lafiyar mahaifiyata akan maganar kishiya ..nan zan baki mamaki ..
kishiya ...bama daya zanyi ba har biyu idan nagama sai nayi .
"inyaso ki mutu sai ki kashe kanki kmr yadda kika ce ,sha sha kawai ya fadi hakan yana may da jan mugun tsaki... mtssss .

take jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma jin maganar bama kishiya daya ba har idan yaso zaiyi ..
"ai ...batasan sanda ta zube kasa ba.
Tana kuka Tana girgiza masa kai dan gabadaya kasa magana tayi sai jujjuya kai kawai take tana zubda kwalla.

Wata uwar ,harara ya watsa mata hade da binta da wani irin bazan kallo wanda yasan hantar cikinta kadawa wayyo hrt karka min haka dan girman Allah karka min kishi....sai km Tayi shr Tana cigaba da kuka.... bakinsa Ya tabi tare da cewa meyya haka oya Mike .. Mike ni kibar min dakin kinsa fa ni bana son damuwa .

Yana gama fadar haka ya haura saman gadonsa ya dau towel daman km abinda ya fito dauka kennan .

bathroom ya sake koma ya sakarwa kansa ruwa tare da dauro alwala sannan ya fito kugunsa daure da towel .

mamaki ganinta yayi har lokacin bata bar dakin ba Tana nan durkushe tamkar yadda yabarta ,ganin yanayinsa da km yadda yake kallonta da rikitattun idanushi masu matukar birkita mata kwalkwaluwa ,da hana zuciyarta sukuni .
yasa ta mike tsaye da sauri jiki har rawa rawa yake tsabar tashin hankali ,a sukwane ta tabar masa dakinsa Dan tasan halinsa maseefar sa, bakaramin aikinsa bane ya shuka mata rashin mutunci idan ma taci sa'a Bai hada mata da mugun duka ba tunda daman ya mata gargadi kar sake ganinta bedroom ba .

Fitarta daga dakin yayi daidai da sauke naunauyen ajiyar zuciyar da yayi..
, yayinda wani gefe na zucitarsa na Dan tausayawa mata game da halin rayuwar data jefe kanta ciki.

hakika shi yasan tana wahalar da zuciyarta ne kawai akan batun kishiya .
Dan kishiya ba fashi sai ta zauna daita.

'ahankali ya sake sauke wani naunauyen ajiyar zuciya tare laso lip's dinshi na kasa ...
" cikin sauri ya shiga shirya kansa cikin wasu hadaddun kananan kaya masu matukar kyau da daukar hankali shirt ce ashi colour mai gajeren hannu sanye a jikinsa sai wando blue jeans wanda suka yi matukar karbar surar jikinsa.
' koda yake shi din may matukar kyau ne km kowani irin kaya ya sanyawa jikinsa sai sun amshi karbi shi.
, cikin sanyin nan nasa da takunsa na kasaita yakarasa gaban mirrow ya dauki turarensa mai matukar kamshi ya feshe ilahirin jikinsa dashi.
' sannan ya gabatar da sallah byn ya idar sallah ne ya sauko parlour kasa cike da isa .

Anan ya iske ,Ummi tare da zeenat zaune sunyi jugun jugun abin duniya ya damesu.

Ummi ta rafka uban tagumi tana tunani duk da yasan zance dai bazai wuce akan maganar aunty shi bane .

Yana tsaye yana kallonsu yaga zeenat ta kwanta akan cinyar ummi tana kuka ' tana goge Hawayen idanunta da bayan hannuta kukan ya isa haka mamana kada wani ciwon yakamaki fa.. . Ummi bazan iya zama da kishiya ba wlh taba kirjina kiji ta fadi haka tare da janyo hannun Ummi zuwa saman kirjinata .
Chapter 60 · 0% Book details