← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 149

Sashe 71

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MMN SUDAIS CE
[7/12, 7:08 AM] 0mmer Farouk: 💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 64

Tun byn fitar Zeenat nablah ke faman aikin gyaran gidan batare da samu damar zama ta huta ba.
,duk da matar gidan bata nan hakan bai hanata yin kokarin taga ta kammala da aikin ba .

Tana tsaye a kitchen din yayinda hannuta ke kai kawon gogen kayan kitchen din Wanda ya zame mata dole kullun garin Allah Ya waye sai tayi.

laraba ce tashigo kitchen din tana yimata sannu tare da sanya hannu tasoma kokarin taimakawa nabla da wasu ayyukan .

Nablah Tayi murmushi dama kinbarshi aunty yanzu zan gama ai"

Karki damu sis nima zaune nake bana aikin komai shiyasa kikaga naxo .
gashi km Naga kmr aikin Yayi miki yawa dan nasan yadda yanayin aikin gidan nan yake da cin rai km bai karewa.
" Dan ma Allah taimaka madam batanan da yanzu tasa jininki ya hau kilometers duhu.

,Dan har gara hjy da mai gidan akanta " Dan shi maigidan kwata kwata baya shiga harkar mutune yayinda ita hjy wani lokacin takan tausayawa mutun.

nablah tace Haka ne .laraba tacigaba
amman ita madam Komai zata saka mutun Sai ta nuna maka iko da isa " Ga zagin rashin mutunci , tamkar ta haifi mutane , km duk irin aikin da zakiyi mata idan bai gamsar daita a banza yake a gurinta .

nablah Tayi shr kawai tana sauraronta batare da tace mata ba , komai Sai ma maida hankalinta datayi kan aikinta.

laraba ta sake cigaba kinsa Allah ko abinci kika dafa wannan matar , muddin baiyi mata ba wlh dole ki sake yin wani .

Nablah dake tsaye 'tana aikinta , tace nifa Ina ganin kmr mdm din nan taki , kwarkwar ce.......

"Haba aiko laraba ta kwashe da wata muguwar dariya , kai gsky nablah baki da kirki wlh madam din ce kwarkwar tana mai sake kwashewa da dariya .

nablah ta bar abinda take ta juyo Sosai tana duban inda laraba take .

Kinsa Allah wlh Ni kallon kwarkwar nakewa matar nan sbd wasu abubuwa dana Ga tana yi Na marasa hankali.

" nan dai sukai ta hirarsu tare da zagin Zeenat din ,.
nablah har da cewa Allah Yasa ogon madam yakarowa mdm amarya labara Tayi saurin kai hannuta ta toshe wa nablah baki ,tare da leka parlour sakamakon jin kmr motsin mutun .
"ganin bbu alamun kowa ne yasa ta dawo ta tsaya kusa da nablah .

"ai inaganin abinda mdm din tafi tsana kennan a rayuwarta .
"kishiya.... uhm zata iya yin komai akan mijinta. ba kya ganin ko inda mijinta yake bata son ana zuwa ,ke ko kananan kaya kika saka wlh Sai takawa mutun miki birki da guzirin Harare da zagin .

,kinji ba , ai abinda yasa kikaji nace miki , Ina mata kallon kwarkwar ,Dan some time sai inga kmr tana hararata byn ban mata komai ba inji cewar nablah.

Laraba ta numfasa sannan tace shiyasa lamarin zaman gidan Sai kin kara da hakuri. nabla ta sauke naunauyen ajiye zuciya sannan tace indai hakan kike fama da matar nan Na jinjina miki dan gsky kinyi kokari wlh.

, ai a Haka ma bakiga komai ba indai mdm ce inji cewar laraba , Dan naga kmr ke kina da wani matsayi a gidan" tunda har an barki kina ganin mai gidan ,gashi km har special room aka baki a sama.

" Mtssss nablah taja wata muguwar tsaki matsayi ko walaha byn bakada wata darajar a idanun masu gidan. "nabla ta sake yin kasa kasa da muryarta Dan kar wani yajiyo abinda zata ce sannan tacigaba abinda zan fada din nan Dan Allah bana son ki fadawa kowa" Amman Allah nayi mugun tsanar mdm Zeenat din nan byn Haka km Ina fatan Allah Yasa mijinta ya kara aure.
, Dan kawai nayi kallon irin kalar haukar da zatayi koda yake ma ,may be by the time din da zai kara auren ma ,na dade da barin gidan Dan bana jin zan dau wani lokaci a gidan nan .
, laraba tayi saurin marairaice fuska haba nabla Dan Allah kada kiyi Haka ,Karki tafi ki barni na rigada na saba dake banzan so ki tafi kibarni ba .hakuri kawai zakiyi da halinta ,kiyi abinda yakawo ki.

laraba da nabla suka cigaba da aikinsu suna hira sama sama laraba Na sake cigaba dabawa nablah labarin gidan dama estate din gabadaya ,Da yake ita tana fita sosai .
nabla sai murmushi take km tana kwadayin fita taga yanayin estate din Dan tun zuwanta gidan ko get bata sake lekawa ba .

Washegari gabadaya da gyre gyre aka tashi dashi a gidan.
koina ka kalla a hargitse yake saboda wani gyara da za'a a sama da km zuwan bakuwar daza suyi daga kasar India, kmr yadda nabla taji zeenat nafawa wata friend dinta datazo .

kai kawo nablah ta dinga yi tsakanin upstairs da downstairs , kallo daya zakamata ka gane tsansar yadda ta fita haiyacinta tsabar gajiyar dake tattare daita dole ma kaji ta baka tausayi .

tsaye take kusa da zeenat ta takure jikinta waje daya , byn ta gama waken kayan da Zeenat din tayi amfani dasu ,banda harara da kallon banza bbu abinda take jiho mata .

,A zafafe Zeenat din ta kallo inda nablah ke tsaye kinzo kin wani tsayamin a kai kmr zaki tsotsemin jinin jiki ki dauki plastic ki kawai my hrt.. takarasa fadar Haka tana watsawa nablah wanimugun harara .

Nablah tasa 'hannu kennan zata dauka sai ga laraba tashigo kitchen wasu kayan wando jeans da Riga Tayi gurin frij .

zeenat ta kallite ta kalli kayan jikin laraba sannan ta watsa mata wata uwar harara ,har nablah ta ji hantar cikinta sun cure gurin daya .

Fuskarta a yatsine Tace meyye haka kuma laraba ...kinsa bana son wannan iskanci a gidana .
bama na hanaki saka irin wayan nan kayan ba?

Nablah ta dago ta dubi aunty laraba jens ne a jikinta sai riga iya gwiwa .

ok karuwanci kika zo yimin a gida ko me?
, da sauri laraba tasoma bata hakuri .
dan Allah madam kiyi hakuri wlh bazan sake sanya su ba wannan mistake ne .
,da hannuta mdm Zeenat ta dakarta da ita ya isa bana son jin komai daga yanzu ma na kashe sa irin iriin wayandanan kaya muddin kina son zamanki ya daure dani. sannan ta kallo inda nablah tsaye har lokacin bataje inda ta aiketa ba ,tsawa ta buga mata ke kuma tsayuwar uban me kikewa mutane da bazaki wuce ba kin wani tsareni da shegun idanuki masu kama dana mayu.. bazaki wuce inda na aike ki ba.

Duk da nablah taji maseefar tsoron yadda taga Zeenat Tayi Amman hakan bai sa ta nuna ta fito da tsoronta filli ba a dake sannan km fuskarta a hade ta bar kitchen din hade da tausayawa kai banta.

Domin bata ganin laifi Zeenat sai nata domin ita takawo kanta da kanta cikin wannan maseefa.

Ta Dan tsaya kafin takarasa parlour mai gidan Tasa 'hijab dinta tana goge hawayen daya yasoma bin kuncinta dan iri irin abinda zeenat takeyi musu yana taba mata zuciya sosai .

'cikin sanyin jiki tasoma tafiya har ta iso parlour da mai gidan yake tare da bakinsa da sallamarta tashigo. muryata fal cike da tsoro da fargaba.

kallo daya DEENI yayi mata ya dauke idanunsa sai abokansa guda biyu ne suka amsa mata sallamar.

, ahankali cikin tafiyarta mai daukar hankalin ga duk wanda ya kalleta , ta karaso ciki sosai , ta tsugunna ta ajiye plastic din da cup's .

Banda kallon kasa ido bbu abinda DEENI yake mata ,'ahankali tare da natsuwa ta soma tsiyaya musu coffee .
cikin wata kwasatsiyar murya taji ance ke zaman me kikeyiwa mutane anan .... oya live this place now...

Gabanta ya dukan uku uku ,cikin tsananin tsoro hade da tashin hankali ta Mike tsaye , jikinta ,har rawa rawa yake tasoma kokarin daga kafafunta yayinda idanunta suka ciciko da hawaye tafff, ta bar parlour, daidai bakin kofar main parlour ta kusan ci karo da zeenat da sauri taja da baya ta tsaya, tana mai sa bayan hannuta tana goge hawayen dake bin fuskarta.

Zeenat ta tsaya kawai tana kallonta tare da nazarinta da kyau sannan tace kukan munafurcin uban me kikeyiwa mutane ,kmr ba aikin kudi kikazo yi ba tasoma maseefa tana zaginta .

, duk yadda nablah taso hadiya damuwar dake zuciyarta hakan yakasa samuwa , domin kuwa sabon Hawayen dake makale a idanunta ne suka samu nasarar zubowa .

, uhmmmm daman Sai Dana gaya ummi tabari a sallemiki Dan nasan bazaki iya tabukawa mutane komai Amman tace Sam...

Yanzu kukan iskanci me kikeyiwa mutane nablah ta girgirza kai tare da cewa bbu .

Zeenat ta tasoma kada kai cewa zama ayi komai din sannan ta Miko nablah wani karamin jug mai dauke suga tace ungo Ni ki kaiwa mijinta baiwar banza kawai.

,jikinta a sanyaye km badan ranta yaso ba ta sake koma parlour ...

byn ta fito ne ma abokinsa manir yace DEENI ina kasamo wannan fine bby din mai tsabar kyau gaskiya tamin kyau sosai .....

Take DEENI ya hade rai tamkar Wanda yaji wani mugun abu .. meye matsalarka daita ?

Manir yace yarinyar ce tamun kyau kawai , a fusace deeni yace bakowa bace facce house girl dina.

dayan abokin nasa ne yace gaskiya yarinyar tana da kyau sosai ba karya gashi Tayi maseefar ta haduwa dayawa .
irin wayan nan Ai nashiga mota ne da kewaye kasashen duniya .

A zafafe DEENI yace bafa nason iskanci nan naku idan abinda yakawoku kennan natashi nakama gabana .

Manir yayi dariya tare da cewa kai fa matsalar kennan to laifi ne dan mutun yaga abu ya yaba sai km yazama abin damuwa.
Fahad dake zaune yana nazarin deeni ya amshe da cewa kai meyasa DEENI kike yin irin haka ne ? Kacika daukar komai da zafe.
Chapter 71 · 0% Book details